Sashe 21
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wannan dare Gwadabe ya sha rarrashi sosai, dan birkice mishi nayi kamar lalatacciyar besfa, da ƙyar ya iya shawo kaina a wannan dare. Washe gari muka wayi garin babu walwala sam daga ni har Gwadabe, dan shi kanshi ina ankare dashi da damuwar da tafi tawa ya kwana. Bayan sun dawo daga sallar asuba ya shigo, sai yace "Bari in ɗan kwanta kaina saramun yake yi sosai, zazzaɓi ne ma yake son kamani" Sai jikina yayi sanyi, a tausashe nace dashi. Allah ya ƙara afuwa, sannu inka karya ina da fanadol sai in baka ka haɗiya" Har ya kwanta sai kuma ya tashi, ina shirin ficewa a ɗakin kenan zan juyo ruwan wankan ƴan biyu. "Dawo ki zauna Iyabo mu yi magana " Babu musu ko kafiya a tsakaninmu, cikin saurin bin umarninshi na zauna ina fuuskantarshi. "Wallahi Iyabo ko tsirara Laila zata yi a gabana ba zata taɓa burgeni ba, domin bana daga cikin mazan da suka fifita kyawun mace, ko dirinta. Ni kyawun halinki, da haƙurinki ya fi ye mun komai. Ai mace ta gari farin cikin rayuwar duniya ce. Zance na gaskiya bani da wata hanya da zan bi in kori Laila a ɗakinnan. Ina gudun yawan fishin da Babala take yi a kaina. Dani dake mu yi haƙuri ki taya ni mu yi mata biyayya ta zauna ɗin,in taga dama ta zauna har mahadi ya bayyana, zata ɓata ma kanta lokaci a banza, dan ko matan duniya sun ƙare Gwadabe ba mijin Laila bane. Iyabo na ƴar duma_duma mai hanci a tsakiyar kumata itace nutsuwata. Kiyi haƙuri nasan na danneki da yawa" Shiru nayi kawai ina wani tunani, har ga Allah Ni kam ina yaye Taiwo da Kahinde aurena da Gwadabe yazo ƙarshe ma, nasan ina tafiya babu makawa Laila burinta zai cika na mallakar Gwadabe a matsayin miji. Iyakar son da zan yima Gwadabe kenan in zama tarihi a cikin labarinshi, ko dan ya samu rabauta, dan fishin iyaye bala'ine babba akan yara musamman fishin uwa al'amarin da girma yake" "Baki ce komai ba Iyabo" Ɗagowa nayi muka haɗa idanu nace. Babu komai Gwadabe, zan tayaka biyayya ma Babala ka samu aljanna ta hannunta, Laila taci gaba da zamanta kuma in sha Allah bazan sake asarar hawayena akanta ba. Dukkan wata ƙaddara ko jarabtar da zata samu bawa daga Allah ne, dukkannin wani tsanani baya dauwama face sauƙi ya samu." Ina gama faɗar hakan na miƙe na fita cikin dakiyar zuchiya muka gaggaisa da matan gida suna tsakar gida anata hada_hadar aikin daya zamema mata jiki a rayuwa. Ɗakin Yaya Haula na shiga na durƙusa a gaban Babala na gaisheta, saida nayi baki biyu kafin ta amsamun a yatsine. Yaya Halima kuwa ciki ciki ta amsa, ni banji sautin muryar tata ba ma, sai dai labɓanta da naga sun motsa. Har zan fita Babala tace. "Zo ki zauna Iyabo inason magana dake" Dawowa nayi na zauna kaina a ƙasa ina wasa da gezar majanyin ashoke dana goye Taiwo da Kahinde dukansu a gadon bayana. "Ba komai bane yasa nace kizo ba dama. Kuɗi nake son ki bani kamar dubu talatin haka, inason zan sai taki in tafi dashi, nayi magana da Baban Nazifi hidima tayi mishi yawa, ke kuma naga kin samu kuɗi a wajen suna sosai" To Babala bari in kawo miki" Na miƙe na fita ina jinjina wannan lamari. Nera dubu talatin cib na ƙirgi na kai mata, tako sa hannu ta amshe ba sannu bare madallah. Harna yi ma ƴan biyu wanka na shiryasu ina ta'ajibin wannan al'amari. Toye na ja muka fita tsakar gida nayi mishi wanka a ƙofar ɗaki ya shigo. Ban gusheba sai da na ɗauraye kayan da ƴan biyu suka cire da wanda nasa naci suna, da wanda nasa jiya, dana Gwadabe duka. Kafin in gama wankin matan gidan suka cike igiyoyin da shanya tsab. Sai mayafi na yafa na shiga gidan maƙota na yi shanyata. Ɗaki na shiga na shinfiɗe ƴan biyu a gado, Toye kuma na shafa mishi mai, yasa kaya. Ina juye ruwan wanka na mayar da ruwan kunu kan wutar. Ina fitowa na dama kunu na juye a jug ɗin silver na mayar da ɗumamen tuwon jiya. Ɗaki na shiga na shirya tsab cikin jar atampa sabuwa fil ɗinkin dai buba da zani, yana cikin kayan suna da Iyaa ta hado mun dashi, na murza kwalli da jan baki, na bi jikina da body milk na Mrs Bukhari, na shafa har a ƙasan mamana kunsan masu jego sai da ta'amali da ƙamshi. Ina gyaran falo Gwadabe ya fito daga ɗaki. Murmushi nayi mishi, shima murmushin ya sakar mun. Yallaɓai ka tashi, ya kan naka?" Bai amsa ba sai da ya haɗe jikinshi da nawa, Laila fa duk abinnan tana naɗe a doguwar kujera tana bacci. "Lafiya lau Iyabo, sai kewarki a shinfiɗata. Irin wannan kyau haka Babbar mace kenan, cinyar sa maganin mai haɗama" Dariya muka kwashe dashi kamar babu matsalar dake damun mu. Inason in ji Gwadabe ya kirani da Cinyar sa maganin mai haɗama, ko Babbar mace, daya faɗa sai in jii ƙibata ta sake burgeni, barenma in nai kwalliya, dan kwalliya tafi amsar masu jiki irinmu. To yanzu dai karyawa zaka soma yi ko wanka?" Ido ya kashe mun yace. "To ba sai ki zaɓar mun ba kawai, tunda dai ni mijin Hajiya ne" Ina dariya ciki_ciki nace. To ka soma da wankan, zaka fi jin daɗin karyawar. Ina faɗar haka na fita, har na juye mishi ruwan a bokiti zan je rijiya in sirko, sai ya riƙe hannun bokitin ƙarfen yace. "In banda fitina irin taki kina jego ina ke ina aiki, gafara cus kawai." Ya ɗauki bokitin yayi bakin rijiya dashi. Baban Nazifi dake zaune a turmi yana rage ƙasumbarshi da aska, ya ja tsaki yace. "Allah wadaran naka ya lalace, Laila da majnun ma ƙarshen tarihin soyayyarsu sam babu armashi a ciki. Gwadabe kayi asara shanyayye fitsararre" Ya ci gaba da askinshi, ni kuma na shigewata ciki. Ina haɗa mana abun karyawa a tire mandiya hamshaƙiya ta tashi. Tsaki ta buga, ta fice fuu. Ni kuma na girgiza kai kawai na dure mana abincin a gefe, ni na tattare mata kayan rufarta na sa mata a saman akwatunanta. Na kunna turaren tsinke na Baba flora ɗakin ya biɗe da ƙamshi. Ina zaune ina kallon wani kaset ɗin yarbawa, shiru_shiru yau Gwadabe zai shigo, gobe ne, har goman safe bai shigo ba. Ni kuma yinwa sai sasiƙata take yi, abinci na zuba na soma cin abuna. Ina kan ci wayata na jiyo kukanta daga uwar ɗaki, da sauri na shiga ɗakin. Wata number ne ba suna, ina karawa a kunne na jiyo muryar Gwadabe. "Nine Iyabo. Kiyi haƙuri muna asibiti tare da Babala. Na je dubata na tarar zasu koma asibiti shine muka tafi tare, muna gamawa zan dawo. Kici abincinki kinji? Zan tawo da cefane" To Shikenan Gwadabe Allah ya ƙara mata lafiya, sai kun dawo. Dan Allah ka gaisheta sosai da jikin." "To shikenan Babbar mace zata ji, ki kula mun da kan ki" Mu kai sallama na ajjiye wayar. Ina gama karyawa sai na shige ɗaki har bacci ya soma ɗibata sai naji ana tattaɓani kamar a mafarki naji ana kiran sunana. Ina buɗe idanu naga ashe Uwani ce." Kai Uwani irin wannan duka haka" Na faɗa ina miƙewa zaune. "Ke dai bari Iyabo, damuwace ta ciyo ni shine na kasa haƙuri sai da na tawo. Amman kafinnan akwai abinci a gidan in ɗan sama cikina, tun duku_duku na bar gida babu abunda naci" Ki fita falo zaki ga tire akwai dumamen tuwo da kunu" "Yanzu kuwa zaki ji labari Iyabo in na take cikina" Fita tayi sai gata da tuwo shaƙe da kwano da kununta cikin ƙaton kofi, bayan taci ta yi gyatsa tace. "Tun safe ni da matan gidanmu muka fita muka bazama gari neman aikin yi yinwa na shirin halakamu da yaranmu. Da ƙyar muka samu aiki mu huɗu. Wani sabon asibiti da aka buɗe a bakin titin layinmu to anan ni na samu nawa aikin na wanke bayangidun asibitin, Hafizu kuma Allah ya so shi ya samu gadin get da ƙyar wallahi, a hakanma saida nayi mishi jan ido ya karɓa, gani yake shi yafi ƙarfin gadi, matar gidanmu kuma nata aikin shara da goge gogen ƙasa ne. Iyabo albashin bashi da yawa sam wannan rayuwa ni nama rasa yadda zan tsoma kaina a ciki ga matsalar gidan haya. Shaddarmu fa wata biyu kenan data rufza me gidan yace bazai gyara ba mu da muke haya a gidan mu zamu gyara. To mu bamu ci ba balle har mu iya gyara masai sai dai fa ko wacce mata tayi kashinta a po ta ɗauka taje ta watsa. Gabaki ɗaya gidan sai wari kawai" Jigum nayi ina saurarenta, yinwa bata da daɗi sam ni kaina a baya mun sha kwana da yinwa mu wayi gari babu abinda zamu ci sai ruwa. Uwani rayuwar ta zama sai a hankali, gashi mutane basa son taimako daga ƙwauri sai guiwa kowa nashi ya sani. Amman a ƙalla aikin zai rage muku sosai, sai ku gina rayuwarku akan albashin da kuke ɗauka kusan yanda zaku tsara komai. Allah yasa dai mu dace kawai amman rayuwarma wataran sai kaji duniyar ta fice maka fit a ranka in matsaloli suka haɗu suka cakuɗe maka. Jiya da kinga irin tashin hankalin dana faɗa da daddare da kin tausaya mun sosai" Nan na kwashe labarin iskancin Laila na bata. "Kusun uwa kuma baki yi kukan kura kin dira a wuyanta kin narki shegiya ba?" Kai na girgiza tare da cewa. Hmmm motsi ma wannan na kasa. Ni da nake zaune a ɗofane Uwani ai ina taɓata zata jijjigemun auren nawa ne, kinga burinta ya cika ai ko?" Sai kuma ta sakko tace. "Sai dai dan hakan amman in ba haka ba wallahi da saita gane kuranta. Amman ke haka zaki zuba ido kuci gaba da zama da'ita ko yaya kike so?" Miƙewa nayi tsaye na ɗauki Taiwo na saɓa a baya, na sake sa hannu na ɗauko Kahinde sima na sashi a kusa da ƴar uwarshi, na ɗamaresu tamau da zanin goyo na bisu da majanyi. Hijabina na zura, na saƙa hannu a ƙasan kayana dake jere a wadrop na ciro