← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 237

Sashe 8

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

na yanke hukunci kai baka isa ka koya mun yanda zan yi ba. Ka tashi kawai ku wuce in ba so kake ranka yai mummunan ɓaci ba" Cikin faɗa sosai Babala take yin magana, har muryarta tana rawa. Ba shiri na miƙe har wani jiri nake gani tsabaragen kishi. To Babala zamu koma, sai mun sake zuwa kuma. Amarya Allah ya zaunar da'ita lafiya a gidanta" A mugun fusace Babala tace. "Ameen in da gaske kike yi baƙar muguwa kin rabani da abunda na haifa. Kema in sha Allah haka wata zata rabaki da ɗanki kiji in da daɗi" Bance uffan ba na ja hannun Toye muka fita bana ko gani da kyau. Ji nayi duniyar na juyawa dani, kaina na wani irin saramun tamkar zai rabe biyu. A ƙofar gida na nemi dakali na zauna jikina na rawa. Tsawon shekaru shida ina shanye dukkan abunda dangin Gwadabe suke yi mun. Amman ji nake yi kamar ma zamana da Gwadabe ƙarshe yazo kawai. Wallahi bazan iya dai dai da kwana ɗaya a ɗaki tare da Laila ba. Gara ni in matsa sai su aura mishi ita zaifi. Wasu zafafan hawayene suka gangaro a kumatuna. Ƴar ƙaramar wayata ce ta soma kuka, wayar da tunda nazo ba wanda ya kirani sai yanzu. In zaro wayar a jakar na kasa sabida tsabar turirin da zuchiyata take yi. Laila ce ta fita kici_kici da fantimotai guda uku hawan hawa, harda wata ƙatuwar jaka. Sai fara'a take yi tamkar wacce akaima bushara da gidan aljanna. Kawar da kaina nayi dan bana ƙaunar sake ganin fuskar Laila. A sanyaye Gwadabe ya fito daga cikin gidan. Duk yanda yaso mu haɗa idanu naƙi bashi damar hakan. Bara'u da Sakina ne suka katse mana tunaninmu. Gwadabe ya janye Bara'u zuwa gefe. Sakina ta zauna a kusa dani hannunta riƙe da baƙar leda. Laila tana daga gefe tana amsa kiran waya. "Meke faruwa Iyabo duk na ganku a birkice haka, naga Laila da fantimotan aurenta?." Hmm Babala ce ta danƙa amanarta a hannun Gwadabe, suna nufin tare da kishiyata zan zauna, bayan ta gama sanin sirrina sai a bashi umarnin aurenta." A hasale nayi maganar kuka na tunkuɗo kanshi. Sakina ta riƙe haɓarta tare da sakin baki cike da ta'ajibi tace. "Danƙari maƙari. Kika ce me, Lailan ce zaku tafi da'ita ta zauna a wajenku? Lailan da duk ƙauyannan ba wanda baisan irin son da take ma Gwadabe ba. Ke a wata ruwayar fa cewa akayi sabida Gwadabe ta kaso aurenta. Haka naji a wajen Goggona, kuma hakanne Bara'u ma ya sani. " Kaina ne naji yayi wata iriyar buɗewa, gabana yaci gaba da harbawa. Zuchiyata ta shiga watsa jini bisa rashin ƙa'ida, take na soma haki tamkar numfashina zai dakata. Yawu nake so in haɗiya in jiƙa maƙoshina da nake jin tsabar bushewa ya shiga daddarewa. Kika ce me Sakina?" Da ƙyar na jawo numfashi daga huhuna zuwa cikin bakina, harshena kuwa da ƙyar na iya sarrafashi. "Wallahi Allah kinji na rantse Laila sabida Gwadabe ta kaso aurenta, kowa ya sani." To gata ga Gwadaben, dan ni muna isa zan tattare inawa inawa in bar musu filin ɗakin, tunda dama abinda suke so kenan. Wallahi Sakina bazan iya zama inuwa ɗaya da Laila ba, gidanmu zan koma" Hawayena yaci gaba da zuba a kan kumatuna. Dafa kafaɗata Sakina tayi tace. "Bazan ce kar ki ƙwaci ƴancinki ba Iyabo. Haƙiƙa kin shanye abubbuwa masu yawan gaske tun daga aurenku kawo iyanzu. Amman barma Laila gidanki ba mafita bane Iyabo. Kiyi tunani kafin yanke hukunci, kar ki aikata aikin da zai jefa ki cikin dana sani marar amfani." Murmusawa kawai nayi dan banji akwai abinda Sakina zata faɗa yai tasirin hanani barma Laila Gwadabe ba."
Chapter 8 · 0% Book details