Sashe 33
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba zaka manta da gudunmawar dana ba rayuwarka ba....." Tashi nayi ina shirin shigewa uwar ɗaki domin soma shirya kayana. Gwadabe kuwa duk illahirin jikinshi rawa kawai yake yi mun. Cikin kaurin murya irin ta cikar mazantaka yace. "Iyabo..." A maimakon in tsaya sai na shige ciki da gudu na saka sakata. A jikin ƙofar na jinjina ina jawo numfashi daga cikin huhuna da ƙyar. Iyabo ki buɗe ƙofarnan dan Allah na roƙe ki kar ki sa zuchiyata ta buga." Ya faɗa hakan a mugun raunace, tsabar ɓarin da jikina yake yi ma na kasa ko da motsawa, jin za'a shiga Masallacine yasa ya fita dole, ina jiyo rufo mana ƙofar falo da yayi. Sai da na haɗa ƴan tsunmokaraina a ƙaramin akwati, na ajjiye gyalena a saman akwatin kafin na tada kabbarar sallah. A lokacin ƴan biyu sun tashi daga bacci. Ina idarwa saina gyara zama na soma azkar, ina yi ina kallon yarana. Toye yana tsakankanin ƴan biyu yana wasa dasu. Sai dariyarsu suke yi. Yara kenan su basu da matsalar komai. Iyaka su yi bacci su tashi su ci abinci. Ku sakko ku je ku yi alwala ku yi salla, na faɗa musu da yaren yarbanci. Dukkansu sai da suka rungumeni kafin na buɗe musu ƙofa suka fita. Ai sai na kife a dadduma na shiga rera wani irin kuka na tashin hankali. Inayin kukan nan ban mance da ambaton Allah ba. Jin hucin mutum nayi a gefe na, Gwadabe ne nasan babu makawa. Riƙo hannuna yayi gam, ya rarrasheni ya kasa, yayi magana wallahi ya kasa. Duk dauriya da irin shanye abu na Gwadabe yau zuchiyarshi a tsinke take. Shima hawayen yake fitarwa a gidanunshi. Mun fi minti goma a haka, yara dai ban sake jiyo ɗuriyarsu ba ma. Sai can Gwadabe yayi ajjiyar zuchiya kana yace. "Iyabo yanzu me kike so in yi, ina alƙawarin da muka ɗaukarma kawunanmu zai kwana, babu rabuwa a tsarin da muka tsaroma rayuwar gidan aurenmu...." Dakata Gwadabe, kar so ya rufe maka idanu, ka kai rayuwarka ga halaka. Wallahi zaman mu babu alkhairi, kuma ba zamu taɓa ganin haske ba. Tunda Babala ko da yaushe a cikin zubar da hawaye take. Ta yiwu bijerema iyayenmu da mu ka yi ne ya jefa mu a cikin halin da muka shisshiga a baya. Siraɗi nawa muka tsallake Gwadabe? Ka tsayar da zuchiyarka kul sona ya ruɗeka, uwa tafi gaban a tsaya ana jayayya da'ita wallahi. Dukkanmu ba zamu so yaranmu su yi mana taurin kan da mu ka yi ma namu iyayen ba, Gwadabe mun zuba taurin kai sosai da sosai. Allah ya jarabcemu da talauci sosai da sosai sakamakon fishin iyaye da muke ciki. Ka daure ka sake ni kawai in tafi" Cikin dashasshiyar murya yace. "Ko dai har yanzu da ragowar soyayyar Debisi a zuchiyarki ne Iyabo? Ni fa bazan iya rayuwa babu ke ba. Da maraici kike so yaranmu su taso ne?" Cikin jin haushi, gami da tausayinshi a haɗe na dubeshi. Nayi mishi uziri dan tabbas a cikin tsaka mai wuyar fita yake, dole nice dai zan lallaɓashi ya sauwaƙe mun. Billa babu ko sofanen son Debisi a zuchiyata. Mutumin daya gujeni sabida halittar ƙibar da Allah ya hore mun, to shin me zan yi dashi a cikin rayuwata. Ka sake ni kawai, domin cika umarnin Babala da cika alkawarin da nayi mata. Ce mata nayi a ranar daka samu lafiya ko kwana da igiyoyin aurenka bana kumawa" Mun fi awa guda muna tataɓurza tsakanina da Gwadabe. Muna cikin haka, Allah da ikonshi muka jiyo sallamar Babala a cikin falo, tana tambayar Toye ko muna ciki ne" Jijjunanmu a mace muka fita falon, ita da Baban Nazifi ne, sai Yaya Harisu. Gurfana nayi a gabansu cikin rawar baki na gaishesu, babu wanda yayi yinƙurin amsawa. "Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya. Gwadabe yau zan yi bacci harda munshari sabida wannan jikar oduduwan zata bar gidannan, igiyoyin aurenka zasu sauka a kanta. Kuma bari kaji danginta ne su kai ma Agumu ( sammu) ba kowa ba, domin ba ƙaunarka suke yi ba. Wajen malamai har biyar muka je, duk maganar ɗaya ce dai. Maza saketa ta kama gabanta yanzu_yanzu. Ko wallahi in tsine maka" Idanuna na runtse bakina, harshena suna kakkarwa kunnena na baza ina jiran kalmar saki. Kamar saukar aradu naji ya furta. "Na sake ta saki ɗaya Babala" Wani wuji_wuji naji yana dibata, take mashashshara ta saukar mun. Ajjiyar zuchiya Babala ta sauke kana tace. "Cikace mata ya zama uku ɗan albarka" Na sake ta saki biyu, in aka haɗa dana baya dana yi uku kenan." Ya faɗa muryarshi a mugun dashe kamar wanda aka shaƙe. Miƙewa nayi tsam, duk da jirin da nake gani, amman bazan iya jure shaaƙar numfashin Gwadabe ba. Uwar ɗaki na shiga, Toye da ƴan biyu suna katifa suna wasansu. Ganina yasa Toye cewa.. "Mama kinga Kahinde yana dukan Taiwo ko, bayan itace yayarshi" Sai da na zari jakata kana nace. Kahinde ka dena dukanta, yayarka ce. Kai kuma Toye ka kula sosai da maraicin ƙannenka. Zan yi wata ƴar tafiyar da bansan yaushe zan dawo ba" Duk da yaron yana da ƙarancin shekaru amman sai naga yayi jigum kamar mai tunani. Kayukansu na shafa tare da saka musu albarka, na fito daga ɗakin a sanyaye, har na kai bakin ƙofar fita na jiyo muryar Babala tana cewa. "Yaran wa kika barma, wa kike tunanin zai riƙe yaran yarbawannan? Maza koma ki kwasosu..." "A'a Babala yara kam zan rayu dasu, ni yafi dacewa in kula dasu tunda dana aurota iyayenta ita gayanta suka bani, kiyi haƙuri dan girman Allah " Gwadabe ya katseta da hanzari. Kai nasa nayi ficewata daga ɗakin. Matan gidan duk suna tsakar gida da yaran gidan, suna hangoni ko wacce ta sau abunda take yi kallo ya koma sama wai shawo ya ɗau giwa. Ni ko murtuke fuskata nayi sosai ta yanda ba wacce zata iya samun fuskar tambayata, nayi ficewata zazzaɓin dake jikina sai tsananta yake yi. Ko da na shiga Bus ɗin unguwarmu na kifa kaina a bayan kujerar dake gabanku ban ɗago ba har sai da muka iso. Duk wannan abun babu ko ɗigon hawayen daya sake zubo mun tunda kunnuwana suka saurari kalmar saki. Ko gidanmu ma bansan ya akayi na iso ba, ganina kawai nayi a ƙofar shagon Iyaa. " Ahh ahhh ahh Iyabo kini o ti sele? ( Me ke faruwa )" Iyaa ta faɗa cikin kwakwazo da kuzuzuta lamarin. Kafin in mata amsa sai ga Iyaa Kokodeen ta fito daga cikin gida, itama ganina ne yasa ta nufo ni. "Iyabo lafiya da sassafe haka harda jaka a hannunki?" Jin haka yasa Iyaa fitowa a kidime zaninta na suɓucewa. "Ahhh ahhh ya sake ta ba? Ai dama mu munsan zaki dawo, ba riƙe aure suke yi ba saki ko da yaushe, da laifi ba laifi saki. Kinga abunda muke guje miki tun ba'aje ko ina ba har ya faru. Da yarenki kika aura da kin samu kwanciyar hankali. Ai sai ki shigo mu ci gaba da zama kafin Allah ya ɓullo miki da wani. In ce dai babu wani ragowar igiyar da tai saura? Dan wallahi kin bar komawa wannan auren, an yi na farko, gana ƙarshe yayi." Duk wannan maganar cikin yare take yi, tana yi tana buga cinya tare da tafa hannaye. Jiyo muryar ta ne ya tilastama su Iyaa Beji fitowa da sauri. Suna fitowa ni kuma na shige cikin shagon Iyaa na ɓulle cikin gida abuna. Ina shiga ɗakin Iyaa na tarar da Yemisi a kwance a ƙaramin gadonmu a kwance da dukkan halamu itama a gida ta kwana. Zama nayi a ƙasa jiɓur. Zaman nawa ke da wuya sai ga su Iyaa sun shigo da duk matan gidan, suka tutsiyeni kan sai na faɗi silar mutuwar auren. Daga masu cewa gwara da aka rabu, sai masu cewa zasu je su ɗebo yaransu su girma a cikin yaren mahaifiyarsu. Ni dai suka sak sani a tsaka mai wuya. "Ki buɗe baki kiyi magana mana kin ma mutane shiru" Babu abunda ya haɗa ni dashi.mahaifiyarshi ce ta bashi umarnin ya sake ni. Igiyoyin auren sun ƙare duka" na faɗa a sanyaye. Da hanzari Yemisi ta tashi zaune zumbur kamar wacce aka tsikara. Idanu muka haɗa, dan na riga na gane manufarta na wannan zabura haka. Iyaa ce ta katse mun kallon Yemisi da nake yi dafe da kirjinta. "Sai da kika gama mishi jinya tas ba, iyayen nashi ba ke suka bari da ɗawainiyarshi ba? Kika kaɗar da kayan ɗakin ki tas komai ya ƙare a nemo lafiyarshi, to ga sakamako kin gani. Wanne irin bijere mana ne baki yi akan Gwadabe ba, amman shi gashi ya nuna miki yafi son uwarshi sama dake" Cewar Iyaa da take magana a tsawace. Iyaa Kokodeen ce tace. "Ahh ki barta haka ta ji da zafi gami da raɗaɗin mutuwar aure, daga baya ayi wacce za'ayi." Da ɗaya da ɗaya suka watse ɗakin ya rage daga Iyaa sai ni da Yemisi. Da ƙyar Yemisi ta amsa gaisuwata har tana hararata. Ni abunda yake damuna shine a gabana da ta kwantar da hankalinta ma ƙila wannan itace gamuwata da'ita ta ƙarshe daga ita har mijinta. Dan a wannan karon garin Kano ta yi mun zafi ainun, na fi son in je rugar mahaifiyata in zauna a cikin danginta da ƙannena nima. Ina cikin zancen zuchi sai ga sallamar Debisi ya shigo. Irin kallon daya watso mun da dukkan halamu Iyaa ta labarta mishi abinda ya faru dani. Kaina a ƙasa na gaisheshi cike da ladabi. "Lafiya lau Iyabo. Sai kuma naji mummunan labari marar daɗin sauraro?" Ɗan murmushi kawai nayi kaina a ƙasa. "To Allah yasa hakan shine a'ala gareku baki ɗaya. Allah ya fito muku da waɗanda za su yi dai dai da rayuwarku. Kar ki saka damuwa a ranki. Shi aure rai gareshi nasan kin sani" Duk wannan maganar da yayi yana tsaye a kaina yake yi. Shigowar Burodami kokodeen, da Anty Mulka, da iyaa, da iyaa Debisi, da duk masu ruwa da tsaki na gidanmu ne yasa Burodami Debisi ya nemi waje ya zauna. Alfa Kulle shine ya shigo a ƙarshe, Wa yake ga mahaifina, ƙani ga Iyaa Debisi cikinsu ɗaya. Kuma ya kasance shine mai