Sashe 142
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
hannu in doɗe mai lafiyar, shi marar lafiyan kuma yana buɗe sai duhu da ɗan ƙyallin tocila kaɗan nake gani Innalillahiwa'innailaihilrajiun na dinga ambatawa. Tada kabbarar Sallah nayi ina sallah ina hawaye ga wata ƙaddara kuma ta kuma samuna. Washegari A gurguje na sake kayan jikina, na buɗe adaka na ciro kuɗi na cusa a jaka na fito. Hama na ƙofar ɗakinta tana kwashe Manshanun data gama burgawa yanzu na iso. Baddo ma na ƙofar ɗakinta tana aikin burga. Hama dan Allah inaso kiyi mun magana da Yaya Hamma ne?" "Dan jaraba da wannan duku_dukun zaki zo neman min miji. To baya nan bai shigo gidan ba" Kafin in ja numfashi in saki sai gashi ya iso inda muke. Yana isowa ya toshe hancinshi yana ƙoƙarin shigewa ciki. Dan Allah inaso zanje asibiti Yaya Hamma" "Sai kin dawo" Ya bani amsa a taƙaice. Hama na kalla, na kuma kallonta da kyau nace. In kinfi ƙarfina baki fi ƙarfin Allah ba. Baddo yima Yuguda magana zaki rakani asibiti" Hama ta cokaro ɗaurinta gaba bata ce dani komai ba. Baddo ta bar abinda take yi ta shiga ɗaki, bata jima ba ta fito goye da diyarta. Ɗakin Yafendo muka je na sanar mata abinda ake ciki. Nera dubu biyu ta miƙo mun. "Ungo ku riƙe a hannunku, Allah ya ƙara sauƙi bazan hanaki zuwa asibitiba a birni kika rayu shiyasa, amman babu irin maganin da babu a gargajiya. Nima zan fita da hantsi inje in karɓo miki maganin idon, da tofi" Kudin Baɗɗo ta karɓa mu ka yi mata Sallama. Baɗɗo kina jin wari a jikina dan Allah?" Hawayen daya zubo mata sanadin tambayar dana yi mata ta share. "A'a Adda. Ina tunanin asirin warin jaɓa Hama tayi miki dan ta rabaki da mijinki. Jiya muna tsakar gida muna hira ai ya baro ɗakinki yazo ɗakinta. Shine take tambayarshi me yazo yi ai ba kwananta bane. Shi kuma buɗar bakinshi yace warin jaɓa kike yi mishi, dake da ɗakin. Shine nake tunanin irin asirin da Lanti tayi ma kishiyarta kenan, ita kam baiwar Allahn mutuwa ma tayi daga ƙarshe. Sai da mijin ya shekara biyu tim baya shiga ɗakinta, baya cin abincinta, baya ko kallon inda take. Wannan baƙin ciki shi yai sanadinta. Ƙaƙa sara ƙaƙa kundai ji halin da Jabu Iyabo take ciki.