← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 237

Sashe 44

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

baiwa matarka taci gaba da kular maka dasu. To nasan zaka fi son yarannan a hannunka Gwadabe. Amman sauƙi muke nemar maka kayi haƙuri ni zan tafi da Toye tamu zai riƙe Taiwo da Kahinde, tausayin yaran muke yi a hannun su Babala. Na ji daɗin samuwar lafiyarka, babu abinda zamu ce da Allah zai godiya. Ka yi haƙuri ka daɗa" Wata wawuyar ajjiyar zuchiya ya sauke mai nauyi yace. "Bara'u yau ko ni kuka ce zaku ɗauka da kai da Tamu ba yaran ba, bana jin zanyi muku musu. Yarannan naku ne ku yi yadda kuke so dasu. Nagode da soyayya Allah ya bar zumunci. Sannan Bara'u wallahi na rungumi ƙaddarata, ina fatan Iyabo ma ta rungumi tata ƙaddarar. Amman fa ni da Iyabo Allah shi ya haɗa zukatanmu. Ko anan gaba in nayi aure, matar zata tsaya ne kan iyakar matsayinta, bata isa hawa matsayin Iyabo ba. Ita kanta nasan hakanne ta ɓangarenta. Bara'u Iyabo mutum ce har da ɓari" "Zahiri Iyabo Mutum ce guda da ɓari. Allah yai mata sauyin alkhairi, kaima Allah yai maka sauyin alkhairi. Yanzu mu je mu shirya yaran, tunda jikinka yayi kyau ai sai mu je Abujar tare mu kai ƴan biyun. Daga nan sai mu wuce Takai. Dan Malam magaji ya zo jiya. Inajin su Yaya Hambali basu sani ba tukunna dai" Ai kuwa haka akayi. Bara'u da kanshi ya haɗa ma ƴan biyu kayansu a jakar buhu, ya haɗa na Toye. Gwadabe ya rufe ɗakin da ko tabarma babu. Yaima su Yaya Hambali sallama kan zashi Abuja daga can zai zarce Takai gaishe da Baba Magaji da yazo. Yaya Hambali yaso jin dalilin tafiyar, amman Gwadabe sai ya ɓoye mishi dan ko fuska bai bashi ba, yana kan turmi Yaya Haula na gasa mishi baki. Bara'u shi ya biya misu kuɗin mota. Cikin Awa shidda sai gasu a Gwagwalada. Da mota Tamu yazo ya ɗaukesu har zuwa dan madaidaicin gidanshi. Bayan sun yi sallah sun huta, Ayashe ta kawo musu abinci Falo ƙanwar Tamu na biye da'ita da plate a hannu. Ayashe ta shiga da yaran ciki, bayan ta jajantama Gwadabe abinda ya afku cike da jimami. "Kaga Shafs ce wannan data shiga ciki yanzu. Da shine nake tunanin Bara'u ba zan ba Gwadabe Shafa ba kawai. Kaga a matsayin wa kake a wajenta, kuma ta ɗanyi karatunta yanzu haka karatun diploma take haɗewa anan Gwagwalada. Da in ta kammala sai ayi auren ko ya ka gani Bara'u?" Bara'u yayi dariya suka tafa da Tamu kafin yace" "Yarinya zuƙeƙiya son kowa, gata budurwa sharab. Shafa a gabanmu aka haifeta. Bana mance taron sunanta, kasan gida _gida mu ka dinga bin abokanmu muna raba musu alawar gaiyata. Kowa yazo da sile da sisinshi. In abun ya tabbata zaiyi kyau sosai " Tamu yace. "Wato kai Bara'u baka da mantuwa sam. Ni ai tunanina in rama halaccin da Gwadabe yayi mini, ko banyi mai daidai da abinda yayi mun ba, in kamanta mishi. Gwadabe na baka Shafa halak malak. Nine maɗaurin aurenta dama. Zan mata bayani duk lokacin da ka samu nutsuwa sai ka neme ta, a hankali tunda ba sauri akeyi ba sai ku daidaita tsakaninku. Yara kuma zanci gaba da riƙonsu ko kun yi auren ma, in sha Allah ni zan aurar dasu da hannuna. Zan kuma so in haɗe su aure da nawa yaran dakan ɗaka shiƙan ɗaka" Gwadabe bai yi musu jayayya ba bare turjiya. Kwana ɗaya su kayi a garin Gwagwalada suka juya washe gari, bayan Gwadabe yayi sallama da ƴan yaranshi, abinka da yara sun shige cikin yara ƴan uwansu sai adabo ma suke ma uban. Ganin yaran sun sake ne uban ya ɗan ji ƙarfin guiwa kuma.
Chapter 44 · 0% Book details