← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 221 OF 237

Sashe 221

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Babu guiwa na ƙarasa gaban Hajja Mama nace.
Ku yi mun bayani yadda zan fahimta wani abun kuka gano ne Hajja Mama? Gara in sani tun kuna nan in auren ba mai yiwuwa bane in biku tun wuri"
Hajja Mama tace.
"Iyabo ke wai kinga kyau da girman gidan da matan Usman suke ciki kuwa? Ga motocinsu a tsakar gidan. Ke ko wacce da ɓarayinta. Ba wannan ba Matarshi ma fa kamar balarabiya ce dan gaskiya ba da fulani tayi kama ba, dan larabci ma take yi ma wani farin yaro. Baki ganta ba siririya kyakkyawa. Ɗakinta danƙare da kayan ƙawa. Wallahi ni sai na rainaki da kayan ɗakinki a cikin wannan gidan. Kinji dalilin tsoratarmu gaskiya "
Idanu na lumshe na sauke ajjiyar zuchiya mai nauyin gaske.
Harga Allah ni tunanina wani waje daban ya dosa.
Duk da dai labarin da suka bani yasa guiwata tayi sanyi take saina raina kaina da kaina. Ammam dana tuno da balarabiyar matar tashi nima ya ganni ya auroni, kuma da balarabiyar matar tashi yake shagaltuwa wajen kallona harma ya sanar dani nice ainihin zaɓinshi tun na ƙuruciya. Sai na sake sauke ajjiyar zuchiya. Hajjja Mama ta dafani tace.
"Amman ba wai ina nufin ki raina kanki bane ko mu mun rainaki ba a_a. Mun sanar dake ne dan ki sani ki san yaya ma zaki tunkareta duk da sauƙin ta ba tare zakuita zama ba. Duk da ganin tamfatsetsen gidannan yasa na soma tunanin zaiyi wuya Dr ya barki a India din_din_din alhalin ga sauran matan a gida Najeriya. Ina ganin hakan kuma kamar zai iya haifar miki da baƙin jini sosai a wajen matanshi. Ke dai ki iya takunki a sannu, kar yaje ya jawo miki baƙin jini a cikin dangi.
Ajjiyar zuchiya na sake saukewa a karo na barkatai dan ba ƙaramin tsinkar mun da zuchiya suka yi ba.
Hajja Mama ta daɗe tana yi mun hudubobi nasu na ƴan duniya, da dabarbarun zama da miji, da su kansu kishiyoyin, da kawar da kai akan duk abinda bai shafeni ba, wanda ya shafenin ma ta horeni da yin haƙuri.
"Amman fa bance ki mayar da kanki banza bane. In miji yayi miki yau kika ɗaga mishi ƙafa, gobe in yayi miki ki zaunar dashi ya fahimceki ki fahimceshi gaskiya. Haka suma kishiyoyin bana nufin kita shanye takaici yazo ya haifar miki da hawan jini a banza. Sannan ki gina kanki, dan gwal ɗinnan, dan filinnan kiyi ƙoƙari ki mallaka sabida halin rayuwa, miji zai iya sakinka, ko ya mutu, ko ya juya maka baya ma. In kana da naka na kanka abun yana zuwa da sauƙi. In akwai sana'ar da kike ganin ya dace acan ɗin in kuka nutsa sai ki gabatar mishi da sana'ar ki dinga turo kaya ana siyar miki ana tura miki kuɗinki, ko kuma ki dinga siyen kadarorinki kina gina rayuwarki.
Ta daÉ—e tana bani baki.
Washegari sassafe suka wuce sai ni da ƴan biyu ƙwalam, ra baƙunta na damuna, duk da ni daɗi naji ma da Alhaji Baba yace in yi zamana a nan. Tun kafin in ga matan Usman tsoronsu ya ɗarsu sosai a raina. Da dai na gaji da zaman bayan mun gama waya da Usman saina fita falon na tadda ƴar aiki tana ta goge_goge Hajiya kuma tana sama. Sai kawai na shiga kitchen na soma taya Luba abinci. Ni nayi ma Alhaji faten acca da jan wake, yaji Aleyiwo da hanta. Na dama mishi kunun acca na zuba a flaks kasancewar yana ɗauke da ciwon siga ire_iren cimsrshi kenan. Ina kan haɗa plate Hajiya ta sakko.
"Luba Alhaji zai fita kin gama ne?"
Ganina a kitchen É—in yasa ta faÉ—aÉ—a fara'arta.
"A_a Iyabo kece a kitchen? Ai da kin bar Luba tayi aikinta kin huta. Yanzu da Usman zai zo ya taddaki a kitchen da inya dinga mita a gidannan har sai mun gaji" Luba tayi carab tace.
"Nayi _nayi ta bari ƙi tayi Hajiya"
Hajiya ai ba komai. Dake ban saba zaman ba sai duk na gaji shine nace bari in kama mata aikin "
Murmushi tayi tace.
"Ikon Allah Luba kinga mun samu suruka mara son jiki. Matan yaran gidannan ko wani ɗan taro aka haɗa sai dai a siyo abinci a hotel. Ai ko Usman ne zai shigo ƙasar a hotel ake sissiyo abinci dan ganda."
Ni dai kaina na ƙasa ta gama shi mun albarka ta koma falo. Dani da Luba muka jera komai a babban daining ɗin gidan Alhaji Baba sai shi mun albarka yake yi tare da yabon abinda nayi.
Tun daga ranar na karɓe girkin Alhaji Baba a hannun Luba ni ke mai girkinshi. Yana ci yana jin daɗi sosai.
Kwanana Bakwai muka wayi gari yau su Usman zasu shigo ƙasar. Tun suna Airport muke waya dashi har zuwa shigansu jirgi kafin yayi mun sallama. Ina zaune kunyar in fita ince zan yi mishi girki nake ta yi. Sai ga Luba ta shigo da sallamarta.
"Anty Iyabo Hajiya tace in sanar dake sun tafi ƙauye ita da Alhaji Baba. Mahaifiyar mai wanki da gugan gidannan ce Allah yayi mata rasuwa, wai sai gobe zasu taso daga nan zasu biya wani wajen."
Ai sai naji daÉ—i sosai.
Ayya Allah ya jiƙanta nima yanzu nake son in fito ki taya ni girkin tarbar Usman ai"
Dariya Luba tayi tace.
"Tabb su Uncle yau har kitchen za'a shiga ayi mishi girkin tarba? Tabb shi da wata rana sai ya shigo ƙasar zai kwashi matan ya kaisu gidan cin abinci ma"
Mamaki sai ya kamani. Muna kitchen ina ferar dankalin turawa, Luba na zuba ma kaza nono da kayan ƙamshi tana bani labarin abubbuwa daya kamata ace na sani, da kuma yin taka tsantsan sosai. Ni dai mamaki duk ya bi ya isheni.
Faten dankalin turawa da niƙaƙƙen naman saniya nayi. Sai nayi shinkafa kaza . Nayi mishi zoɓo mai kyau yaji abarba da inabi bushasshe. Sai bayan la'asar muka kammala aikinnan na shiga wanka na bar Biyu tare da Luba a falo suna turara falon da turaren wuta. Sai da nayi sallar la,asar kafin na soma shafe_shafen mai da turarukan ƙamshi, da humrori harda humrar matan aure. Sai da na gama mulke jikina da Humrar matan aurennan na tuno sister Badiat Ibrahim tayi gargaɗi akan sai in zaka turakane zaka shafa ba'aso kowa yaji ƙamshin face mijinki, ko kishiyarki ba'aso ki shafa ranar kwananta gudun kar a shiga hakkinta. Dan wannan humra wani key ne na buɗe sha,awar ɗa namiji, hanyace ta sawa miji ya zamema matarshi ɗaye manna, tana da tasiri ainun. ( Babu boka babu malam wallahi Allah ɗaya ne babu wani abu na surkulle a ciki. Sanin aikine da sanin itatuwa masu tasiri ga ma'aurata. An sanmu Kanuri muna gaba_gaba wajen mallakar zuchiya da ruhin ɗa namiji ta hanyar ƙamshinmu na jikinmu, da ƙamshin gidanmu. Me so tayi magana ina ɗiba a ƙaramar kwalba dan kowa ta mallaki nata) ina cikin rabe ɗayan biyu kawai na jiyo muryar Usman yana wasa da biyu.
Gabanane ya yanke ya faÉ—i duk saina dibibice. Sake kayan zanyi ko in fita a haka kawai?
Luba ce naji tana kirana da ƙarfi babu shiri na fito ko mayafi babu.
Da matarshi muka soma haÉ—a idanu tana tsaye shi kuma yana zaune Æ´an biyu na cinyarshi sunata zillo.
Kallon sama da ƙasa tayi mun irin kallon tsantsar wulaƙancinnan dan a zahiri kyakkyawace baƙa mai dogon hanci da dara daran idanu. Idanuna na mayar kan mijinmu shima ni yake kallo amman kallon burgewa.
A hankali na tattako da fara,ata na wuceta ina karkaɗa abun duniyar da ni shi kaɗaine kyauna wanda nayi imanin ya girgizata ga ƙamshin humrata daya sumar da'ita. Saida naje daf dashi saina juya mishi bayan nawa ita na fuskanceta da dariyata.
"Antyna bari in soma dake barkanku da dawowa da fatan kun dawo lafiya?"
Na ƙarashe ina dariya. A zuchiyata kuma duk fa na raina kaina dan harna soma kokonto akan Usman.
"Lafiya lau Amarya ya baƙunta?"
Ta faÉ—a da salon cinye kishi. Kallon Usman tayi tace.
"Gaskiya ka iya zaɓe wannan karon lutiya kaji sha'awa kenan. Naga tana da ƙiba masha Allah"
Ni nasan magana ta caka mun. Shi ko gogan naka sai ya saki murmushi yana wani jin daÉ—i.
"Sannu da dawowa ango mijin Amarya ya hanya?"
Ai kafin yayi magana sai ta kwashe da uban dariya harda rufe idanu. Shi kuma yayi lub a kujera sai shaƙar ƙamshina yake yi idanunshi har sun sauya kala.
"Lafiya Honey meya faru?" Ya tambayeta murya ƙasa_ƙasa
"A_a ba daku bane a waya ne aka turo wani abun dariya shine ya bani nishaɗi. Ni kam ina buƙatar watsa ruwa"
Murmusawa nayi na bita da idanu, itama ni take kallo.
Zama nayi abuna ina jiran abinda zaice.
"To ko in kai ki gidane ni sai in dawo? Tun a Airport nace in kai ki gida kin ƙi. Gimbiya kaita masaukin ki ta watsa ruwa. Ina Luba taje mota ta dakko miki akwatinki"
Ni dai ina zaune ina kallonsu kar.
"A_a ta barshi kawai. Sai ka tawo dama na zaci Alhaji Baba na gidanne mu gaisa"
Tana gama faÉ—in haka ta yi ficewarta.
"Asma'u!! Asma'u!! "
Ko juyowa batai ba. Kallona na dawo dashi gareshi, ni yake kallo harda ƙanƙance idanunshi. Yayi wani kyau na musamman.
"Ya akayi Gimbiya. Duk kin kashe mun jikina da ƙamshinki sai wani kasala ke sakkomun. Kinyi kyau fiye da da. Da wanne turare kike amfani haka mai sanyin ƙamshi haka?
Murmushi nayi nima na juya da kyau ina kallonshi nace.
Da yaushe kenan yallaɓai?"
"Da kafin in aureki mana"
Dariya muka yi tare. Ya kama hannuna da hannunshi masu ɗumi ya riƙe. Lumshe idanuna nayi. Kun dai san mutuniyar taku ba daga nan ba, balle an jima ba'a haɗu da rijalu ba.( Ummu nabeeha ni Iyabo dake nake) Da ƙyar na buɗe idanuna na kalleshi. Shima ya shige cikin kujera yana ta aikin kallona ga ƴan biyu sai gwarancensu suke yi mana.
Yanzu dai muje kayi wanka sai kaxo kaci abinci nayi maka girki mai daÉ—i"
Kamar rakumi da akala haka ya zamemun. Ko wankan da ƙyar na rarrasheshi ya shiga kun gane ai? Hahaha
Kafin ya fito na fita tsakar gidan ina tambayar da wacce motar suka zo. Mai gadi ne yake sanarmun a motar Hajiya Asma'u ta tafi gida.
Ina komawa ciki na sameshi a kwance a gado daga shi sai tawul a jikinshi.
"Ina jakar kayan nawa ko ba ita kika je É—akkowa ba.?
A hankali yake magana kamar bacci yake ji, ko kuma wanda ake yima susa a takashi. ko kuma ya kwaso gajiya ne ƙila daga wajen aiki, tunda jiya ma a asibiti ya kwana.
Hajiya Asma'u ta tafi da motar da kayan ke ciki. Ƙila ta manta ne. Kazo muje kaci abincin ko?"
"Ta tafi mun da kaya fa?".
Ya faɗa da mamaki. Ni kawar da zancan nayi ta hanyar taimaka mishi yasa kayanshi, bayan na bashi kulaccam ɗina ta musamman ya shafe jikinshi dashi, yanata santin ƙamshin. Muka wuce daining na zuba mishi abincinshi nima na zuba nawa.
"Ya baƙunta dai. Da fatan Family na sun karɓeki hannu bibbiyu ko?"
Sai da na haÉ—iye abincin bakina kana nace.
Sun karɓeni fiye da tunani na ma. Gaskiya akwaisu da karamci"
Murmushi yayi yana kallona.
"Kinga Asma'u yau ko? Ita Suhaila ai kun haÉ—u a sha'anin biki ko?"
A_a za dai mu haÉ—u gobe in sha Allah?"
Cokali ya ajjiye yana tauna abinci yana kallona so yake ya gama tauna abincin nasan ya jefo mun tambaya.
Ai kuwa ilay
"Bata zo buÉ—ar kai bane ko Yaya. Kina nufin bata zo gidannan ba.?"
Gaskiya ko tazo bamu haÉ—u ba. Babu mamaki abubbuwane sukai mata yawa"
Dariya kawai yayi tare da kurɓan zoɓo ya girgiza kai kawai.
"Wacce ƙasa kika taɓa fita shine ko labari baki bani ba har sai da kuka je ofishin yin paspo tukunna. Ko umara kika je ne uhm?"
Ya tambaya yana dariyar zolaya.
Cikinane ya karta mun, sai da na ɗan riƙeshi kaɗan kafin nace.
Umara na taɓa yi. Na mance ne ban sanar maka ba."
"Okay to naji kince gobe Suhaila zata ganki. Ba yau kike son tarewa da angon naki bane, ko baki shirya bane?"
Ya kafeni da idanu take na ƙware. Saida na daɗe ina tari kafin ya faɗa mun.
"Sannu kiyi a hankali"
Sai da na dawo cikin hayyacina kana nace.
"Sai su Alhaji Baba sun dawo gobe tukunna zamu tafi"
Dariya yayi harda tafi.
"Au so kike yau in kwana a gidannan kenan ko mu yi abun kunya?"
Da dariyata nace.
"Akan me ga matarka can tana jiranka."
Hararar soyayya yayi mun.
A haka dai mu ka ci abincinmu muna hira har akai sallar magriba.
"To zanje masallaci daga can zan wuce can gida in dubo Antynki da yara. Zan dawo mu kwana anan É—in tunda dai haka kike so muyi abun kunya"
Kafin ma in yi magana ya fice.
Da sauri na shiga É—aki na tura mishi text akan ya zauna tare dasu, nima zanyi zamana anan har zuwa ranar da zamu juya tunda yace kwana uku zaiyi ni na barma Hajiya Suhailat kwanan.
Ina turawa na datse wayata na ta da kabbarar Sallah.
Chapter 221 · 0% Book details