Sashe 203
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
dariyar suketa ɓaɓɓakawa da ƙyar dariyar ta lafa aka ɗaura da gaishe_,gaishe. "Ya kujerar muƙami ya akaji da jama'a kuma?" "Gwadabe ga kujera nan lokaci ya kusan cin mana. Dama akan abinda nake son muyi magana kenan. So nake yi a zaɓe na gaba mu tsayar da kai a matsayin ɗan takararmu Gwadabe. Nasan wallahi zaka iya shi yasa da muka yi taron meeting Chairman na Takai ya bani umarnin in akwai wanda nake ganin ya cancanta to in kawoshi ni da kaina. Ni kuma duk hange_hangena a cikin abokanmu kai kaɗai na hango sabida kaine kake da takaddar shaidar sakandare. Amincewarka nake nema sai kuma in ɗaukeka in kaika wajen Chairman ku gana. A ɗaukeka a tsomaka a party" Tunda Zulƙi ya soma magana zufa ta soma karyoma Gwadabe. Bara'u kuwa sai washe baki na farin ciki yake yi. Wata ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke kana yace. "Bazan iya siyasa ba balle har in riƙe wani muƙami ba Zulƙi. A nemi wani a saka ni sana'ata ta fiye mun komai. Ina tsoron danne hakkin al'ummar data rataya bisa wuyana. Gidana ma ban gama bi dasu ba wallahi. Mata in suka haɗa maka tenshon sai kaji kamar kayi musu ƙaura, ina ga jagorancin al'umma?" Da Bara'u da Zulƙi suka haɗe bakunansu wajen cewa. "Zaka iya kujerar dakai tafi dacewa" Dariya suka yi duka. Zulƙi yace. "Gwadabe kar ka buɗamun ƙasa a idanuna mana. Ka daure mufa amincewarka kawai muke buƙata, ba'a buƙatar ko sisinka yardarka kawai ake nema. Kuma ka sani ai zaɓe za'ayi matawar jama'ar gundumarka suka zaɓeka to tabbas ka cancanta. Gidanku babban gidane kuma sananne, nima naci zaɓe balle kai Gwadabe. Ni da Alkhairi na soka Bara'u ya bani labarin duk halin da kake ciki da danginka da Babala. Har asibiti ma naje na dubata." Zulƙi da Bara'u sukaita ba Gwadabe baki, shi kuma yana nuna musu girman jagorancin al'umma. "To naji na amince Allah yasa hanyar arzikin kenan. Amman zan zauna da matana muyi shawara ko ba gaskiya bane?" Zulƙi yace. "Wannan gaskiya ne. Amman shawarar karya wuce yau. Tunda dai gaka a Takai sai muyi komai mu gama mu san mun samu cansila mai jiran kujera" Dariya su ka yi dukansu. "To Alhamdulillah Zulƙi kayi zumunci. Gwadabe ka kyauta daka amshi wannan tayin. Kuma ayi istikara Allah yasa albarka a cikin lamarin. Muyi ta adda'a, mu kuma zamu shiga mu fita da izinin zaka samu wannan kujerar." Murmushi Gwadabe yayi kawai. Wayarshi ce tayi ruri. Ya ciro a aljihunshi ya kara a kunnenshi. "Alhaji barka da safiya, kaine da waya sassafe haka?" Alhajin yace. "Dole in kiraka. Na jima ina neman maganin lalurata ban samu ba. Amman cikin yardar Ubangiji sha biyu nayi ma maganinka na samu waraka. Sabida wannan na biya maka umara da kai da matarka in sha Allah. Wannan shine tukuicina na jin daɗin maganinnan." Kabbara Gwadabe yayi harda miƙewa tsaye dan murna. Nan ya dinga ragargazo mishi godiya. Da haka su kai sallama ya ajjiye wayar. "Ku taya ni murna wannan babban mai muƙamine na bashi magani ya samu waraka shine ya biya mana kujerar umara" "Allahu Akbar. Allah da girma yake haƙiƙa na taya ka murnar wannan tukuicin Gwadabe. Allah yasa shekarar arzikinka da ɗaukakarkace ya tsaya. Masha Allah" Cewar Bara'u. Zulƙi ma ya taya shi murna. Nan suka shiga cin masa da miya anaci gaba da hirar duniya da irin yadda zumunci ya taɓarɓare a wannan zamanin da ake ciki. Basu suka fito daga gidan Zulƙi ba sai wajajen goman safiya. Suna tafe sai Gwadabe yace da Bara'u. "Bara'u bayan na gama murnar kyautar da wannan bawan Allah yayi mini. Sai zuchiyata ta shiga canki_cankar shin dawa zamu tafi umararnan Shafa ko Hadiza" Tsayawa Bara'u yayi cak ya zuba ma Gwadabe idanu" Ƙaƙa_sara_ƙaƙa. Ku a tunaninku wacece tafi cancanta a tafi da'ita a babin adalci? A kafta. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI