Sashe 29
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ina bashi ina sake yi mishi nasihu masu ratsa jiki, akan ya gode Allah ma da ba hatsari yayi yaji raunuka masu yawa ba, da izinin Allah muddin muka dage da adda'a koma sammunne Allah zai bamu nasara, amman zuwa gobe zamu je asibiti. "Babu ko ficika a jikina Iyabo, kuma kinga asibiti sai da kuɗi Iyabo" Haba Gwadabe, zan siyar da atampopina in samu ɗan kuɗin da zamu riƙe a hannunmu, mu gode ma Allah muna da abinda zamu ɗaga mu siyar ma. Ina zuwa da zafi_zafi akan daki ƙarfe. A zabure na miƙe na shiga zaro atamopin sunan ƴan biyu, kala goma na fitar na zuba a bako. Gwadabe bari in je shagon me sai da atampopinnan ta bakin titi yarenmun nan, bazan jima ba, ga yara a falo" Ban tsaya jin abinda zaice ba na fice, sai dai kunsan mutane in suka ganka cikin matsuwa ka fitar da abu zaka siyar, sai su dinga yi maka tayin wulaƙanci. Dubu goma sha biyar ta taya atampopinnan kuma manyan atampopi harda Holland, da ƙyar muka ƙarƙare a sha bakwai da ɗari biyar. A cikin daren yau daga ni har Gwadabe kusan kwana mu kai muna Sallah muna adda'a, wallahi har akai sallar asuba bama ko jin digon bacci sai jarababben ciwon kai daya jarabeni. Ana fitowa Sallah na jiyo sallamar maza a ƙofar ɗakinmu. Baban Nazifi ne yake sanar dani dattawan unguwane suka zo duba Gwadabe. Hijabi nasa kafin nace su shigo. Gaggaisawa mu ka yi dasu, tare da yi mun jajen abinda ya faru, daga bisani kuma suka shiga ciki dubo shi. Ni dai jigum nayi a wajen na rasa me ke yi mun daɗi, a wajen suka fito suka taddani, su kai mun sallama suka fita. Ruwan wanka na juyo a bokiti na shiga da sallamata. Na samu Gwadabe yayi jigum yanata aikin tunani, na sani ban isa na hanashi tunani ba, domin jiya uwar haka da lafiyarshi ras ya fita. Gwadabe bari in ɗan goggoge maka jikinka da tawul sai ka yi asuwaki mu samu mu je asibitin ko?" Sai da ya sauke nannauyar ajjiyar zuchiya yace. "Na yi ma Yaya Hambali magana kan batun asibiti da muke son zuwa. Bai goyi bayan hakan ba, yace ciwon yafi kama da sammu, tunda babu inda yake yi mun ciwo, sai nauyi da ƙafafuna su ka yi, kuma Oga lurwanu ma yace sammu ne" Hakane Gwadabe, amman zuwa asibitin ai yana da amfani, in muka je suka auna basu ga komai ba shikenan sai a yi na gargajiyan "E haka na ce mishi nimaa. Ya dai ce Da'u zai tsaya mu tafi asibitin tare." Goggoge mishi jikinshi nayi tas, na saka shi a po ya rage mararshi, yayi asuwakin zamani, kana na bashi tea da burodi, da ƙyar yaci burodi yanka ɗaya, ni ko iyaka shayin kawai na kurɓa, mu ka jiyo sallamar Uwani. Miƙewa nayi na fita falon ina sharar hawaye, ita kanta uwanin kuka take ta faman yi. Muna cikin haka Da'u da Nazifi suka shigo, basu kula mu ba, ciki suka wuce abinsu. Ni kuma na sallami Toye ya tafi makaranta. Fitowa dashi suka yi, Da'u sai tsaki yake yi. Mu dai bayansu muka bi, ashe sun kira tasi tana tsaye a ƙofar gida. Asibitin Murtala muka wuce, ganin halin da muke ciki sai wani likita yace bari ya bamu gado ayi duk binciken daya dace a tsanake zaifi. Hakan kuwa akayi aka bamu gado a Ward ɗin maza, Da'u da Nazifi kuma jin an riƙe mu a asibiti sai suka yi tafiyarsu. Hawaye kawai nake sharewa, likita yace mu zauna daga waje. "Yanzu tsabaragen ƙiyayya yana ciwon ma ba zasu taimaka mishi ba, a lokacin da yafi buƙatar taimakonsu ba. Tafiya fa suka yi Iyabo" Takaici da damuwa duk suka taru su kai mun yawa sosai. Muna zaune aka fito da Gwadabe a keken da ake tuƙa guragu zasu tafi ayo mishi hoto. "Baiwar Allah ya kamata ace akwai wani namiji da zai tsaya tare da marar lafiyan ba ke mace ba, kinga da su zasu sashi a keke, kuma su tuƙashi zuwa ɗakin hoto. " Nurse ɗin daya tuƙo Gwadabe ne ke magana. Gwadabe na kalla, shima ni yake kallo ya dafe kanshi da hannun dama, idanuwanshi tamkar garwashin wuta. To mun gode, suna hanya masu kula dashi ɗin." Na faɗa mishi haka, kafin ya miƙo mun wata takadda. "Ki je wancan tagar ki biya kuɗin hoto, in mun fito sai ki bari in mun dawo ki bani" Karɓa nayi jikina na rawa, su kuma suka wuce. Kuka na fashe dashi babu ƙaƙƙautawa, Taiwo da Kahinde suna ganin ina kuka suma sai suka soma kukan. "Iyabo kije ki dawo, wannan kukan ya isa haka kinga ga yara suma sun soma. Jakata na kinkima na je na biya kuɗin hoto na dawo. A taƙaice sai da muka wuni zumbur babu wanda yazo daga dangina ko na Gwadabe, Hafizu mijin Uwani ne ya kawo mana abincin da muka ci, da naga magriba na shirin yi na dubi Gwadabe nace. "Inaso zanje gida in dafo ruwan zafi, in tawo da tabarma." A'a su Babala suna hanyar zuwa. Ɗazu da likita ya kiraki Yaya Hambali ya kira ni a waya" Baima gama bayanin ba sai gasu sun iso dukkansu, harda Yaya Haula tana riƙe da filas na ruwan zafi da kular abinci. Da sauri na tashi a kujera na ba Babala waje ta zauna. Abu na farko daya fito daga bakinta shine. "Ba ga irinta ba, akan son gwanance mace kaje ka kai kan ka mahallaka. Waya sani ma ko daga danginta ne aka bugo maka wani agumun. Duk da sammu a tsakanin direbobi abune mai dogon tarihin gaske muma munsan tarihin. Gwadabe bazan yi maka baki ba, amman kaji na rantse maka da girman wanda yayi ni yayi ka buwayi gagara misali. Kana tashi zaka sallami wannan matsiyaciyar ka auri Laila, in ba haka ba sai in tsine maka ka bi duniya uban kowa ya rasa ka. Banga riba a aurenta ba sai ci baya da koma baya da rayuwarka tayi. Ke kuma na dawo kan ki, ki zauna da shirinki, Allah na tasan kafaɗarshi ƙarshen zamanki kenan dashi, ya'isa haka, inason yarona ya dawo yanda yake. Kin shigo cikin zuriyarmu kin tarwatsa mun kan yara." Da kuka taƙarashe zancen, yaranta na bata baki kan ta dena kuka. Baban Nazifi ya ɗaura da cewa. "Ya zame mishi dole ya rabu da'ita matsawar mune danginshi. In kuma zai sake iyaye da ƴan uwane sai mu gani. Sabida wannan baƙar kadarar matar tashi marar asali yasa na kasa tallafama Gwadabe Babala, amman a baya wanne irin so ne banyi mishi ba." Wannan yace wannan, wannan yace wancan kowa sai da ya tofa albarkacin bakinshi. Mu dai mun yi shiru kamar ruwa ya cinyemu. "Babala kima Allah kar ki zama silar rabani da Iyabo, son gaskiya take yi mun, bazan iya samun macen da zata soni rabin nata ba. Iyakar zamana da'ita babu abunda ta taɓa yi mun na assha." Miƙewa Babala tayi tace. "To gaka ga Iyabo. Ta maye maka gurbina dana ƴan uwanka da baka da tamkarsu. Ta zauna tayi jinyarka, ni kuma babu ni babu kai. A cikinku duk wanda ya tsaya ya kula dashi ban yafe mishi ba, ko ya cire dukiyarshi ya ba Gwadabe. Haula ɗauki abincin da kika kawo mu koma dashi. Da gudu nasha gaban Babala ina haki nace. Babala kiyi haƙuri ni nayi miki alƙawarin Gwadabe na warkewa a ranar zan bar gidanshi rabuwa irinta har abada. Bazan iya tafiya in barshi a wannan halin bane, ko babu komai uban Ƴaƴanane, kuma a zamanmu bai taɓa cusgunamun ba. Nima dashi da aurenshi ya fice mun a raina, wallahi ko baki ce ba ya zama dole in rabu da Gwadabe dan ba shi bane autan maza ba, kuma ba mutuwa zanyi ba. Amman fishinki masifa ne, yana buƙatarku yaya Harisu, Babala Gwadabe na buƙatar adda'arki" Duk wannan maganar cikin dimuwa nake yinta. Majinyatan dake kwance, da masu jinyarsu kab hankulansu a kanmu yake. Tsawa Babala ta daka mun. "Gafara dallah. Ke baki da uwa dama da sai in ce ki je kisa ta mai adda'ar mana. Tunda akan ki wannan ciwon ya same shi, ke zaki yi mishi jinya dan ubanki" Fuu suka fita suka barni. Bansan sanda na durƙusa a ƙasan ɗakin ina salati ba, Allah nake ambato a lokacin wani irin duhu ne ke mamaye mun idanuna. Uwani ce ta ɗaga ni. "Tashi Iyabo meye haka kike kuka kamar ƙaramar yarinya, ɗakinnan kab ke suke kallo. Rabuwa da Gwadabe shi ya fiye miki." Jaye ni tayi ta zo ta zaunar dani a kujera. Gwadabe yana kwance idanunshi a buɗe suke amman yayi zurfi a cikin tunani hankalinshi baya tare damu. "Bara in fita bakin asibiti in siyo muku ko da tuwo ne. Zan yi ma Hafizu filashin in ya kirani zan sa ya kawo ruwan zafi." Bani da niyyar bata amsa, itama bata buƙaci amsar tawa ba ta fice. Ƴan biyu suna ƙasa na shinfiɗa musu ɗankwalina suna bacci. Har Uwani taje ta dawo ni da Gwadabe babu wanda ya tanka ɗan uwanshi. Tayi yin duniya muci abinci mun ƙi yarda, damuwar da take gabanmu ta wuci a tsaya ana saka lomar tuwo a baki, ni in banda ɗaci babu abunda bakina yake yi. Mijin Uwani ma yazo yayi roƙon duniya kan mu ci abinci, ni ko magana na kasa, Gwadabe ne ma yake iya cewa a ƙoshe yake. "Iyabo ki taso mu je gidana, in yaso Hafizu zai kwana gobe mu ma dawo" "Ku barta tare dani, ina buƙatarta a kusa dani, damuwar zata yi mun yawa" Cewar Gwadabe, sai lokacin hawaye suka surnano da idanun Gwadabe wasu sirara. Uwani ta tattare yaran su kai mana sallama suka tafi. Da ƙyar ma'aikatan kiwon lafiya suka barni zan yi jinyar Gwadabe kasancewar ward ɗin na maza ne, akwai wata mata itama ita take ma mijinta jinya, sai muka zama mu biyu. Shiru wajen ya ɗauka na kasa rarrashin Gwadabe shima ya kasa rarrashina. Wannan daren na ba makaranta gari ku hasaso da kawunanku. Washe gari sassafe aka sake zuwa aka fita da Gwadabe zuwa wani hoton. Kafin a dawo dashi sai ga Yemisi da Burodami Debisi, da Lekan. Hannunsu riƙe