← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 237

Sashe 45

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruga

Iyabo:.
Tabarma Daso ta ɗauko ta shimfiɗama Yaya Hamma daga can gefe guda. Jatau ne ya shigo da garken shanunshi guda yana tafe yana waƙar fullanci, hannunshi da ƴar tsaraba.
"Jatau yau kai ka soma shigowa gidan?" Da Hausa tayi mishi wannan tambayar. Shi kuma hankalinshi duka yana kaina, ina son in ɗebo ruwa a randar ƙasa in kawo ma Yaya Hamma.
"Baƙuwa mu ka yi ne Daso?"
"E baƙuwa ce kuma ƴar gida, Yayar su Boɗɗo ce tazo daga birni"
Sai ya washe bakinshi muka gaisa cikin girma da arziki. Na dure ma Yaya Hamma ruwan sha a gabanshi na koma kan turmi na zauna. Jatau da Hamma nan suka kacame da yare, daga bisani Jatau ya wuce da shanunshi izuwa maÉ—aura.
"Jabu zo ki zauna sabida ke nazo gidannan da yammannan" Daso dake hura wuta tace.
"Ko ni na faÉ—a a rayina, sabida Jabu ne kazo Yaya Hamma"
Sai tayi murmushi, nima murmushin na mayar mata, na ƙarasa kan tabarmar da Hamma yake na zauna a gefe.
"Na ji labarin mutuwar aurenki ƙanwata. Abun ya dake ni ainun, naji tausayinki sosai. Amman mu zamu baki farin cikin da har sai kin mance da komai a matsayinmu na dangin uwa, muma zamu taka tamu kalar rawar, tunda kika zaɓi ki rayu damu a ruga, kika haƙura da rayuwar maraya duk da acan ki kai wayau. Kiyi haƙuri kinji am?"
Wasu hawaye ne suka gangaro mun. Ban aune ba sai kuka mai gunji ya tawomun babu zato. A tiɓi tiɓi_tiɓi da kayan mazaunai na shige bukkarmu na zauna akan gadon ƙasarnan na shiga sana'ar kuka. Wani tuƙuƙin baƙin ciki da takaici sai yanzu ne komai ya soma dawo mini. Kuka na zage nayi na ban mamaki. Ƴan uwana suka bani sarari na dirji kukana yadda yayi mun nayi shiru dan raɗin kaina. Sai zuchiyata ta ɗan washe ta rage nauyi. Na yi zaman tunani a zaune bansan iyakar adadin ba. Sai shigowar Yafendo na gani kawai. Da sauri na share guntun hawayena ina duban fuskarta. Sai naga fuskarta cike da damuwa, da dukkan alamu damuwa da damuwata ce take yi. Ledar hannunta ta miƙo mun nasa hannu na karɓa kafin tace.
"Ban isa hana ki kuka, ko hanaki damuwa da tunanin yaranki ba Jabu. Kinga Daso tun bayan rasuwar mijinta kullum sai ta yi kuka zuchiyarta babu daɗi. In Hamma yazo gidannanne ma take samu tayi farin ciki. Ni kuwa ban taɓa hanata kuka ba. Rabuwa da miji ciwonshi bashi da misali sam, musamman mijin da kuke soyayya da zaman lafiya. Ace mutuwace tayi muku yankan ƙauna. Ko kuma wata ƙaddararce ta raba ku ba da son rayukanku ba. A lokacin da mahaifinki ya rasu Adda Daso ta shiga wani irin mawuyacin hali. Mahaifiyarki har jinya sai da ta kwanta na tsawon wata shida masu kyau. Har gaban abada ba zata dena tunanin mahaifinki ba. Musamman data haɗu da azzalumin namiji magoki. Da girmansu haka bai bar dukansu ba. Zuwan da ki kayi ma dan kawai ta roƙeshi ya barki ki zauna a wajenta har ki gama kwanakinki ki tafi. A daren zagi da cin zarafi babu wanda baiyi mata ba, har marinta sai da yayi"
Da mugun sauri na ɗago. Wata kibiya ta soki ƙawon zuchiyata, siraran hawaye suka gangaro kan kumatuna masu zafi.
Yafendo yanzu kamar Dada da girmanta da yaranta manya sai mijinta ya daketa harda zagi, a halin da take rayuwa kenan?" Zama Yafendo tayi a kusa dani tace.
"A haka Adda Daso take rayuwa da azzalumin mijinta. Har da tsohon ciki a jikinta dukanta yake yi. Ko a cikin Boɗɗo yayi mata wani dukan da tai ta zubar da jini, duk muka cire rai da cikin. Sai daga baya cikin ya tashi. Amman sai da Boɗɗo ta shekara biyu cir a kwance a cikinta kafin ta haifeta. Wannan kuma ana tunanin da sa hannun uwar gidansu akan lamarin. Kuma ya karɓe shanunta na gado ya haɗe da nashi shanun, Adda Daso bata ribatar komai. Shanune masu tarin yawan gaske, kinga gaa nawa garken can Jatau ya dawo dasu, sai hauhawa suke yi. Ita kuma bata san adadin yawan haihuwar da nata shanun suka yi ba, dan nata mata ne, namijin guda ɗaya ta samu. Ke Jabu in nace zan ta baki tarihin mijin mahaifiyarki zamu kwana mu wuni a nan bamu ƙare ba. Shi yasa ko da yaushe take cike da tunanin marigayi mahaifinki. Soyayya da kulawar daya bata ne, yasa ta fifita soyayyarki fiye da soyayyar duk yaranta. Duk ɗan abinda ta samu burinta ta tara in zata kai miki ziyara ta miki hidima, kinji na rantse miki tun bayan rasuwar mahaifinki ban sake ganin annuri akan fuskar Adda Daso ba, sai yau data zo gidannan tana sanar dani zuwanki garinnan, damma a hakan ta kwana cikin tashin hankali akan mijinga."
Kukane yaci ƙarfina, zuchiyata sai luguden daka take ta faman yi. Ina jin duniyata na wujijjiga rayuwata. Tausayi da zunzurutun kaunar Dada ya sake ɗamfaruwa a raina. Yafendo ta dafa ni nayi firgigit na kalleta.
"Ki tashi ki É—auro alwala ki yi sallah. Wannan ledar dana baki Hamma ne ya ce a baki. In ki ka yi sallah sai ki fito tsakar gida in gabatar dake ga Æ´an uwanki"
Jikina a sanyaye na ɗauro alwala nayi sallah. Na daɗe ina adda'a, a lokacin zazzaɓin dake jikina ya rabkeni ainun, ko idanuna bana iya buɗewa. A halin da Daso ta shigo ta same ni kenan. Abu kamar da wasa_wasa sai na rasa numfashina, jikina kuwa kamar garwashin wuta. Sai da na shafe tsawon wata biyu da kwana goma sha ɗaya cur a kwance babu lafiya, sai maganin gargajiya akeyi mun, hatta ruwan wankana da ganyen magani a ciki, kuma Yaya Hamma suke kawo mun magani da ɗan abinda zan sa a bakina, Yaya Jatau ma yana kawo mun ɗan abun kwaɗayi, matarshi ma kullum zata shigo ta duba lafiyata, kuma in Yafendona, da Daso sun tafi tallen Nono, Hari itace ke zama dani matar Jatau. A wannan jinyar naga gatan dangin uwa. A wannan kwanciyar sai da dangin Dada suka zo kab suka gaisheni da jiki, a lokacin na gansu suka ganni. Dada kuwa kullum cikin suntiri suke ita da su cubu da Yusufu, Boɗɗo kuwa da hama suma kullum babu fashi sai sun zo dubani. " A cikin wata uku cib jikina yayi ƙwari babu laifi, lokacin iddata ta cika cib, lamarin da ya ɗan ƙara jagula lafiyar jikina kenan, sai da Yaya Hamma ya dinga bani baki, tare da lafuzza tausasa, har mamaki nake yi in naji yana furta wasu lafuza masu kwantar da zukata. Da yamman wata asabar bayan Daso ta dawo daga tallar nono muna ɗaki mu na ɗan taɓa hira, fuskarta cike da farin cikin ganin jikina yayi kyau yau. Duk da na rame fiye da tunanin masu karatu, fuskata ta yi fayau. A jinyar dana kwanta na samu kulawar mutane uku da bazan mance da hidimar da su kai mun ba. Daso, Yaya Jatau, Yaya Hamma. Duk kwanan duniya Daso itace mai bani abinci a baki, tare da gyara mun kwanciyata, ko amai nayi itace ke kwashewa. To a wannan kwanciyar jinyar nayi jinin al'ada hatta da tsumman jini da ɗan kamfaina Daso ke wanke mun da ruwan toka ta shanya su, wanda zai maka irin wannan aikin ba ƙaramin masoyinka bane. Yaya Jatau kuma kullum in zai dawo daga kiwo yana kawo mun wani gashasshen hanta mai yaji, shi nake ci da daddare, shi kaɗai ne nake iya ci ba tare da naji tashin zuchiya ba. Yaya Hamma kuwa shi ya dinga bin ƙauyuka ruga_ruga dan sama mun magani, wani gari wani ganye, ko kiwo yaƙi ya mai da hankali akai har sai da ya ga samuwar lafiyata. Kuma kullum a cikin yi mun nasiha da tattausan laffuzza yake. Muna ɗan hirarmu muka ga an buɗe labulen kaban dake ƙofar bukkarmu. Yaya Hamma ne ya shigo hannunshi riƙe da kwano. Daso ce ta miƙe ta karɓi kwanon ta dure a gabana tana dariya tace.
"Nasan ai nata ne ko Yaya Hamma? Shi yasa na dure mata a gabanta" Dariya yayi tare da nunata da yatsa yace.
"Kin ganki akwai zolaya. Ai itace marar lafiya a gidan, shi yasa na kawo mata tasha romo" Sai tace.
"Nima in na kwanta jinya ashe zaka kula dani sosai irin kulawar da ka ba Jabu?"
Dani da'ita duka sai muka kafe shi da idanu. Sai da ya zauna a ƙasa ya tanƙwashe ƙafarshi kana yace.
"Ai kamar ratayayyen hakkine a kaina in kula daku, ko da a gidan mazajenku kuke balle kuma kuna gabanmu.
Jabu ya ƙarfin jikin, yaya haƙuri ds rayuwa, da haƙurin zaman ƙauyanmu mara wuta balle ruwan daɗi?"
ÆŠan murmushi nayi nace.
Jiki Alhamdulillah sauƙin yana samuwa sosai. Babu abunda zance sai godiya. Kuma ina godiya da wannan ɗawainiya da kukaita yi dani" Bayan na bashi amsar na sauke kaina ƙasa.
"Ai ya zame mana dole, ki daina godiya ma Jabu"
Miƙewa tsaye yayi.
"Ba dai tafiya ba?" Cewar Daso.
"Tafiya zanyi. Dama abinci na kawo mata. In kuma ƙara ganin jikin nata. Amman dai ku shirya zuwa dare zan zo mu leƙa dandali Jabu taga yadda muke wasanninmu gwanin sha'awa, wala Allah hakan ya rage mata raɗaɗi."
Dariya nayi musu kawai. Aini na rabu da nishaÉ—i tunda na rabu da Gwadabe, dan nishaÉ—i na wajen tsuntsun soyayya. Amman a fili saina amsa da cewa.
Allah ya kaimu"
Ko dan in ƙarfafasu tunda burinsu suga na saki jikina na mance komai.
Da haka mu kai Sallama, bamu muka fito daga cikin bukkarmu ba saida mu ka sallaci sallar isha. A tsakar gida muka ci fsrfesun da Yaya Hamma ya kawo mini harda Yafendo da Jatau, dama Hari Matarshi.
MRS BUKHARI ce.
Chapter 45 · 0% Book details