Sashe 37
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
a kumbure. Matar da muka zauna waje guda na tambaya. Baiwar Allah a ina zan samu motar Jere Banyo?" Cikin kwaÉ“aɓɓiyar hausa tace. "Nima can zani, mu je daga can gaba zamu samu mota sai mu tafi" Ajjiyar zuchiya na sauke, na bi bayanta tiryan_tiryan har zuwa wajen akori kurar dana ga ta cika ta batse da mata da mazan funani. Duk masu tallar nononnan da sukaita wucewa ashe duk can zasu je. Iko sai Allah tafiya mabuÉ—in ilimi kenan. Haka na haye akori kura na biya nera É—ari, a cakuÉ—e muke da maza, motar an cika mutane har bana iya shaÆ™ar numfashin kirki, baka jin komai sai warin hammata da Æ™arnin nono. Ga hanyar babu kyau, haka mu kaita cuccurewa waje guda da mazan da matan. Na sha É—an karen wuya ainun kafin mu isa Jere Banyo. A mugun galabaice na fito, ina mayar da numfashina. Masu acaÉ“a ne naji suna ta ihun faÉ—in. "Jaɓɓi lamba zaki je, kuzo mu je" A galabaice na isa gaban acaÉ“ar nace. Jaɓɓi lamba zani, nawa ne?" "Nera hamsin ne, hau mu je" Hawa nayi ya ja muka nitsa. Ya Allah birni ma rahamane, kwazazzabo muka dinga shiga, acaÉ“arnan tana sama tana Æ™asa damu tamkar zamu kifa. Ƙarafan acaÉ“ar na riÆ™e dam, na runtse idandunana inata karanto adda'a,. Ga Æ™urar jar bushasshiyar rairayi data cika mun idona da hancina dam. Wallahi na É—auka kafin in sauka daga acaÉ“arnan zamu rikito mu afka wani Æ™aton ramin, babu kwalta ko guntu. Bani na buÉ—e idona ba har sai da mai acaÉ“a yace. "Mun iso madakata fa" kana na buÉ—e idanuna a hankali na ganni a tashar Æ´an acaba. A mugun gajiye na sakko daga acaÉ“ar tare da sallamarshi. Jarabawar dana samu duk yaro ko yarinyar da na tambayeta inane gidan Modibbo Yuguda mai nagge. Sai dai su bini dana mujiya basu iya yaren hausa ba, ni kuma ban iya fullanci ba. Ga duhu ya soma doso kai. Wata baiwar Allah ce ta ja hannuna zuwa gidan wani dattijo. Bayan sun yara yaren fullanci mai daÉ—i da garÉ—in saurare sai ya fuskanceni cikin gurÉ“atacciyar hausa yace. "Gidan Modibbo Yuguda mai nagge kike nema ko yarinya? Dan Æingel tace iyakar abunda ta gane a bayaninku kenan" E gidanshi na zo Baba. Ni Æ´ar wajen matarshi Daso ce, yayar su ÆodÉ—o ce daga birnin Kano " Baki ya rike tare da girgiza kanshi, ya dubeni da mamaki maÉ—aukaki yace. "Kika ce ke Æ´ar Daso ce kuma daga birnin Kano, to Daso dama tana da wata Æ´a?" Take naga ya sauya kala daga fara'a zuwa kicin_kicin. Wata dattijuwar fara sol É—in bafulatana mai yala yalan gashi ya kirawo ta shiga dani cikin asalin gidan. Bayan yace mun zai tura yanzu a tawo da Dadan. Cikin wata bukka aka shiga dani, sai da na sunkuya sosai kafin na iya shiga cikin bukkar, irin gidajen da suke dashi kenan a rugar . Ban taÉ“a ganin É—akin gargajiya a zahirance ba sai yau, É—akin ya burgeni ya Æ™ayatar dani. Jeren Æ™orene kyawawa masu zanen tsuntsaye da masu zanen Æ™adangare gasu nan iri iri an mammanna su a jikin bangon bukkar. Daga kusurwa biyu kuma wasu Æ™waryane hawan hawa a jejjere ko wanne anyi mishi murfo da faifal mai kala_kala. ÆŠayar kusurwar kuma jeren kwallane masu hoton tsuntsaye da korayen ciyayi, ga wasu tukwanen Æ™asa a kikkife a gefe. Abun al'ajabi baya Æ™arewa sai gani ga gadon Æ™asa da katifar yayi. Ƙasan cikin bukkar kuma buhune aka É—inka aka shinfiÉ—a a matsayin ledar tsakar É—aki. A gefe na zauna Æ™uri ga duhu_ duhu a cikin É—akin. Wannan dattijuwar ce ta shigo hannunta rike da fitilar aci bal_bal, akwai wani É—an gini da akayi a saman É—akin kamar anyi gininne musamman domin ajjiye wannan aci bal_bal É—in. Bayan ta ajiye sai tace dani. "Use É“ilgel ( sannu yarinya)" Sai naga ta fita. Inaso ince zan yi alwala in yi sallah amman bansan me zance ba, dole haka nayi gum. Can bayan duhu ya mamaye sararin samaniya duniya tayi baÆ™i Æ™irin sai na jiyo muryar Dada. Murya mai zaÆ™i da siranta, muryar dake raunata zuchiyata take kara mun so da tausayin uwata. Cikin bukkar ta shigo da sallama. Tana saye da wata iriyar jemammiyar atampar dana taÉ“a sai mata a shekarun baya. Sai É—an wani yalolon tattararren mayafi mai ruwan Æ™wai. Ƙafafuwanta kuwa duk Æ™ura. Idanu ta Æ™ura mun Æ™ur, sai naga guraben idanunta tab da ruwan Æ™walla. "Jabu kece a Jaɓɓi lamba a darennan? Kinsan fa kin tambayeni zaki kawo mana ziyara nace miki a'a. To me yasa zaki yi gaban kanki ki zo, ita kuma uwar taki ta barki bacin tasan...." Sai ta ja bakinta ta tsuÆ™e tare da sauke gwauron numfashi. "Tawo mu tafi to, kawo jakar in riÆ™e miki" Ta kai hannunta zata É—auki jakata nayi wuf na É—auka. A'a Dada zan É—auka. Kuma kiyi haÆ™uri dole ce tasa na zo gareki, dole ce tasa Iyaa ta barni nazo, ba a san ranta na tawo ba" Duk fa maganganunnan da yarbanci muke yinshi. Babu dai abinda tace dani sai naga ta sunkuya ta fice. Bayanta nabi muka fita, muna tafe a jere da juna abinda bamu taÉ“a yi ba kenan. Tiryan_tiryan mu kaiya tafiya, muna wuce samari da Æ´an mata. A yadda na lura kab garin gidajensu iri É—aya ne, gidajen bukka zagaye da jinka, basu da dangar gini ko da na laka ne. Wani gida muka shiga Æ™atoton gaske, mata da yaran gidan nono_nono kowa ya ja zugar abokan hirarshi. Ga aci bal_bal kashi kashi, sai fullanci akeyi ana dariya. Mijin Dada yana zaune akan tabarmar keso da rediyo a gabanshi yana ji, ga abinci da kofi a gabanshi. Sallamar Dada yasa wani yaro namiji da Æ´ar budurwa suka nufota da sauri suna faÉ—in. "Use Dada" ( Sannu Dada) Mijinta ya juyo ya dube ni, ya dubi Dada dana fuskanci tun shigowarmu jikinta yake rawa. "Je ki gaishe da Babanku gashi can" Ta dubi wannan Æ´ar berar da tazo ta tareta sai tai mata yare. Shi kuma namijin sai ya amshi jakar hannuna, ita Æ´ar budurwar kuma tai mun jagora zuwa wajen mijin Dada, gashi ni ban iya Fullanci ba. Haka dai na durÆ™usa a gabanshi gaisuwar dai ta kurame mu ka yi, sannan muka zo mu ka tarar da Dada tsaye inda muka barta ta nausa a cikin tunani mai nauyi, har sai da Æ´ar rakiyata ta jijjiga hannayenta. "Dada am" Tace kafin Dada ta dawo cikin nutsuwarta, bayan ta ja fasali sai ta dubeni tace. "Mu je in kai ki ki gaisa da abokan zamana" Binta nayi a baya ta nuna musu ni, nai musu gaisuwar kurame biyu a cikinsu suna É—an jin Hausa sai muka gaisa da kyau. Daga cikin Æ´an mata da yaran gidan ma suna jin Hausa hakan yasa na É—an ji sanyi. Amman bansan me Dada tace dasu a kaina ba ni dai. Zungul_zungul na bi bayanta har cikin bukkar da nake da tabbacin nata É—akun kenan. Babu komai a É—akin sai tarkace kawai, sai gadon Æ™asa da katifar yayi taji zanin gado. A bakin gadon tace in zauna. Bayan na zauna Dada sai ta fita. Wannan budurwar kuma tana wajen tulu tana É—ebo mun ruwa a Æ™oÆ™o, bayan ta bani na sha, sai nace. "Inason zan shiga bayan gida, banyi sallar la'asarba Æ™ila isha tayi ma ko?" "E muma mun yi sallar Isha. Muje in kai ki" Cikin gurÉ“atacciyar hausar da ba ko wacce nake ganewa ba tayi maganar. Muna fitowa tsakar gidan sai muka tarar da Dada da abokan zamanta a tabarmar da mijinsu yake zaune. Sai faÉ—a yake zubowa yana ambaton Daso_Daso. Jikina tuni ya bani a kaina ake tattauna maganganu, da jin Æ™arfin muryar kuwa ba magana bace ta daÉ—i. Na sake gasgata hakanne da na ji muryar Dada na rawa, da kuma irin yanda kab yaran gidan su kai ciko_cirko kuma suka Æ™ura mun idanu kamar maye yaga jariri. MRS BUKHARI NAMA YA DAHU.... ROMO ÆŠANYE BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI