← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 237

Sashe 34

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

ƙarfin faɗe aji a family kasancewar shi kaɗai ne namiji da yai ragowa. Gidanshi yana jikin namu gidan. Amman iyalinshi suna Ibadan da zama, sai dai duk shekara yana kai musu ziyara. Burodami kokodeen ne ya buɗe taron da adda'a kafin Alfa Kulle ya tambayeni cikin yaren yarbanci. "Meye silar rabuwarki da mai gidanki?" Murya na rawa na labarta mishi a taƙaice, sai Iyaa tayi carab tace. "Dama tun auren a difane fa take a gidan auren. Dangin miji kullum cikin ƙyamatarta suke suna aibanta mata yarenmu. Buradomi Kulle meye kai baka zaunar da yarinyar nan ka faɗa mata ba, ba ƙafa tasa tashure ba, sabida ganin ba mu muka tsugunna muka haifeta ba, ƙasa ta rufe ma Toye idanu. Cikinmu nan babu mai son wannan auren " Alfa Kulle yace. "Ta faru ai ta ƙare. Ba shikenan ba auren ya ƙare kan kat ba. Sai. Ki zauna zuwa lokacin da Allah zai ɓullo miki da wani mijin. Inason in koma Rugar mahaifiyata can inda kowanta yake. Dan Allah kar ku hanani wallahi bazan iya zaman Kano ba" Ina jiyo ajjiyar zuchiya da Yemisi ta sauke mai ƙarfi. Iyaa kuma ta dire akan ban fa isa in bar hannunta ba. Sai da kowa dake wajen ya sa baki kafin ta amince sai zubar da hawaye take yi. Burodami Debisi kuwa ya kasa cewa komai. Zahiri bai ji daɗin amince mun da kowa yayi akan komawata ruga ba. "Zuwa yaushe kike son tafiya Iyabo?" Burodami kokodeen ya tambaya. A sanyaye nace. Zuwa gobe in Allah ya kaimu" A haka dai taron ya watse, duk yanda Burodami Debisi yaso keɓancewa dani Matarshi ta hana shi wannan ƙofar. MRS BUKHARI
Chapter 34 · 0% Book details