← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 237

Sashe 115

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

daɗi domin kuwa wasu basa ko ga miciji da wasu. Ko wanne ƴan ɗaki isu_isu da matansu suke mu'amala, gaisuwa wannan bata shiga tsakani. Shi yasa tsakaninsu Hadiza da matan su Auwala ne kawai suke mu'amalarsu a tsakaninsu, sai Yaya Tasi'u daya zame musu garkuwa. Ko wacce in zata fito bata da aiki sai waƙe da habaice_habaice. Sai gasa da hassada ta shigo cikin lamarin. Daga masu suyan kifi, sai masu suyan nama, ko kaza. Ga gasar sutura da kwalliyar safe data yamma dan tarbar miji." Ta bangaren gidan Malam kuwa rikicine ya ɓalle ƙaramar maganace take son zama babba. Iyayen matanshi daya tura gida sunyi jelen har sun haƙura. Amsa ɗaya malam yake faɗa musu itace "Su je su huta a gidajen iyayensu. Nima inaso in huta" Yaran Baba Suwaiba suka haɗe kansu suka samu Malam akan batun gyatumarsu. Suma Malam ya fatattakesu da zancan. Bayan kwana uku suka je suka dawo da Babarsu gidan. Ranar sunga tsiya. MRS BUKHARI
Chapter 115 · 0% Book details