← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 237

Sashe 152

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kano:. Saukarsu Gwadabe ke da wuya a garin Kano suka wuce unguwarsu Iyabo gidansu Uwani. Mahaifiyar Uwani Hajiya ce ta fito. "Au Gwadabe shine kuka tsaya a waje sai kace baƙi bismillah ku shigo" Dole haka suka kutsa cikin gidan. Hajiya ta shinfiɗa musu tabarma suka zauna aka gaisa a nitse. "Dama Hajiya gidan Uwani muke son yaro ya rakamu." Hajiya tace. "Allah sarki ai kuwa kunyi saɓani Uwani ta tafi Jaɓiɓi wajen Aminiyar tata Iyabo acan take aure, to tafiyar ta gaggawace ma dai. Kuma tunda ta tafi ba mu yi waya ba, yaranta ma suna nan tare dani" Tashi ɗaya Gwadabe ya koma kalar tausayi. Ba baƙin ciki yake da auren Iyabo ba. Ba kuma baiji daɗin jin tana gidan aure bane. Kishine na zahiri wanda bashi da masarrafarshi. Sai yaji ƙirjinshi yayi mishi nauyi. "To Hajiya ko zan iya samun lambar wayar Uwanin ko ita Iyabo ɗin?" "To gaskiya ni babu waya a hannuna. Yara da zasu baku lambar gashi duk kowa ya fice. Sai dai in gobe zaku dawo sai in sa yara su rubuta lambobin a takadda" Bara'u yayi carab yace. "A'a ki barshi Hajiya. Nanda sati ɗaya ma dawo kafin lokacin Uwanin ta dawo sai muzo a kaimu" Hajiya tayi jim tace. "Amman Allah dai yasa lafiya ba wani abun bane ba ko? Naga kamar kun matsa lallai sai kunga Uwanin" murmushi Gwadabe yayi yace. "Babu komai wallahi Hajiya. Dama dai labarin Iyabo muke son ji a bakin Uwani. Baya ga wannan babu komai" Dariya Hajiya tayi irin ta manya tace. "Allah sarki. Ai indan wannan ne ba dole sai kun nemi Uwani ba. Iyabo dai tayi aure a dangin mahaifiyarta. Dan kamar Uwani tace mun da gyatumar yaron da ita Iyabo ta aura. Da gyatumar Iyabo ya da ƙanwa suke. Sun jima suna son junansu tun su Uwanin da IYABO suna Saudiyya. Auren bai jima ba da akayi shi." Sai kallon kallo tsakanin Bara'u da Gwadabe. Gashi babu damar su matsama Hajiya da tambayoyi. Saidai abubuwa da yawa sun cunkushe kan gwadawa. Na farko shine Saudiyya da yaji Hajiya tace tun suna can. Na biyu jin a irin dajin da Iyabo taje tayi aure. Yasan labarin ƙauyen a bakinta amma bai san komai baya ga labarin bakinta ba." "To Shikenan Hajiya mun gode. Mu zamu koma, a isar mana da saƙon gaisuwarmu wajen Uwani dama Iyabon." Cewar Bara'u kenan. Shi kam Gwadabe yana cikin dabaibayi. "Zasu ji. Ya yaran duk suna cikin ƙoshin lafiya dai ko?" Bara'u yace. "Suna lafiya. Suna karatunsu arabi da boko. Hajiya mu zamu wuce to" Bara'u ya zaro jaka biyar ya ajjiye ma Hajiya. Sukai mata sallama suka fito. Suna zaune a motar Takai Bara'u yace. "Wannan shirun yayi yawa Gwadabe me kake nufi ne. So kake IYABO ta zauna babu aure ko me? Naga kai mata biyu ka aura rana ɗaya" A fusace yace. "Na auresu ne a bisa tayin aurensu da akayi mun. Waɗanda sukaimun tayin sun fi ƙarfin komai a wajena. Iyabo itace rayuwata Bara'u " "To itama saika ɗauka umarnin mahaifiyarta tabi tunda ai kaji ance ɗan uwanta ne ta aura. Ni na ɗauka ma Debisi ne zai aureta wallahi" "Hakane Bara'u. Ina tayata farin ciki da auren data yi. Sai dai ina tayata jimamin zaman ƙauye. Dan a yadda take bani labarin ƙauyan ƙauyene ƙayau, gasu da ƙauyanci da ƙarancin addini. Ko asibiti babu fa, balle wutar lantarki, kaga babu ruwa babu kwalta, babu makarantu." Jim Bara'u yayi yace. "Sanin da ba. Kasani ko sun samu tallafin gwamnati. Ita kanta sau ɗaya fa kace ta taɓa zuwa tun tana yarinya. Inka lissafa daga lokacin da taje zuwa yanzu ƙila sun samu ci gaba. Ko shekara biyar baya ka kalli takai ai kasan an samu gagarumin ci gaba ko? Ni batun zuwansu Saudiyya ita da Uwani shi nayi tunanin zaka yi nazari akai ma" Kai Gwadabe ya dafe tare da lumshe idanunshi. Baice komai ba, tunani da lissafe lissafe yake ta faman yi har Allah ya dawo dasu Takai lafiya. Cikin gidan ma daya shiga wani tarin tulin takaici ya tarar. Hadiza sai kumbura take yi kamar kwaɓin gurasa. Sakina da Shafa su kuma sunata faman hirarsu da nishaɗi. Gefe guda Gwadabe ya zauna jigum. "Bara'u Gwadabe ba lafiya ne?" Bara'u ya amsa ma Hadiza da cewar. "Kanshi ke ciwo ga hanya mun shawo" Shafa sai tabar abinda take yi ta koma wajen mijinta ta kai musu abincinsu. Lamarin daya sake zugunɗuma fishin Hadiza ta sakei hawayen da take riƙewa kenan. Ta kullace wannan wulaƙancin da Gwadabe yake yi mata dan yaga ya kawota garinsu. Da yamma liƙis suka dunguma gidan Zulƙi sun ko yi saɓani Zulƙi da iyalanshi basa nan sun tafi wani taro na masu kujeru a hannu a Abuja. Gwadabe ya kwashi su Hadiza harda Bara'u da Sakina suka je. Kwanansu biyu a gidan Tamu. Ayashe itama ta tarbesu tarba me kyau sosai. Nan da aka haɗu dole saida labarin Iyabo ya ratso ta cikin zancan. Hadiza tana mamakin irin tasirin Iyabo a cikin rayuwar Gwadabe da duk makusantanshi. Wai shin wanne irin kirkine da Iyabo, wannan irin kawaici da juriyane da'ita? Hadiza taima kanta tambaya. Kishi na rugurguza zuchiyarta d gangar jikinta. Saita tsinci kanta cikin son zama kamar Iyabo badan komai ba sai dan kishin mijnta da son mantar da Gwadabe Iyabo. Wannan dalilin nata yasa ta cakaloma Ayashe da Sakina zancan Iyabo. Sai dai me da suka soma zana mata Iyabo sai taji e lallai takai macen da dole ta tsaya a zuchiyar ɗa namiji. Sai taji a madadin ta zauna kishin Iyabo ya hanata jituwa da Gwadabe ai gara ta ari rigar Iyabo ta yafa. Amman me a daren ranar Hadiza ko runtsawa takasa yi. Sai jujjuya al'amura take yi a zuchiyarta wata zuchiyar tace da'ita. "Ashe baki cika mace ba in har sai kinyi koyi da halayen tsuhuwar matar mijinki. Kenan ke ba zaki iya juyarma da mijinki hankali ba sai kin zama irin matarshi? Ai kamata yayi kema ki ɓullo mishi da sabon salon tarairaya da tattalin daya doke na beyerabiyar matarshi ba ki tsaya kina bin diddigin halayenta ba" Ai sai ta hau kan shawarar zuchiyarta tayi ɗare_ɗare. Haka dai suka gama kwanakin da zasu yi suka tarkato suka baro Takai da tarin tulin tsarabobin da Sakina da Bara'u sukai musu ƙunshi_ƙunshi. Motarsu tana gudu a hanya. Hadiza zuchiyarta na gudu da tunanin mafitarta itafa tana ji tana gani ba zata bari Gwadabe ya sauya mata ba ta zama itace ma bare ba. Jibi Shafa tun shigowarsu motar take ta janshi da hira ya sake sai amsata yake yi sunata nishaɗinsu. Ajjiyar zuchiya ta sauke haƙiƙa ta fahimci Gwadabe ya gundura da ƙorafinta da saurin fishinta. Ta daɗe tana lura ita Shafa irin matannanne da kamar basu san ciwon kansu ba, kuma ba komai ke ɓata musu raiba. Da ire_iren wannan tunanin bacci yai awon gaba da Hadiza ɗiyarta na rungume a jikinta itama baccin take yi. Juyowa Gwadabe yayi ya kalleta ya lumshe idanu. Hadiza tana da wani matsayi mai girma a zuchiyarshi yana sonta. Sai dai ɗabi'unta na ƙorafi, yawan fishi sun kaishi maƙura shi yasa a wannan karon shima yayi watsi da lamarinta. Ummi ya zare a hannunta hakan yasa ta farka da sauri tare da sake cabke ɗiyarta. "Nine ba wani ba. Kawota ki samu kiyi baccinki" Miƙata tayi ta koma baccinta ba tare da tace dashi komai ba. Sai dare suka isa gidan sosai. Sun jima sosai suna buga ƙofar gidan kafin Mammada yazo ya buɗe musu. "Sannunku da dawowa mutanen najeriya kune da tsohon darennan Gwadabe?" Matan ciki suka yi, Gwadabe ya tsaya suka gaisa da Mammada kafin ya ƙule ɗakin Shafa. Hadiza tana kwance sai juyi take yi fitowarta daga wanka kenan. Tayi tsammanin Gwadabe ko babu komai zai leƙo yai musu sallama ai. Amman sai taji shi shiru a ɗakin Matarshi. Washe gari ma ta jima sosai tana jiran ya shigo su gaisa da taji shirun yayi yawa dole ta goya ummi ta fito ta nufi ɗakin Shafa dan a ƙofar ɗakinta aka jibge tsarabar. "Shafa Gwadabe yana ciki kuwa?" A kitchen ta samu Shafa tana zuba abincin da zata ci. Ita sai lokacin ma ta tuno ashe ko karyawar batai ba. Sai da Shafa ta gaisheta tace. "Da wurwuri ya fita zaije cin kasuwar Damagaram. Ko ya shiga ɗakinki kina bacci ƙila" Wannan abu ya daki Hadiza sosai, sai dariyar yaƙe tayi tace. "Babu mamaki kam dan ban jima da tashi ba. Bari in kunce tsarabar zan shiga ma da su Baba nasu' "To Yaya gasu nan. Nima inna gama karyawa zam shigo cikin gidan " Hadiza dai zuchiyarta na tafasa ta yi cikin gida da tsaraba. Saida ta mikawa matan malam nasu tsarabar kafin ta nufi ɓarayin Baba Fhatsima. "Zafine a garinne Hadiza naga dul kin rame, ga ƙuraje duk sun feso miki?" Cewar Baba Asshi dake duƙe tana dauraya. Baba Suwaiba tace. "Takai fa ƙauyene sosai. Ni nasan ƙauyan da jimawa dole su rame ai" Hadiza dai bata ce komai ba tayi murmushi tasan abune mai wuya ƴan gidan su canja halinsu. Tana shiga ta samu Baba Fhatsima na shan fura. Yaya Tasi'u yana zaune a gefe yana cin ƙwadon zogale." "Hadiza kaddai kune jiya da daddare kuke ta faman dukan ƙyaure?" Cewar Yaya Tasi'u kenan. Murmushin dole tayi mishi tace. "Mune Yaya Tasi'u shigowar dare muka yi. Ina wuni yasu Safara'u, da Anti Badi'a?" "Basa nan sunyi tafiya shekaran jiya suna da biki" "Baba ina kwana mun sameku lafiya?" Abunka da uwa tuni ta gano Hadiza na cikin damuwa ga idanunta sun farfaɗa. "Lafiya lau ya mutanan Takai, inasu Sakina da Toye?" Sai Hadiza ta ɗan sauke kanta sai hawaye shar_shar. Yaya Tasi'u ya miƙe tsaye yace. "Sakara bata da aiki sai shirme. Baba ni zan wuce wajen aiki saina dawo" Baba Fhatsima tace. "To a dawo lafiya. Kar ka manta da maganarmu akan Balaraba kayi tunani ina sauraren amsarka daga yau zuwa gobe" Bayan Yaya Tasi'u ya fice Baba Fhatsima ta mayar da hankalinta akan Hadiza. "Wani abunne ya faru a Takai ɗin. Ko ke da mijinkinne, ko kuma abokiyar zaman taki ce? Ki nutsu kiyi mun bayani" Cikin shessheƙa Hadiza tace. "Baba Tunda muka shiga Takai Gwadabe yaga Shafa da
Chapter 152 · 0% Book details