← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 237

Sashe 125

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daɗi ganin dilolinnan sai ya sharemun ƙuncin da su Iyaa suka dasamun a raina. Ɗakin uwani muka koma, ɗaki masha Allah har kayan kallo Uwani ta saka ga firjinta ƙatoto. Kinyi gyara gaskiya Uwani. Kuma gidan yayi kyau babu laifi" "Wallahi kinga ga wani gida na jikin nawannan daga hannun hagu, shima da shago babbane dan yafi nawannan girma. Ni dai da zaki siya ko haya sai ki zuba Iyabo, ki ɗan dinga karɓar kuɗinki, kuma ko babu komai kin ajjiye kadara. Gidan a hannun dillalin dana siya wannan gidan ta hanyarshi yake. Yana ta mun tayi gidanma akan in siya in haɗe da nawa. Ni dai ki siya Iyabo. Ina da kuɗin siya amman ke naima sha'awar gidan " To Uwani naji shawararki zan siya babu matsala, dan dama shanu naso in siya ayimun kiwo. Ammam bazai gagaraba zan sai gidan" Uwani bata ƙyaleni ba har saida ta kaini ofishin dillalinta muka tsayar da magana harda rabin kuɗi na ajjiye mishi mun tsaya akan gobe inzo da shaiduna insa hannu a takadda a mayar da sunan gida nawa a bani takadduna, in cika kuɗi a bani ɗan makulli. Hakan kuwa akayi Burodami Kokodeen da Lekan sai Uwani su su kaimun shaida akayi aka gama komai aka bani takaddun gidana da ɗan makulli. Ɗakuna shida ne falle falle, sai ban ɗaki da kitchen, da shago a waje kamar dai gidan Uwani. Daga haka muka shiga sha'anin gyaran jiki, magungunan mata daga wajen Anty Ramlex, shiga kasuwa, kai dinki. Kafin dai sati guda duk abinda zan siya na siya na jibge a gida har dilolin kayana nasa mota ta ɗaukarmun ta kaimun gida. Na buɗe jakar tsaraba naba duk wanda ya dace. Ranar laraba sai ga mutanen Banyo da yamma sakaliya mota ɗaya duk mata, sai direba namiji. Sun samu tarba ta girmamawa sosai dan ni banyi tunanin hakanba ma. Sun tawo harda akwatinsu mai taya guda biyu. Kayan ciki babu yabo babu fallasa ga bazawara kamata dai. Wasu a ɗakin Iyaa Debisi suka kwana, wasu kuma a ɗakin Iyaa Kokodeen suka kwana. Ni da Uwani muka kwanta a ɗakin su Lekan. Washe gari sassafe muka ɗauki hanya. Motar da suka tawo da'ita ɗaukar Amarya muka shiga mu biyar. Ni da Uwani, sai Anty Ramata, da Iyaa Kokodeen. A gaban mota kuma Burodami Kokodeen ne sai direba. Motar kaya kuma aka lode kayayyakina hardasu dilar kayana aka rufe da tampol dan hadarine baƙi ƙirin a garin motar kayan ta daɗe da kama hanya ita kafin mu. Muka kama hanyar Adamawa. Tun kafin mu fita daga cikin garin Kano aka soma yayyafi sama_sama. Da muka soma shaga ƙauyuka ruwan yanata ƙaruwa, duk ƙauyan da aka wuce ruwa akeyi sosai. Sai tafiyar ta zama me daɗi babu zafin rana sam sai sanyi dake ratsawo ta ƙasan motar. Su Iyaa Kokodeen tuni sukai baccinsu sai gwara kai suke yi. Idanu na lumshe inata tunani, tare da adda'ar Allah yasa kada Yaya Hamma ya bani kunya ya tozarta zumuncinmu. Yanzu Shikenan rayuwata ta koma ƙauye nima zan zama baƙauya kenan? Wasu siraran hawayene suka gangaro a kumatuna wanda ni kaina bansan na meye ba. Haka mukaita gudu har muka isa Adamawa ruwa akeyi sai tsurarun ƙauyuka da basu wuce uku ba da muka wucesu ba'a ruwa. A Girai motocinnan suka tsaya gashi ruwa akeyi sosai. Haka dole muka fita daga cikin motar muka fake a ƙasan wata bishiya mai yalwar ganye. Maza da mata duk muna fake mota ake jira. Munfi awa guda ana zabga ruwa daga bisani ruwan ya tsagaita mota ta tawo duk ta kwashemu. Kowa a takure yake sanyi ga jikewa da mukayi amman ba sosai ba. Hanyar tafi ta kullum muni, ko ina ruwa camɓal a kwance, ga laka sai riƙe motar take yi a haka dai har muka iso masauki. Daga nan muka tari mashina suka shigar damu. Gidan Dada kai tsaye nace su wuce dani dan ina buƙatar in sake kayan jikina, ba a kai amarya a jike sharab ba. Dada da Yusufu ne kaɗai a gidan tana ganin su Iyaa Kokodeen ta soma murna tana musu yare. "Daso ciwo kikayi haka naga duk kin ƙare sai wuya?" Dada ta dubi Iyaa Kokodeen tace. "Zauna tukunna manyan baƙi nayi farin ciki da ganinki. Yau gaku a garinmu." Zazzaunawa sukayi Jikkunansu duk a mace. Sai jimantamun suke yi. "Ni ina mamakin abinda Iyabo ta gani da har ta amince da rayuwar ƙungurmin ƙauyen nan. Rayuwar ƙauye a wajen ɗan birni takota ina cutarwace. Jibi nisa da wuyar da muka shawo. Ohh ke kuma haka kikeson kaddararki ta kasance" Cewar Iyaa Beji kenan. Iyaa Kokodeen ita kam hawaye take ta sharewa. Take nima na fashe da nawa kukan sai shessheƙa nake yi. Ni wannan maganganun duk sun isheni. Ni ba yarinya ƙarama ba, kuma ni nace naji na gani ba sai su sa albarka su bini da ido ba? Haka aurena da Gwadabe akaita koke_koke da tashin hankula iri daban_daban gashi a aure na biyu dana auri jinina bata sauya zani ba. Ko babu komai ni inaso in zauna a kusa da kannena da mahaifiyata. Tunda da tun farko an barni a hannunta da a wannan ƙauyen zan rayu, kamar yadda itama ta rayu." Kaya na sauya, akwatin kayan sawata dama yana tare damu. Ruwa daya tsagaita Yusufu yai mana jagora bayan mun rama sallolin da ake binmu har magriba munyi, an kawo mana jallof ɗin shinkafa da Dada tasa aka dafa domin tarar baƙi. Yafendona Dada ta aika aka kira duk suka haɗu aka rankaya kai Amarya da ƙafa. A kacame gidan yake sosai anata kacaniyar biki. Tsakar gidannan ta damalmale da ruwa da abinci da yara suka zubar. Rumfunan gidan cike da mata da yara anata haya_haya. Ɗakin Yafendo Kaɓoji aka wuce dani kai tsaye. Anan muka tarar da su Yafendo A'i da yaransu mata dake gidan aure. "Lale lale. Amaryarmu tazo gida. Sannunku mutanen Kano" Waje aka basu na zama aka taresu da lafiyayyen tuwo miyar ta wadatu da naman saniya da man shanu. Yafendo A'i tace. "Ga abinci kuci, ayi sallah sai a shiga da Amarya ɗakunan matan gidan kafin a shiga da'ita ɗakinta. An gama jera mata komai. Tun ɗazu mata suke zuwa kallon ɗakin Amarya tubarkalla masha Allah" Ɗan dariya Iyaa Kokodeen tayi a matsayin amsa kawai. A nan mu kai Sallah, Baɗɗo ta shigo ta sameni. "Adda ragowar wasu muhimman kayanki duk suna ɗakina gudun kar a ɓarnatar miki. Akwai ƙunshi wasu buhunhuna duk na shiga dasu ɗakina" Yauwa Baɗɗo su waɗannan buhunhunan ki barsu a ɗakinki zuwa gobe zamu ware kayan amfanina ragowar gidan Dada za'a Kai mun." Raɗa naima uwani a kunnenta, ta miƙe suka fita ita da Baɗɗo. Yafendona tace. "Iyayen Jabu ku taso mu kai amarya ɗakunan matan da tazo ta tarar a gidan bisa ga al'ada kafin a kaita ɗakinta" Gaba suka tusani Yafendona da Iyaa Kokodeen. Ragowar kuma aka nuna musu ɗakina suka kama hanya. Da ɗakin Hama muka soma, ɗakin ma cike yake da ƙawaye babu masaka tsinke. Duk sun tarune domin suna son ganina, ance musu daga Saudiyya na dawo. Sai da wasu dole suka fita kafin mu muka samu waje. Yafendona ta nuna mun gefen gadon Hama tace. "Jabu ga bakin gado zauna muyi a gurguje ki samu ki shiga ɗakinki sanyin yayi yawa" Ɗofanuwa nayi a bakin gadon, fuskata ba'a rufe take ruf ba ina iya ganin kowa da komai, duk wanda ya kalleni zai iya ganin fuskanta. Hama fuskarta ta kumbura tayi jawur da halama taci kuka ta gode Allah. Dan ina zama ta bani baya sai jijjiga ƙafarta take yi. Ga Daso a gefenta sauran manyan ƙawayen nata suna tsakiyar gadon sai ƙaremun kallo suke yi. Ni ko ina lure tsab da motsin kowa. "Hama ga ƙanwarki mun kawo miki. Duk da dai zata iya girme miki amman dole kece sama da'ita tunda ke ta shigo ta samu. To Jabu dai ba baƙuwa bace ku daure ku haɗe kawunanku domin a zauna lafiya. Jabu dai ƴar uwa take ga Hamma da mahaifiyarta da mahaifiyar shi uwa ɗaya suke uba ɗaya kin sani. To ayi haƙuri a martaba wannan halaƙar" Hama dai taƙi buɗe bakinta tayi magana har saida Daso ta zungureta kana tace. "Allah ya bada zaman lafiya ya sanya alkairi " Yafendona tace. "Ameen to Jabu muje a kaiki ragowar ɗakunan" Haka mukaita shiga ɗakunan matan ƙannen Hamma daga ƙarshe suka wuce dani bukkata dake wata ƴar kwana can ƙarshen gidan sai an shiga lungu. Tun daga ƙofar lungun akayi blue ɗin fenti har cikin bukkarnan data kasance ɗakina. Da bismillah na shiga ina karanto adda'a duk wacce tazo bakina. A takure bukkar take sosai kasancewar kayana da yawa sai ya zamana babu ko wajen da zan iya sallama. A kujera aka zaunar dani. Uwani da Baɗɗo sai gyare_gyare suke yi mini. Anti Ramata tace. "Allah me iko. Yau wannan shine ɗakin auren Iyabo" Sabida rashin waje ishasshe basu jima ba duk suka fice, ɗaki ya rage daga ni sai su Uwani. "Iyabo kujerunnan dole ki rabu da wasu gaskiya. Ni ina ganin waccan 2 sitter ɗin kawai za'a bari in kinaso ki samu fili. Sannan kayayyakin kitchen ɗinki fa duk mun lode miki a sib ɓangare ɗaya baki da kitchen, da kitchen da banɗaki duk na gandune, kinga ai ba zamu yi miki jere a kitchen ɗin gandu ba. To Uwani duk yadda ya dace ayi kawai" Nace da'ita ina takure a kujera" "To yanzu dare yayi zuwa gobe da safe duk saimu gyara komai ni da Baɗɗo. Kun haɗu da angon naki kuwa Iyabo?" Idanu na lumshe nace. A'a bamu haɗu ba, ƙila ma sai gobe dare yayi, gida kuma haɗe da iyaye" Mayafina na cire na koma kan gadona da yasha lafiyayyen zanin gado mai laushi. Fentin ɗakin nabi da idanu, bai biyu ba yayi wani roɗi_roɗi. Na ɗaga kaina azara tana kallona ina kallonta. Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Uwani nace. Uwani wannan azarar babu yadda za'ayi a rufeta?" Dariya ce ta kama Uwani sai da tayi mai isarta sannan tace. "Zamu rufeta zuwa gobe ko da zanin gadone, dan dama nace zan shiga gari in siyo cottin a zagaye miki ɗakin dashi zaifi fasali fiye da wannan fentin ƴan ƙauyen a hakanma naga ke kaɗaice
Chapter 125 · 0% Book details