← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 237

Sashe 140

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sai yaushe Hamma zaka sake kawo mun Jabu zuwa na musamman? Na yaba da'ita sosai, kaga har Halima ƙanwata tace tana sonta da ƙawance naga har adireshin juna suka karɓa, ita tana aure a Girei ne" Ɗan murmushi Yaya Hamma yayi ya sauke kai. Hama ai saita haɗe fuska tai kicin_kicin. "Hajiya zan kawota duk ranar data shirya in sha Allahu" "To to Shikenan. Jabu zannuwan gadon zasu kai guda nawa wanda ya rage miki?" Ta tambayeni. To gaskiya da yawa dila guda na buɗe, sai dai ki faɗi guda nawa kike so" "Kice Hajiya ce. Ko da yake Hamma ya ba Alhaji labarinki lokacin baki dawo saudiyya ba. To a ba Hamma guda talatin ya kawo mun, zai tawo miki da kuɗin" Faɗin da Hajiya tayi Hamma ya sanarma Alhaji oganshi labarina ba ƙaramin kura Hajiya ta kwanto ma Yaya Hamma ba, dan sai kallon Hama yake yi a _ido_a_ido. Tako turɓune fuskarta, daga ƙarshe ma wajen ta bari sai a bakin get muka taddata, muka koma gida duk a gajiye, ni dai da nasan ba kwanana bane, ɗakin Yafendo na leka nai mata sannu da gida nayi shigewata ɗaki. Nasan masu jiran abincina dole suna can suna jira, dole na kunna risho na ɗaura macroni fara. Ina kan dafawa saiga me sunan Yafendo ta shigo bako sallama da roba a hannunta an shaƙo shinkafa an camɓala miyar akwai. Hancin yarinyar du majina, kayan jikinta kuwa du ƙura. Kije kuci ke da ƙannenki kinji yarinyata" Bata jin Hausa ni kuma fillancin nawa baikai yadda zan mata bayani ba. Ta dai fita da abincin ta mayar. Ina zuba ma Yusufu da yazo yanzu abincinsu dana gidan Dada sai Hama ta fado ɗakin bako sallama har tana tuntube da ƙafar Yusufu, daga ita sai ɗaurin ƙirji. "Na aiko yarinya kin dawo da'ita ina cin abinci kinsa an tasoni" Tana magana sakaka kamar goyon kakannin. Murmushi nayi nace. Na riga da nayi girki ki karama yaran suci" Saita fice fuu. Washe gari sai rigima ta kaure tsakaninta da Hamma. Ashe tunda aka kawoni aketa faman rikicin dole sai dai mu dinga yin girki ɗaya kamar yadda mijin yake ɗaya. Kunsan ƙauye suna da riƙo da al'ada, rikici har gaban Yafendo ita kuma a ƙoƙarinta na son a zauna lafiya sai tace. "Tunda dama hakan akeyi, kuma daga yau kuyi hakan banason wata magana kuma. Ke Jabu ki soma girki da abokiyar zamanki tunda girkin naki ne yau. Ke kuma ki sani akwai kwanon ƙannenta dana mahaifiyarta da ake sama abinci saiki dinga sa sanwa dasu. Banason ƙara jin wata fitina." Inaji ina gani haɗa girki ya tabbata. A ranar ansha waƙe a tsakar gida kafin su fita tallar nonon. Na shige ɗaki naci kukana na share hawayena ni bansan ta yaya zan iya ɗanɗana girkin Hama ba. Mai gayyar ya dinga rarrashina kafin ya tafi aiki. Da zai fita sai Hama sai taga mun fice tare, sai hankalinta ya tashi. Ina ganinta har ƙofar gida ta fito bata koma ba saida muka yi kwana. Ni kuma zannuwan gado na kwasa a gidan Dada na bashi zai tafi ma matar Oganshi. Na jido kaya Kari ta tayani muka kawo gida, daga haka sai muka ɓige da hira har wannan baiwar Allah mai sarin dogayen riguna ta iso. Tako sari riguna sosai ta caskemun kuɗaɗena kuma tace. "In sun ƙare gobe ma zaki iya ganina na dawo. Yola zan kai kayan gobe akwai cin kasuwa, ko mai mutum yakai ƙarewa yake yi." Nan tai mana sallama dai Gaga_gaga haka ranaku sukaita zama wata, al'amura sunata sauyawa. Tunda muka haɗa girki, duk ran girkin Hama su Dada basa samun abincin arziki. Sannan karfa ku mance ita Hama abincin dare dana safe kawai take yi da rana dole ni in ɗaura tukunya in girka, daga baya ne na dena girkawa sai dai in dama mana nono da fura musha, ni da kaina nake tatsar madarar in mayar da'ita nonon. Duk kwanan Hama abincin da take kawo mun saita bado magani a ciki. Ni dai ban taɓa ci ba, hatta banɗaki in zan shiga saina sake wankewa sai inga garin magani a kasan bayan gidan an barbaɗa mun. Har wata baƙar laya na tsinta a tsakiyar gadona, na ɗauketa da bismillah. Karambani irin nawa maimakon in cillar saina buɗe layarnan. Zanen mace na gani a jiki, an caccaka mata abu a mararta, sai gashi silli ɗaya, da ƙwayar barkono guda bakwai. A shara na cillar na ja bakina nayi shiru. Ta ɓangaren Yaya Hamma kuwa ina ganin soyayya ta haƙiƙa na fahimci ɗakina ya mayar dandalin nishaɗi da nutsuwa, dan kullum sai yayi mun waƙar soyayya. Soyayya ta yi soyayyar da duk ran asabar da lahadi ina rakashi kiwon shanu, sai in dafa mana abinci insa a wata jaka da ruwa da komai in bishi mu kutsa jeji muna tafe muna hirarmu ta soyayya. Da wannan soyayyar na jawo ra'ayinshi na askeshi tas yana noƙewa ni dai ina sara. Kunsan Allah sai da yayi zazzaɓin wannan aski da nayi mishi, wajen har kumbura yayi na kwana biyu kafin ya saɓe. Wanka kuwa Alhamdulillah yana yi, yana goge bakinshi, kayanshi na ɗakina suna samun wanki mai kyau har turare nake fesa mushi. Kayayyaki kuwa sai karɓuwa suke yi a_ hankali _a_ hankali kaya nata tafiya. Harna sake sayo Shanu, na sake siyo tunkiya inata kiwon abina, Kari kuwa ta koma tallar Nono tana girkinta ita da Dada, amman hakan baisa an dena zuba ma Dada abinci daga gidana ba, haka su Cubu. Matar ogan Yaya Hamma kuwa ya kaini naje na wuni mata, da zan dawo ta hadoni da goma sha tara na arziki. Ƙanwarta Halima naje mata itama tazo mun. Ashe layin su ɗaya da layin da Daso take aure. Gidanta yafi ko wanne gida kyau a unguwar. Dake Yaya Hamma ne ya kaini shine yake nuna mini gidan Dason. Da yamma da yazo ɗaukata sai muka ratsa bata dawo talle ba. Gaga_gaga dai anata tafiya ana ƙarawa da haƙuri da kawar da kai. A cikin matan ƙannen Hamma Safiya ce kaɗai muke shiri, duk sauran basa shiga harkata bana shiga tasu harkar, sun haɗe ma Baɗɗo kai ta dena jin daɗin zaman gidan. Ba dama tazo ɗakina ko ni in shiga nata ɗakin sai tsogumi a tunaninsu sai gulmace zata haɗamu. Dan a zauna lafiya sai nace da'ita tayi zamanta ma dinga haɗuwa a gidan Dada. Amman in na ɗan dafa abin ɗaukani ina zuba mata, harsu matan gidan ina basu kuma su lashe, amman saidai in ɗauki kwanono a bakin rijiya an yasar mun dashi. Wata ranar juma'a nice da kwana, gaga_gaga na gama aikin tuwon dare na sallami kowa, Hama na bar mata nata a kitchen dama anan nake ajjiye mata inta dawo ta ɗauka. Na shalla wanka, jiki ƙamshi ɗaki ƙamshi ina harɗe misalin tara na dare Yaya Hamma ya shigo. Me zai faru, kamar yadda na saba tarbarshi da gudu in rungumeshi haka naje, duk da yana tsantsar jin kunyar hakan amman yanaso dan bai taɓa hanani ba. Ina isa wajen sai ya ja da baya yace. "Dakata karki taɓani" Ai sai nayi dariya a tunanina ko zolayace ashe da gaske yake, saida na rungumeshi sai ya ɓanɓareni a jikinshi harda jan tsaki. Da ƙyar na juyo na zauna a gefenshi ba guiwa. Lafiya wani abun nayi, ko wani ne ya ɓata maka rai a waje?" "Ba wanda ya ɓata mun rai, dan Allah ki rabu dani banason surutu" Yana faɗar haka saiya koma kan gado yayi kwanciyarshi. Banfa daddaraba na juye ruwan wankan dana sabar mishi na kai mishi banɗaki. Yaya Hamma na kai maka ruwan wankan" Ba sai ya kawo mun mari ba, nayi maza na kauce ya mari iska. Ai sai hawaye shar_shar_shar." Sai ya shiga faɗa yana zage_zage ni bana sanin ma abinda yake cewa. Wallahi Allah ana cikin haka sai firit Hama ta shigo itace harda zama a bakin gadona. "Menene nake jiyo hayaniyarka, wani abunne?" Ai saina zama ƴar kallo suka zame mun sinima su kuma. Sai ya shiga jero mata bayani, wai daga shigowarshi na ɓata mishi rai, kuma yace in rabu dashi saida na sake yi mishi magana". Uwar kusasu ta samu abinda take so. Saita shiga rarrashinshi, kunga har ƙirjinshi take shafawa. Bantaɓa sanin haka kishi yake da zafi ba sai yau. Dan har wani duhu_duhu nake gani, ji nake kamar in dira a wuyan matsiyaciya. Sai idanu na runtse wata gobara na ruruwa a zuchiyata. Tunda na runtse idanuna inaga tun tara da rabi, bani na buɗe ba sai goma da minti goma,minti arba'in tim nayi. Wannan rufe idanun da nayi Allah kawai nake ambato dan nasan shi kaɗaine zai kawo mun agaji, har ita alkinkimar ta fita ni banma sani ba. Shiko Yaya Hamma yayi bacci abinshi harda minshari, niko ina zaune ga kayan abinci a gabana inata tubka da warwara, amman na kasa gane dalilin fishin daya zama sababin wannan tashin hankalin. A zaune a wajen bacci yayi gaba dani. Cikin dare na tashi naita adda'a ina roƙon rabbissama wati war ardi ya kawo mun ɗauki na shiga tsaka mai wuya. Ina zaune ina salatin Annabi har aka kira assalatu. Abinda yafi bani mamaki har ana niyyar shiga sallah Yaya Hamma baiko motsa ba. Abinda bai taɓa yi ba, ana kiran assatu yake miƙewa. Yaya Hamma, Yaya Hamma lokacin sallah yayi za'a shiga Masallaci " Hmm kunsan daya tashi a zabure me yace dani? Abun da ciwo cewa yayi. "Ke mahaukaciyar inace, haka a gidanku aka koya miki tashin miji marar tarbiyya" Haka fa yace mun Ita zuchiya bata da ƙashi, raina ya ɓaci idanuna sun rufe sai nace. Ni ina da tarbiyya Allah dai ya baka haƙuri naga zuchiyarka a kusa take, ko lefin me nayi oh...." Ba sai jini ba, a ina? Naushi ya kaimun a bakina, zafin ya ratsani kau. Kafin in tare naji yana dukana takota ina ya samu tsoka. Niko bakina na toshe da hannayena bibiyu ina gudun kar kishiya ta jiyo ihun ana jibgarka taji dadi. Saida ya dokeni iya iyawarshi ya fice. Saina durƙushe na saki kuka marar sauti. Idona a kumbure, guda ɗaya, dishi_dishi nake gani dashi, dan mugun naushi Yaya Hamma yaima idon. bakina na ma haka, jikina yayi laushi, gashi
Chapter 140 · 0% Book details