← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 237

Sashe 66

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Hadiza.
Da sauri ta shiga É—akinsu har tana cin karo da Ine wacce suke shirin fita ita da mijinta sun kawo ma Baba Fhatsima ziyara irin ta godiya da angwaye suke yi.
Ganin mijin ƙanwarta yasa tai saurin share hawayen dake bin gefen fuskarta.
"Ango ka sha ƙamshi kune a tafe da daddarennan? Mu da muke shirin kawo muku ziyara"
A ladabce ya gaishe da Hadiza yana yi yana sosa kanshi.
"In kin gama kya same ni a waje ni kam" Yace da Ine wanda hankalinta yake kan Hadiza.
"Yaya Hadiza nifa fishi nake yi wallahi. Tunda kuka kaini ba wanda ya sake leƙoni ma" Ta faɗa a karaye yayinda Hadiza take kallonta da halamar tuhuma. Ganin hawaye na neman ɓallewa a idanun ƙanwar tata ne ya tabbbatar mata tana cikin damuwa, ko kuma kewar gida."
"Ki sha kuruminki dama gobe zamu je gidanki ni da Anty Badi'a. Yanzu dai kije ki samu mijinki karki barshi yaita jira" Ine tace.
"Bamu shiga cikin gidanba ma, yanzu dai zamu zazzagaya, amman munje ɓarayin su Yaya Tasi'u." Fitarta shigowar Auwala yana kwaɗama Hadiza dake shirin zama kira.
Shigowa yayi ranshi a matuƙar ɓace.
"Ke meye ya haɗaki da Gwadabe, da har yake kiranki kina ƙin tsaiwa? Ki sani wanki ne Gwadabe, kuma mahaifiyarshi ƙauna take ga Malam." Hadiza najin wannan sababi na Auwala sai ta saki rushin kuka tana faɗin
"Ni wallahi na fasa auren. Yaje can ya auri ƙanwar abokinshi. Ai ba sona yake yi ba. Malam ne ya cusani wajenshi" Duka Auwala ya kawo mata. Baba Fhatsima dake zaune tana kallonsu tace.
"Bita a hankali Auwala. Zo zauna inji meke faruwa haka uhm?" Zama Auwala yayi a ƙasa, yana dokama Hafiza harara.
"Ki buÉ—e baki kiyi mun bayani Hadiza. Menene ya haÉ—aki da yaiyen naki?" Hadiza ta kwashe yanda Gwadabe ya faÉ—a mata ta sanar ma Baba Fhatsima. Tsaki dogo Auwala ya ja yace.
"Ni nama É—auka wani muhimmin abune yanda naga Gwadabe duk ya damu. To sai me dan ba da ke kaÉ—ai yake soyayya ba, dama cewa akayi dan ke aka halicci Gwadabe ke ke kaÉ—ai?
Baba kinji fa abinda take cewa, wannan baƙin kishin nata ne yasa ta tsallake yaranta ta dawo gida. Tana da aiki ja matsawar irin wannan ƙazamin kishin bai fita a ranta ba." Shiru Baba Fhatsima tayi, tana sauraren ɓaɓatun Auwala, da sautin kukan Hadiza. Ajjiyar zuchiya ta sauke kana tace.
"Hadiza kina nufin ba zaki taɓa zama da kishiya ba ko me kike nufi? Bar ganin ina goyon bayanki Hadiza, ai in dai wai ke bazaki zauna da kishiya bane, to ya fiye miki sauƙi ki ƙare rayuwarki a gidan mahaifinki. Dani da Malam mun san bake kaɗai Gwadabe yake nema ba, kuma a haka muka ji yafi miki ki aureshi. Dan Gwadabe yarone mai hankali da kunya. Ke dai kiyi fatan kasancewa uwar gida a gidanshi kawai. Kai Auwala tashi yi tafiyarka, ka kuma cema Gwadabe ya kwantar da hankalinshi Hadiza mu muka bashi ita, duk duniya in banda ƙaddara babu wanda ya isa soke batun aurennan. " Tashi Auwala yayi ya dubi Hadiza yace.
"Yara basu ajjiye komai ba sai sakarci. Ni zan so ma Malam ya soma aura mishi waccan ɗin kafin ita. Gashi ita ƴar birni wayayya da'ita, kuma hankalinshi take janyewa sosai. Maza ki tsaya kallon ruwa kwaɗo yayi miki ƙafa" Baba Fhatsima ta daki ƙafafun Auwala dake son tunzura Hadiza.
"Ja'irin yaro, fice ka bamu waje" Ta faɗa cikin sigar wasa, fita yayi yana sake kambaba yanda budurwar Gwadabe take kulawa dashi a waya. Kuma duk dan ya tunzura zuchiyar Hadiza ne. Ai kuwa yaci nasara dan take zazzaɓi me zafi ya luluɓeta, sai hawaye idanunta yake fitarwa" Harara Baba Fhatsima ta doka mata tare da cewa.
"Shashasha maza dai ya gane kishi shine logonki kiga in baki faɗi ƙasa warwas ba. Ba'a ƙarin aure ni Malam yayi mun har kishiyoyi uku? Da banyi haƙuri ba ke kina ganin zan kai haka ne? Ai mace a gidan aure da jarumta akeson ganinta Hadiza. Dan Gwadabe ba ke kaɗai yake nema ba, ba hujja bace na cewa ke kin fasa aurenshi ba. Ai kina gani a cikin gidannan dama dariya suke yi ta mana. Ko baki ji Abinda suke cewa bane ɗazu da zaki je wajen Gwadaben? Ai kinji sarai. Maza dai ki ma kan ki shaidar da babu me iya goge miki ita na zafin kishi. Ni kinga tafiyata Malam na son ganinmu dukka a turakarshi, Allah dai yasa lafiya. Dan malam bai fiye haɗe kan matanshi ya tattauna dasu baki ɗaya ba, yafi gane ya tattauna da kowacce ranar girkinta" Tana gama faɗar haka ta sa kai ta fice ta bar Hadiza da jinyar zuchiya. Yayinda maganganun Auwala suka shiga yi mata amsa kuuwa.
"Ni inata wahalar da kaina na son ganin na burgeshi. Sai gashi ashe wata a waya kawai take jaye mai hankalinshi. Ni Hadiza zan iya zaman kishi a karo na biyu kuwa? Wallahi nasan mata Æ´an uwana da yawa ba zasui mun uziri ba
Wasu ma zagina zasu yi. Amman Ubangijin da yayi ni, ya yiku. Shi ya banbanta zuchiyiyoyinmu. Wata abinda tata zuchiyar ta É—auke, wata in akace sai zuchiyarta ta É—auke wallahi mutuwa za tayi. Ni Hadiza macece mai mugun kishi mai zafi, nifa ko baiwace na fi son ace tawace ni kaÉ—ai babu mai irinta. Kishi ni shine raunina nasan ko wacce mace da irin rauninta."
Chapter 66 · 0% Book details