← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 206 OF 237

Sashe 206

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

IYABO:.
Murmushi nayi ma Batula. Na tsame hannuna a cikin fulawar dana kwaba kusan mutu ashirin ta É—anwake, hannuna na wanke na nemi gefen tabarmar da take zaune na zauna.
To zubo mun tuwon Batula inci maza in koma bakin aikina.
Tuwon shinkafa miyar ɗanyar kuɓewa da tsokar kayan ciki da ganda ta zuba mun harda yajin daddawa da man Shanu cokali guda. Ga kuma ruwan kokko kofin roba guda.
A cikin gidan akwai masu saida abinci iri daban daban abincinmu na arewa, kuma ko wacce tana da ma,aikata da yawa. Gidan shi yasa kullum a jaƙale kotako ina ruwa, da tulin wanke_wanke. Yawanci wanke_wanken kayan, maza ake ba su wanke tas suma aikinsu kenan biyan wata akeyi musu.
To gidan akwai mata sosai dan ko wanne É—aki cike yake da mata, abun mamaki harda gwauraye masu haya a gidan É—akin samari cike da gardawa.
Ƴan mata da zawarawan gidan masu ido da kwalli ko wacce tana zaune da abinda take ci a matsayin abun karyawanta.
Wasu ragowar kaza, balangu, tsiren jiya shi suke ci. Wata kuma taliyar ƴan yara da faidayin wainar ƙoyi. Wata dankalin turawa da tea haɗin murtuk. Wata biredi da bota da wainar ƙoyi. Wata masa da farfesun kan rago. Gasunan dai a jere wacce bata da yadda zata yine take cin duk abinda uwar ɗakinta ta basu amatsayin na karyawa.
Batula ma ƙosai da tea da biredi take ci.
Ina kan cin tuwona ina danne maiƙon da kokko Zainura ta shigo gidan hannunta riƙe da ledar shopping haka.
"Kaga manyan mata sai yanzu kika ga damar shigowa kin dena shakkar Hajja Mama ko?"
Cewar Batula. Hauwa dake toya masa sai tace.
"Ai da saninta ne shi yasa ta sakankance. Hajja Mama ce ta haɗata da Alhajin. Ni dai a miƙon kasona ina daga nan"
Zama Zainura tayi a gefena tace.
"Uwar biyu kina fa jina da waÉ—annan matan."
Murmushi kawai nayi mata naci gaba da cin tuwona. Nan Zainura ta raba mana kaza gashasshiya da wani lemun kwali mai shegen daɗin gasken gaske. Ta bamu cake wasu ƙanana, hardama biredi mai kwakwa.
Ni dai adana nawa nayi dan na riga dana ƙoshi da tuwonnan na bari da rana maci ni da yara.
Fitowa mu ka yi ni da Batula zuwa mami market kasuwar matan sojoji dake gefen barikin dake tsallaken unguwar da muke.
"Batula niko mai sunan unguwarnan, naga duk inda muka ratsa hausa nake ji anayi kamar ba kudu ba. Duk da dai akwai ƙabilu amman naga hausawa kamar ma sunfi yawa"
Kafin ta bani amsa wani Alhaji ya sha gabanmu da mota. Har Batula ta juya zata sauke mishi tijara sai kuma ta sau dariya.
"Yaron waye kyawawa kuka kwaso kuke tafe kuna surutu?" Cewar wannan mutumi yana daga mota ya leƙo da kanshi ta tagarmotar. Batula tace.
"Alhaji Ghali kenan. Ga uwar yarannan ka ganta. Ƙawatace sunanta Iyabo bata daɗe da zuwa ba"
Sai naga yana bina da idanunshi yana ƙarame zatina kallo.
"Wannan irin hannun Dr ce wallahi. Batula abinda za'ayi shine ta bani lambarta zan bama abokina zata ji kira. Kakarta ta yanke saƙa" Batula tayi shewa tace.
"Shi Drn yazo da ƙafarshi ya ganta su sasanta. Bawai kai zaka gane mishi itaba" Dariya yayi kawai yace.
"Mata iyayen jan aji. To naji in Allah ya shigo dashi zamu tawo ƙafa da ƙafa. Amman alƙawari kar a kuskura ace wani ya rigamu. Dan Dr bazai iya haɗa nema da kowa ba."
Kuɗi ya ƙirgo ya miƙo ma Batula tasa hannu ta amshe muka tsallaka. Ni dai bance uffan ba mamaki ya isheni da ganin sarkin fawa sai miya tayi zaƙi?
"Dafe kuɗinki Iyabo dan nasan danke ya bayar. In kika bani wani abundai zan karɓa"
Ki raba biyu ki bani rabi, tare ya bamu ta dalilinki dan ni ba saninshi nayi ba." Ƙirgawa tayi ta cire nata ta bani nawa. Ta ɗaura da cewa.
"Yana da kyau ki sai waya sabida irin wannan rana. Dan nasan baki da wayane na kawar ma da Alhaji Ghali tunani fa. Waya na da amfani. Ko ta dubu ukuce ki samu ki siya ki maƙala sim zawarawanki sa dinga huce miki takaicin ƴan uwansu maza ko me kikace?"
Hakane Batula zan siya zuwa ƙarshen wata in Hajja Mama ta bani kuɗin aikina in sha Allah.
Haka dai muka shiga wannan kasuwa muka siyo barkono da mai muka dawo gida.
Mun dawo mun tadda su Hauwa sun tafi shago. Mu kuma Gaga_gaga muka kama aiki ka'in da na'in.
Ina matuƙar jin daɗin zamana a wannan gidan. Musamman in aka zauna ana hirar dare ana shewa wata rana sai a raba dare ba'ai bacci ba ana ɓarin zance. Wata rana darenma ko wacce ta kama gabanta.
Haka rayuwata taci gaba da tafiya a wannan gida. Anayin ƙarshen wata Hajja Mama ta bamu kuɗin aikinmu. Dama jira nake yi in karɓi kuɗin in sai sutura ko kala biyu ne. Karfa ku mance kaya kala ɗaya nazo dashi, sai goduwar baƙar rigar kanti da Hauwa ta bani shine kayana suka zama biyu. In ɗaya na jkina ɗaya na shanya. Na gagganɗa da kuɗin dana tawo dashi da yamma Batula ta ɗaukeni muka shiga kasuwar Sms kasuwar suturu kenan. Atampa guda biyu na siya da mayafi.
"Iyabo ki sai sim anan in munje gida ina da ƙaramar waya sai in siyar miki dubu ɗaya ma zaki kawo tunda dai kece. Kinga mutane da yawa suna tareni suna buƙatar lambarki, amman sai dai ince musu baki da waya. Shin wai ke ko bakya son yin samari da zawarawane. Ki samu kuɗi ki fantama yadda Allah ya yiki da zatinnan ai wallahi ke kalar matar alhazawace"
Dariya nayi mata nace.
Ni da nake shayarwa Batula ina ni ina yin wani zawari dan Allah?"
Dariya muka yi dukka. Da naci dai Batula tasa na sai sim ɗinnan muna dawowa gida ta bani ƙaramar wayarta aka saka sim na miƙa mata kuɗinta.
Washegari ta rakani maƙota na kai ɗinkin kayana. A hanyarmu ta komawane muka ci karo da wannan Alhaji Ghali in baku mance dashi ba, ya sake tsayar damu. Yau ba'a mota yake ba a tsaye suke shida wani dattijo suna magana yaci malum_malum yanata ƙamshi"
"Batula ke da matar tamu ce daga ina kuke?"
Dariya Batula tayi tace.
"Matarku fa? Ku dai tsaya kallon ruwa kwaɗo yayi muku ƙafa. Da kai tunaninka sai taƙi kula zawarawa sabida kace kayi ma abokinka kamu? In ma zai bayyana kanshi ya bayyana kanshi"
Shima dariyar yayi yace.
"Mufa da gaske muke yi. Yau ɗinnan ma dana je shagon Hajja Mama cin tuwo na mata maganar ai Dr mutuminta ne. Bai shigo bane amman yadai ce babu matsala zuwa ƙarshen wata zai shigo. Matsawar ya shigo zan kawoshi suga junansu. Ko me kikace Iyabo?" Ya jefo mun tambaya.
Hakane ai babu komai Allah ya kaimu lokacin da rai da kafiyarmu"
"To to ameen nagode. Ga wannan a siyama Æ´an biyu alawa"
Ya miƙo mun dubu uku nasa hannu na karɓa ina godiya. Mu kai sallama muka shige gida.
Gaga_gaga rayuwar taci gaba da gudu dai.
Wata ranar lahadi Hajja Mama na gida bata je shago ba sunayin tuhu ranar lahadi sabida jiki da jini. Sai naji ta kirani muna tsakiya da sallamar masu zuwa sayen É—anwake.
"Iyabo kin taɓa magana da Dr ne abokin Alhaji Ghali?"
Da sauri na É—ago nace.
A_a wallahi ban taɓa magana dashi ba. Ni bamma sanshi ba"
Sai tayi dariya da taga na ruÉ—e tace.
"Bawai lefi bane Iyabo ki kwantar da hankalinki. Ai ni ban isa na hanaki kula zawarawa ba. Da dama ni na aurar dasu a gidannan. Da dama yawon bin mazansu suke yi domin samun na rufa ma kai asiri. In kin kula babu ruwana da hana kowa abinda yake so. Ni dai in lokacin aikine ayimun aiki.
Sabida haka Dr ya kirani da kanshi yake sanarmun zai shigo yau kuma takanas wajenki zai zo. Zai sauka a zangon baƙi. Dan haka sai ki shirya in ya iso zai kirani sai ki je ki kai mishi abinci ku yi taɗinku acan."
Sai naji gabana ya faɗi jikina yayi sanyi ƙalau har ita hajiyan saida ta fahimta"
Tofa tashin hankali wanda ba'a sa mishi rana"
MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI ce.
NAMA YA DAHU....
ROMO ƊAÑYE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
LITTAFI NA HUDU
(6)

IYABO:.
Chapter 206 · 0% Book details