Sashe 232
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
yace wai kizo ki sameshi a waje." Yayi mun raɗa a kunnena. Hajja Mama ta jawoshi tace dashi. "Ka je ka kirawo mun Nana ja'ira tunda ta fitar mun da waya ban sake ganinta ba. Ni dai miƙewa nayi da ƙyar sabida ƙiba danma ina motsa jiki sosai babu kasala a tare dani, dan wuni nake yi zirga_zirga a asibiti. Matan gidan na ratse na nufi hanyar waje. Wasu mata da suka shigo na bangaji ɗaya a cikinsu, kaina na juye ina kora Nana cikin gida tana son zata bini. Ita wai dole zata yi magana da Abbansu. Da sauri na juyi. Subhanallaah dan Allah baiwar Allah kiyi haƙuri " Na sa kai zan wuce naji ta riƙo hannuna. "Iyabo wai ko ba ke bace, duk da dai Iyabo bata kai farin haka ba, kuma ƙibarta ba haka ba" Na dubi wannan mata na maya. Baiwar Allah sunana Iyabo. Amman ban wayeki ba. "Allahu Akbar Iyabo Uwani Tabalbalin ce ƙawarki. Dama kina raye baki mutu ba. Tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikai." Usman ne ya shigo gidan. A lokacin ni kuma kaina ne yake jujjuya mun, sunan Uwani Tabalbalin yana ta mun amsa kuwa kawai. Abubbuwa suka shiga hasko kansu a ƙwaƙwalwata, lokacin da na baro Jaɓɓi lamba afujajan da goyo nake hangowa ina tafe ina waige. Rayuwar da muke yi da Usman sai sake hasko mun yake yi, Yaya Hamma na tuno, da ƴan biyu na. Ba shiri na runtse idanuna kaina kuwa kamar zai tarwatse dan nauyi. "Ko itace ƙawarki da kike bamu labarin ɓatanta?" Cewar Hajiya Mansa kenan. Itace kimanin shekaru goma sha bakwai da ɓatanta" Kar ku daɗa kar ku raga. Sai na soma hango sanda na goya ƴan biyun yarana a baya na fice cikin dare. Da furucin da Hama ta yi akan saina bar Jaɓɓi lamba a haukace tsirara ma. Ina buɗe idanuna na gane Uwani. Hannuna yana rawa na nunata Tabalbalin kece. Na shiga uku me yasa to na sake wani auren bayan Hamma ne mijina?....." Ban sake sanin kaina ba ashe sunewa nayi ni. Ban tashi farkawa ba sai biyun dare na buɗe idanuna na ganni a ɗakina a kwance ga ƙarin ruwa a hannuna. A wannan sumar ƙwaƙwalwata ta shiga saiti, tare da tariyomun duk rayuwata ta baya. Da ma wanda na gudanar bayan barina jaɓɓi lamba. Hakan yasa a mugun firgice na farka. Uwani, da Hajja Mama, da Usman duk suna kaina. Da uwani muka haɗa idanu ina hawaye, na dubi Usman shima ni yake kallo, wallahi idanunshi yadda kuka san an zuba jini dan tsabar ja, hatta fuskarshi ta koma jawur sai jijiyoyi raɗa_raɗa Ai sai na fashe da kuka kawai ina salati, hankalina ya dawo jikina, kuma wata ƙudura ta Allah, duk rayuwar auren da mu ka yi da Usman yana kaina bai goge ba. Ina Hamma uwani, ina Dada?" Da sauri suka yo kaina nayi sauri na runtse idanuna jin ƙamshin turaren Usman a kusa dani. "Iyabo Hamma yananan a iya tsawon shekaru goma sha bakwai da ɓatanki babu abinda ya sauya na dangane da sonki a zuchiyarshi, har yanzu yananan bai yi aure ba. A kullum adda,arshi Allah ya bayyanaku ke da yaranshi. Ashe wani babbar ƙaddarace ta aure da ƴaƴa ya fitar dake Iyabo. Yau gaki da auren Usman kina a matsayin matar Hamma." "Hasbunallah. Astagrifulla" Muka ji Usman yana ta nanatawa. Tare da shassheƙar kuka na tashin hankali kamar wani ƙaramin yaro. Hajja Mama kuma sai ambaton "Kaico_kaico take yi. Hankalinta har yafi namu ma tashi wallahi. Da ƙyar na buɗe idanuna da su kai mun nauyi, zuchiyata sai dakawa take yi, a halin yanzu babu mahalukin da yake bani tausayi sama da Usman. So zuntsuritunshi wallahi ina yi mishi dan yayi mun dukkan halacci. Tattaunawa yake yi yana shirin fita. Uwani taje da sauri ta taroshi. "Usman kar kaje ko ina. A halin yanzu Iyabo tana buƙatarka fiye da kowa. Dukka wannan abun wata aya Ubangiji ya saukar in mun gane. Usman kayi ma Allah ka dawo ka zauna" Ruwan dake hannuna na zare na sakko, ko kafa ban ɗaga ba na faɗi yib. A zabure Usman ya juyo ya tallafoni zuwa jikinshi. Wata iriyar ƙanƙama nayi mishi ta haƙiƙa. Kallona yake yi hawayena na jiƙa ƙirjinshi. Wata dariya yayi, mai haɗe da kuka lokaci guda. In sakeshi wallahi na kasa, shima ya sake ni ya kasa. Uwani ce tazo ta riƙo hannuna na tashi da ƙyar, a lokacin hannuna sai zubar da jini yake yi ashe harya ɓata ƙasa da jikin Usman. Da sauri ya fice a ɗakin yana fita na lumshe idanuna ina rera nawa kukan. "Ohh Allah. Iyabo ki yafe mun haƙiƙa banyi aiki da tunani ba, idanuna ya rufe burina kawai ki auri Usman. Ashe ke da aure a kanki ban sani ba. Allah na tuba." Likita ce ta shigo ɗakin ta mayar mun da ruwan dana zare. A lokacin jikina yayi wani irin mugun zafi, kaina da idona ciwo kawai suke yi mini. Idanuna na lumshe ina tuno rabuwata da Hamma na ƙarshe a lokacin zasu tafi ciranin kiwo. Wasu zafafan hawaye suka sulalomun Na sake tuno lokacin da nake da cikin Alhaji ƙarami. Irin laulayin da nayi, da irin yadda nake wanke Usman da amai, da wahalar da yasha. Da kuɗi daya kashe ya bani ilimi, ya saka yara a makaranta mai daraja. Da ƙyar na buɗe idanu na dubi Uwani da hajja da duk suka ruɗe sai sannu suke yi mun Murmushin dole nayi musu kawai.