Sashe 28
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kinga can wajen tudun?" Gwadabe ya nuna mun da hannunshi. Wani dan tudune karami akayishi a falon kamar wajen cin abici. ( Daining )Amman bashi da girma, a wajen na saka kayan kallona. "To ki fito da kayan kallon gobe zan siyo miki teburi da dirowar da zaki dinga zuba kayan abinci a ciki. Zaki dinga amfani da risho, ke ko gawayinne in kika kunna a Æ™ofar É—aki daya ruru ki shigo dashi, ki sa labule wajen ya zama miki kicin. Iyabo bana so ki sake fita na kuma na jajjada miki. Kiyi haÆ™uri wata rana sai labari. Ki daure wallahi ba'a sona haka ke faruwa ba, naso mu bar gidannan muyi nesa da Æ´an uwa Kuka babu irin wanda banyi ba, washe gari kuwa sai ga Gwadabe da tebur, da durowarshi gajera ta kicin É—in Æ´an gayu. Tare muka jera kayan tukwanena da É—an kayan abinci da nake dasu, har randunana a cikin wajen na jera, Gwadabe ya hau ya kafa mun labele, Laila sai zirga_zirga take yi tsakanin tsakar gida da ciki. Bai fita ba sai da ya ciccika mun randunanan da ruwa tab, kana ya fice kasuwa. Ni kuma na shiga aikace, aikacen gidan. Bani na fita tsakar gida ba sai da na gama komai nawa na fito da ruwa bokiti uku na sheÆ™ar a rariya, bokitin dana shake shi da wanki na fita dashi na je maÆ™ota na shanya. Ina dawowa na yi komawata É—akina. Haka al'amuran rayuwar su kaci gaba da gudana yau fari gobe tsumma. A kwana a tashi, gashi yau mun wayi gari jama'ar Takai suna hanyar shigowa Kano. Gidan namu shaÆ™e da matan anguwa suna ta faman taya mu aikace_aikacen biki. Dan Yaya Haula hantsice leÆ™a gidan Kowa, babu gidan da bata shiga, kowa a layinnan ya santa. Gida ya É—au fenti, ga girma da gidan ya Æ™ara, sakamakon gidaje biyu na jere damu da Yaya Hambali ya siya, aka rushe katangun gidan ya Æ™ara girman gaske, kuma yasha gyara sosai. Æangaren Amarya Laraba da Ango Nazifi ya sha gyara na musamman. Wajajen la'asar sai ga Æ´an Takai sun iso Bus biyu su da gayyar yara raÉ“e_raÉ“e, gida ya kacame da hayaniya, amman nifa babu wanda yazo daidai da Æ™ofar É—akina . Washe gari aka shiga biki ka'in da na'in. Ranar É—aurin aure tun duku_ duku muka game jallof É—in shinkafa, da tuwon shinkafa, harda masa. Su Gwadabe kuma suka kama hanyar Takai dan acan za'a É—aura auren kasancewar duk haÉ—in gidane. Ko akwatin Amaryar Nazifi baa'a kaiba, ance in aka kawota sai kawai a miÆ™a. Akwatuna masu taya suna nan a É—akin Yaya Haula, ina dai gani matan waje sunata shigowa kallon kaya. Ni ko da nake gidan babu wanda ya neme ni da in zo in ga kaya, nima ban É—aÉ—a kaina ba. Bayan azahar maza Æ´an É—aurin aure suka dawo tare da bataliyar maza Æ´an Takai. Da yamma lis kuma sai ga jerin gwanon tsofaffi da Amarya an tawo da'iya. Harda Sakina aka tawo, suma sun sha ankonsu na Takai. Muma duk mun ci namu ankon na cikin gida, shaddace mai ruwan toka na iyaye, sai wani yaÉ—i haka na Æ™awayen Amarya dai. A haka taro ya watse, duk da ina kaffa _kaffa sai da Yaya Halima ta ci mun mutunci a cikin mutane, daurewa nayi na shanye dan a ranar ma Takai zasu komai. A dangina babu wanda yai mun kara yazo, Uwani ce dai na matsama bata da yadda zata yi shi yasa tazo. A kwana a tashi asarar mai rai. Wasa wasa Æ´an biyu shekararsu guda, har suna dabo, Toye kuma yanata zuwa makaranta. Fitinar gidanmu kuma babu abinda ya ragu sai Æ™aruwa, dan sau huÉ—u Gwadabe na biyan kayan da aka sata. Na huÉ—un ma har Æ™arÆ™ashin kujerata akazo aka saka mun, da suka shigo bincike suka zaro. Nayi imanin Laila ce ta aikata mun hakan ba kowa ba, dan tuggu da munafurci iri iri take haÉ—awa, tsaraicinta da aljanun Æ™arya fa babu abinda laila ta dena, a wannan shekara guda É—in abubbuwa masu dama sun faru. In baku mance ba nace ina yaye Æ´an biyu zan bar gidan, to maganar tana É—amfare a zuchiyata. Ga zawarawa kullum a cikin sallama da' Laila suke, tare da kawo mata Æ™walam da maÆ™ulashe, amman mayyar tana kan bakarta ita sai Gwadabe. Gwadabe ne yaita bani haÆ™uri nima ganin na kusan yaye in barshi ma baki É—aya shi yasa ma ban yi tafiyata ba na haÆ™ura na zauna, na cire damuwar kowa da komai a raina. Kamar wasa wata ranar juma'a sai ga Oga Lurwanu shi da karen motar Gwadabe sun riÆ™o gwadabe ko iya taka Æ™afarshi bayayi, suka shinfiÉ—e mun shi a doguwar kujera. "Gashi nan kin ganshi, mota ya shiga, amman wallahi sai zaro shi akayi Æ™afa taÆ™i takuwa. Muna kyautata zaton sammu akayi mishi. Dama in dai a raba mutum da kafa ko hannune a harkar tuÆ™i ba kanshi farau ba. Sai ku dage mishi da maganin gargajiya" Hannu na É—aura aka ina kuka, shima Gwadabe kukan yake yi yana girgiza mun kai halamar in yi shiru. "Ki gode ma Allah ma, da ba haÉ—arin mota akasa yayi ba ya ragargaje ba. Dan shima anayi kana tsaka da tuÆ™i sai kaga zaki ko kura, kana É—auke hannunka magana ta Æ™are. Wasu kuma teku suke gani a gabansu duk sai su dibibice" Ni dai sai mamaki da tsoron sha'anin mutan Duniya duk ya kamani. Nera dubu biyar ya ajjiye mun. "Mu kam zamu koma Gwadabe Allah ya Æ™ara sauÆ™i" Su kai mana sallama suka tafi. Kifewa a jikinshi nayi ina kuka kamar fitar rai. "Iyabo ki yi ta mun adda'a Allah zai bani lafiya, ta Allah ba dai ta mutum ba. Ni na É—auka wannan jarabawace ubangijina ya jarabceni dashi. Bazan É—aura hakkin akan kowa ba Allah yana madakata yana ji da ganin kowa. Ki yi ta mun adda'a. Kafin in amsa shi Yayyen nashi su kayo sallama suka shigo. Baban Nazifi yace. "Gwadabe haka abun ya faru? Ni ina kasuwa ma shigowata kenan mata suke sanar dani wai an shige da kai a hannu baka tafiya, haÉ—ari ne ya afku kome? Koma dai menene Allah ya kyauta gaba. Ke bamu waje ko?" Ya juyo yana mun kallon tsana, Æ´an biyu na kwashe dan kar su damu Babansu. Ina daga uwar É—aki na kira Iyaa nake sanar mata halin da Gwadabe yake ciki. Halin ko in kula ta nuna, tsaki ma tayi ta kashe wayarta, sai Burodami kokodeen da Burodami Debisi na kira na sanar musu, sai Æ™awar arziki Uwani. Su Baban Nazifi sun daÉ—e sosai a falon kafin daga bisani suka tafi, ni da yaran muka fito. "Iyabo inaso zan É—aura alwala, gashi ina jin fitsari ma. Zaki iya kuwa?" Murmushi nayi ina hawaye lokaci guda nace. "Ai ko É—aukarkane kacokam zan iya mijina. Nice a haƙƙu in yi maka duk abinda kake da buÆ™ata" MiÆ™ewa nayi na kai yara uwar É—aki na kulle, falonma na kulle na tawo da Æ™aton po mai murfi, cikin dabara na zamo Gwadabe izuwa kan po É—innan. Yayi fitsari na mai tsarki, na sake mayar dashi kan kujera. Daga ni har shi sai muka fashe da kuka na faÉ—a jikinshi. Allah kenan mai yin yadda yake so da bayinshi. Mutum ya fita da Æ™afafuwanshi amman yanzu jibeshi a kwance, abunda yafi Æ™arfi yanzu ya fi Æ™arfinshi. Su Baban Nazifi daya kamata ace su zasu mai duk wannan amman kowa ya tafi ya barmu. Gwadabe kayi haÆ™uri kuka ba namu bane fa. Akwai Allah shi zai yi mana sakayya. Ka rungumi Æ™addararks sai Allah ya kawo maka É—auki. Zaka warke bi izinillahi rabbi" "Iyabo ki duba dangina jinina yanda suka nuna halin ko in kula da abunda ya sameni, babu wanda ya tambayeni ko ina jin wata lalura. Yanzu ko Da'u da ba sai ya zauna ya kula dani ba?"... A'a Gwadabe kar ka É—aura musu nauyin da ba nasu ba. Ni ya kamaci da in jinyata maka. Karma ka sake tada wannan zancan. Ga bawo kayi alwala." Shi da kanshi yayi alwala ni kuma na wanke mishi Æ™afafuwanshi. Gwadabe ka daure in kai ka kan gado kaji, sai kayi zamanka acan. Yanzu nan anjima kaÉ—an Laila zata tashi kwanciya." "Ba zaki iya kaini ba Iyabo, ki je ki kira Da'u ko Nazifi É—ayansu yazo ya kaini, ko du su biyun." Bana so in mishi musu da To" Na amsa mishi, na fita da po É—in da yayi fitsari na zubar, sai da na mayar Æ™arÆ™ashin gado sannan na je kiran Nazifi da Da'u tare da sanar dasu saÆ™on dake tafe dani. Abun mamaki ko da suka kinkimeshi su biyun dukkansu sai mitar yayi nauyi suka dinga yi, Æ™afarshi É—aya ma basu kama ba sai janta su kai kii. Ni ko ina durÆ™ushe ina hawaye har suka fice ina kuka. A wajen su Yaya Haula suka shigo suka sameni idanuna sun Æ´i luÉ“u_luÉ“u dasu. "Ohh ni Æ´arnan mutum ba a bakin komai yake ba, yau_ yau É—innan Gwadabe ya zama musaki sai an kwantar sai an tayar. Sannu Iyabo kinji sannu" Kalmar musaki data faÉ—a ya dafani sosai. "Kaimu muje mu yi mishi sannu ko. Laila sai ki kwashe kayanki ki ko É—akin su Halima da Ƙauwama sai ki koma kinga Æ´an zuwa dubiya zasuita sunturi kuma dole falo za'a dinga fito dashi" Ni dai gaba nayi suka biyoni. Suka gama gaisheshi suka fita. Ni kuma ina gefenshi ina tofa mishi adda'a a Æ™afar tashi, shi kuma yana kallon silin yayi wani irin sanyi" "Iyabo kinga irin riÆ™on wulaÆ™ancin da Da'u su kai mun? Kinga yatsan Æ™afata ya fashe. Daga kwanciya lalura yau _yau harna soma fuskantar wulaÆ™anci, sai kace ba ciki É—aya muke ba. Wannan Æ™iyayyar dame tayi kama, ki duba fa yanda su Yaya Hambali suka zo suka dubani wallahi babu damuwar komai a fuskokinsu, sai cewa su kai nima karambanine yasa na shiga sana'ar da bani da ilimi a kanta. Wai sana'ar hatsari gareta." Hawayene suka gangaro daga idanunshi izuwa fuskarshi. Rarrashinshi na dinga yi, a Æ™oÆ™arina na ganin na faranta mishi rai, wala Allah ya samu sassauci. Ruwan É—umi na zuba a bawon na tsoma tsumma na É—an gargasa mishi yatsan nashi da yake jini. Ya samu yayi sallah, na bashi abinci a baki da kaina,