← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 225 OF 237

Sashe 225

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uwani na turare ɗakinta da turarukan wuta Laure tayo sallama ta shigo da tiran abinci niƙi_niƙi. "Hajiya ga abinci inji Hajiya Babba ta kuma ce tana gaisheki." "Allah sarki kice mata ina amsawa zan shigo inna yi Sallah mu gaisa in ga yaran ma" Laure tace. "Za'a faɗa mata in sha Allah" Ta saka kai ta fita. Bayan Uwani ta bi saƙo da lungun gidanta ta turare ko ina. Sai ta yi sallar magriba kana ta nufi daining table domin cin abincinta kuma. Da Uwani ta buɗe abincin wallahi take ta raina kanta. Tun daga ƙamshin, kama da kyanshi a ido, uwa uba daɗi a baki. Tuwone na semobita da wata iriyar miya wanda Uwani ta rasa gane wacce iriyar miya ce wannan dan ba irin miyar tuwon Arewa bane. Ga wasu irin kifaye sama da kala bakwai a cikin miyar gunduma_gunduma. A baki dai uwani ta gane akwai albasa sosai a miyar, ta ji ƙamshin niƙaƙƙiyar gyada ma. ( Miyar duniya ce wallahi) Ɗayar kular kuma farfesun ƙafar saniyace tayi mugun danƙo sosai ta dahu har kashin ya rabu da nama. Uwani na cin abincinnan tana girgiza kai. Sai da ta ƙoshi ta yi ƙas ta wanke hannu tukunna. Sai ta soma tunanin da sakel ya zame mata dole ta sake zage damtse wajen fito da kalolin girki na ƙasashe daban_daban ba iyakar abinda akeyi a Najeriya ba najeriyar ma Arewa. Murmushi tayi ta miƙe da ƙarfin guiwa data tuno da nau'ikan abincin larabawa da abubbuwan shan su. Mayafi ta zara ta fice duk inda ta gilma sai ƙamshin turaren turara kaya take yi ƙamshin yana tsayawa a duk inda uwani ta ratsa. A matattakalar benen sauka suka ci karo da Hajiya Sa'a suna haurowa ita da ƴan yaranta mata su biyu. Tun daga dai nesa data hango uwani sai ta turɓune rai. Itako Uwani da fara,a tace. "Hajiya Sa'a barka da gidan. Sai naji kamar tsayuwar motar Alhaji Sama'ila ko?" Da mamaki ta dubi Uwanin dan ba'a kiran sunanshi da Abba kab yara da su matanshi suke kiranshi harma da masu gadinshi." "E shine" Tana faɗar haka ta yi wucewarta. Uwani tayi murmushi tare da yin ƙwafa. "Dani kike zancan wallahi in dai nice zuchiyarki ma na dab da bugawa ne. Ni bana ɗaukar iskanci Allah ma ya sani. Mata sai shegen baƙin hali, nifa miji bai dameni ba balle kishiya wallahi " Tana sauka harabar gidan ta hango babbar yarinyar Hajiya Mansa mai suna Mabaruka ta amshi jakar uban. Ƙannenta suna biye da'ita yayin da uban ya take musu baya. Uwargida Hajiya Mansa kuwa tana bakin barandar shashenta tana jiran isowarsu. Tayi ado da wata jar atampa dinkin doguwar rigar daya shanye ƙibarta ya ɓoye tumbinta tayi kyau sosai kamar ba itace uwar zagada zagadan ƴan mata da samarin ba. Murmushi ta sakarma mijinta shima murmushin yayi mata suka shige ciki. Uwani na harɗe tanaa kallonsu cikin sha'awa. Hajiya Sa'a na daga barandar sama itama kallon nasu take yi. Uwani na ɗaga kai ta hangota ita kuma sai karkaɗa kai take tana bin shashen Hajiya Mansa da kallo. Murmusawa Uwani tayi kawai ta nufi shashen Hajiya babba. Da sallama ta shiga du suna falo a baje a ƙasa Alhaji Sama'ila yanata ciro kayayyaki a leda. Ita kuma uwargidan tana ɓarayin daining tana zuba mishi abinci. Tana ganin Uwani ta saki murmushi. "Hajiya Uwani kece? Mu da muke shirin haurowa da yaran duka? Samira ga Antynku ku gaisheta." Murmushi Uwani ta mayar mata ta nemi waje ta zauna, cikin mutunci da girmamawa suka gaishe da Uwani. Alhaji Sama'ila ya sallami ko wannensu da tsaraba kana ya dawo da kallonshi wajen Uwani. "Amarya ba kya laifi. Dama kuwa nayi tunanin in haura wajenki dangane da batun shagonki na kasuwa. Yaran da aka saka aiki sun gama jera komai. Zuwa gobe zan ɗaukeki in kai ki, kiga wajen." Hajiya Mansa ce ta karaso suka gaisa da Uwani tare da yi mata Allah ya sanya alkhairi batun shago. Uwani dai bata jima ba ta miƙe Ai kuwa Hajiya mansa ta ciko mata leda da cincin da alkali na bikin ƙaninta da suka yi. Tayi musu sallama ta fita. Washegari da sassafe ta gama aikinta ta ci ado sosai na kece sara ta sakko ƙasa Alhaji Sama'ila na jiranta su fita. A bakin motarshi ta samu Hajiya Sa'a a tsaye suna magana, da dukkan halamu ƙorafi take yi mishi ko akan menene dai oho. Ganin isowar Uwani ne yasa tayi shiru tare da sake tamke fuskarta. Haɗe rai Uwani tayi bata tankata ba ta ratse ta bayanta. Ita kuma tayi ƙabe_ƙabe a gaban motar. "Baiwar Allah ɗan matsa ko inaso zan shiga motarr." Uwani ta faɗa rai a haɗe. Buɗar bakin Hajiya Sa'a sai tace. "Tunda ni kika zo kika samu ai sai ki jira in gama abinda ya kawonu ko tunda ba kwana zanyi ba. Sannan ko da kika zo kinyi sallamane balle gaisuwa?" Ta yi maganar cike da wulaƙanci. Uwani ta kalleta ta sake kallonta har ƙasa. Sai kawai tayi dariya tace. "Hajiya Sa'a ni dinnan da kika ganni bana neman faɗa, amman fa bana barin ta kwana balle tayi tsami. Na fahimci baki samu tarbiyya ba, ko girman kaine yayi miki yawa, ko kishi ke muƙirƙusarki ohon miki dai. Ai tunda nazo gidannan baki taɓa buɗe baki kin gaisheni ba. Kinga kuwa ai ba zamanki nake yi ba da zanta binki da saƙon gaisuwa sai kace wata ƴar iska ba" Wani dogon tsaki Uwani ta saki tare da jan kafaɗar Hajiya Sa'a zuwa gefe tayi shigewarta mota. Hajiya Sa'a kasa magana tayi dan mamaki. Shi ko Alhaji Sama'ila baice musu komai ba. Ya fahimci Uwani dama zata yi mishi maganin rashin mutuncin Hajiya Sa'a. Ta saba cunkusama Hajiya Mansa baƙaƙen maganganu yau gashi ita ake mayarma. Uwani ba tai aune ba Hajiya Sa'a ta bude murfin motar sai ji kake tas ta mari Uwani tare da karkaɗa yatsunta tace. "Ruwa ba sa'an kwando bane. Iyayena sun fi ƙarfin ki zagesu marar tarbiyya wacce ta je saudiyya ta gama iskancinta da mazan larabawa. Wata uwar tsawa Alhaji Sama'ila ya daka ma Hajiya Sa'a. Uwani ta yinkura zata fita ya riƙeta. "A_a Uwani kinga gidannan cike yake da masu aiki. Ki yi haquri in na dawo da daddare sai muyi magana" Ai bai ƙarasa magana ba Uwani ta fice jikinta har rawa yake yi ta dira a wuyan Hajiya Sa'a. Ba sai dambe ya kaure ba. Uwani ta zage ta dinga jibgar Hajiya Sa'a kamar Allah ne ya aikota. Hajiya Mansa da yaranta da Laure ne suka tawo a guje, suna ƙoƙarin ɓanɓare Uwani a wuyan Hajiya Sa'a. Uwani ta maƙalƙale mata wuya sai gula take mata a ciki da dundu a baya. "Alhaji Sama'ila ka fito ka raba wannan faɗan dan Allah, jini ne yake fita fa. Ku Mabaruka maza kuje direba ya kai ku makaranta " Da sauri yaran suka tafi dan basu taɓa ganin tashin hankali haka ba. Alhaji Sama'ila ne yasa hannu ya ɓanɓare Uwani daga wuyan Hajiya Sa'a, yana tsakiyarsu. "Ke shiga mota mu wuce, ke kuma ki haura sama inna dawo zamu yi magana" "Iyakar abinda zaka ce kenan Alhaji. Jibi abinda mahaukaciyar matarka tayi mun." Ta nuna mishi wuyanta da Uwani duk ta yakushe mata yana jini, ga cikinta a ƙulle. "Mekike so ince dan Allah Hajiya Sa'a. Ba dai juninki bane faɗa da masifa ba. To dama watarana sai ka samu daidai da kai." Hajiya Mansa tace. "A dai yi haƙuri ai Sa'a da hakuri kika yi. Uwani yaushe ta zo gidan da har za'a soma irin wannan abun?" "Dallah malama ki rufa mana baki...." Kafin ta ƙarashe Uwani tayi wuf ta matsar da Alhaji Sama'ila ta sake rarumar Hajiya Sa'a suke tafi taga_taga suka faɗi yib a cikin ciyayi. Uwani ta ɗale ruwan cikin Hajiya Sa'a. An yi abu sosai dan kayan jikinsu duk yayyagewa yayi. Nono Uwani ta riƙe ma Hajiya Sa'a carab, sai ihun azsba take yi. Alhaji Sama'ila ya kama hannun Uwani ya haura da'ita sama ya kulle ɗakin nata. Ya sakko ya koma wajen su Hajiya Sa'a da take ta kumfar bakin ita wallahi ba zata yarda ba. "Kin kyauta Sa'a. Na kuma gode da wulaƙantani da kika yi a gidana. Hajiya Mansa cikata nace" Da sauri Hajiya Mansa ta saketa. Keyn ɗakin Uwani ya bata yace. "Gashi zuwa anjima ki buɗeta. Ke kuma in direba ya dawo daga kai su Samira ya Kai ki asibiti." Ya ja motarshi ya fice. Uwani dan jaraba ta window ta zuro kanta ta nuna su Hajiya Sa'a tace. "Zaki san kin ce mun karuwa. Faɗannan wallahi bai kareba kinsan Allah saina zaneki ciki da waje sannan hankalina zai kwanta. Zan nuna miki ni cikakkiyar ƴar bariki ce" Hajiya Sa'a tace. "Ni an faɗa miki ƙyaleku zanyi ki karyani? Wawuya daƙiƙiya ashe mahaukaciya Alhaji Sama'ila ya auro bamu sani ba" Uwani ta dinga aiko guma_guman zagi ji take yi kamar ta diro daga sama. Hatta maƙota sai da suka shigo. Da ƙyar uwani tayi shiru, shima sai da Hajiya Sa'a ta shiga mota direba ya kaita asibiti bayan ta sake kayane. Uwani ta kai mari ta kai gwauro a falonta sai naushin hannunta take yi tsabar masifa hancinta sai bubbuɗewa yake yi. "Hahaha ai na rantse da Allah saina ɗarsa miki tsorona a zuchiyarki ta yadda ko waje nazo sai dai ki gudu. Bura uba ni kishiya zata yima wannan cin kashin a gaban miji in ƙyaleta? Ai wallahi bata isaba da dai iyabo ce itace lusara matsoraciya." Uwani ta jima sosai tana kai kawo. Sai da tayi wanka ta ɗauro alwala ta dinga nafila kafin jikinta ya dena rawa. Wajajen azahar Hajiya Mansa ta buɗe barayin Uwani Laure ta shigar mata da abincin ranarta. Har zuwa la'asar babu Hajiya Sa'a babu labarinta. Hajiya Mansa ce ta kwankwasa ƙofar falon Uwani. Uwani tazo ta buɗe mata tare da tarbarta da fara 'a. Waje ta samu ta zauna. "Hajiya Uwani ashe kema babu damane wajen faɗa?" Ta ƙarashe zancen da dariya. Uwanin ma dariya kawai tayi mata. "To ayi haƙuri dan Allah abun ya wuce kuma dan Allah kar a sake maimaita hakan dan hankalin mai gidan in ya kai dubu nayi imanin a tashe yake. Gamu da ƴan aiki gamu da maƙota.
Chapter 225 · 0% Book details