Sashe 76
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
dani tace. "Ki dena kuka yarinya. In dai arziki kika fito nema da guminki kin samu. Dan ana biya sosai a gidannan. Amman fa akwai aiki masu yawa sai kinji kamar zaki mutu. Bayana, ƙirjina duk ciwo suke yi mun. Aikin ya gagareni shine naima Hajiyar gidan magana inason zan koma Najeriya a samo wacce zata zama madadina. To gashi Allah ya kawo ki. Zan zauna dake na kwana bakwai in kula dake har sai kin gaggane aikin sai in tafi. Akwai wata yarinya itama aiki take yi da ɗayan shashin na gidannan. Amman ita bata jin Hausa daga wata ƙasar take. Yanzu bari in baki tea da biredi ki ci, sai in zaga dake ki kama aikin ki. Sunana Takarofi" Kukana na share, nace da ita. Sunana Iyabo" "Ayya beyerabiya ce ke ashe? Amman kinji Hausa sosai. Ina zuwa to" Fita tayi tana ɗingisawa, nabi bayanta cike da tausayawa sosai da ido. Bata fi minti goma ba sai gata niƙi_niƙi da kayan karyawa. Lafiyayyen biredi da kakkauran tea har da bota da wainar ƙwai. Cin haɗama nayi ma biredinnan. Takarofi sai kallona take yi. Bayan na kammala tsab sai tace in biyota muje. Nan ta zaga dani lungu da saƙo na gidan, da duk wani aiki da zan dinga gabatarwa. Time table na abinci ta nuna mun gasunan a rubuce reras da turanci. Ko wacce rana da irin abincin da za'a dafa. Cikin sarewa nace. Wai Mama dukka aikinnan ke kike yinsu ke kaɗai?" Murmushi tayi tace. "Shekarata biyar cib a gidannan ina aikin bauta. Ciwon baya, ciwon ƙafa da ciwon sanyi duk sun kashe mun jiki. Aiki zaki zage kiyi KAN JIKI KAN ƘARFI dan basa son saiɓi sai yanzu su koreki." Ajjiyar zuchiya na sauke, na shiga ruɗu da tashin hankali sosai. Nayi dana sanin baro ƙasata nace Kuma tsawon awa nawa kike ɗauka kafin ki kammala aikinnan har ki samu ki huta?" Dariya sosai wannan karon tambayata ta bata. Mrs Bukhari