← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 237

Sashe 86

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Assallamu alaikum mutanan kirki Ina Miko gaisuwa daftn alheri👏🏼kamar yarda muka Saba duk sallah munayin adashin kayan sallah Dana kayan kitchen to wannan lokacin ma lokaci yayi @ zee Musa collection taxo muku da hanya Mai sauki domin ga number 📞📞📞08029882667 💃🏼💃🏼💃🏼🤣 samun damar mallakar duk abunda kakyeeda bukata. Cikin sauki ta hanyi Yi muku adashin gata 💃🏼💃🏼💃🏼🤣 idan matsalarki rashin sabbin plates 🍽️idan axumi yaxo 🍽️ to ansamu hanyar maganin wanan matsalar idan kina son siyan atamfane da lace Amma bakida kudi a lokaci daya to duk Dama ta samu Zaki iya shiga wannan dashi namu mu Aiko muki da kayanki ako Ina kikyee da yarda Allah
Akwai
1, zubi duk sati 2k sati 10 kwasar kayan 20k 💃🏼
Akwai zubi duk sati 2k sati 20 kwasar kayan 40k har zuwa duk yanda mutum yakyee bukata zamu turo maka da kayanmu idan lokacin kwasarka yayi da yarda Allah kazabi duk abunda kakyee bukata da yarda Allah to mekakyee kikyee jira ki tintibene domin jin yarda raguwar tsarukan sukyee insha Allah idan Kuma kyee ma,aikaciyace to kyeemafa 💃🏼💃🏼💃🏼hardakyee domin akwai tsarin zubi duk karshen wata iya yarda Zaki iya idan lokacin daukarki yayi ki Fadi duk abunda kikyeeso atura muki ko menene har supplement domin gyaran jikin domin ba iya Kaya muka tsaya ba wasu abubuwan ma sai ka shiga group Dina zakasha kallon sabbin abubuwa masu kyau da Kuma sauki
Akwai kayan Yara yankanti
Akwai takalman da jakunkuna da mayafai
Da sauran kayan amfani kyeedai maxa ki hanzarta kafin mu Fara zubi
Insha Allah zamu Fara zubi a farkon( sabon watan August ) Allah yadafa mana nagodee sossai zee Musa takuce 💃🏼💃🏼👍🏻🥰 ga number din da zaa iya damuna 💃🏼💃🏼🤣📞📞 08029882667

*Ina kuke mata ƴan ƙwalisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haɗaɗɗun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
07082649563 whats app number kira 07036028230

NAMA YA DAHU...
ROMO ÆŠANYE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

11
Ga wannan a rage zafi zuwa monday zan dawo ka'in da na'in

09153081057
Ga masu san magana dani kai tsaye ta whatApp ga number na
Masoyana sunata mun ƙorafin babu number na a jikin littafi kuma suna son muyi zumunci, ƙorafi ya ƙare.

"Na horeki da haƙuri da kawaici. Kiyi zaman aure irin wanda mahaifiyarki take yi. Sannan kiyi kishi irin nata Hadiza. Allah yayi albarka Allah yasa sai dai a fitar da gawarki. Ga wannan ɗan kunnen zinarin ki adanashi zai miki Amfani, ko da zaki siyar ki tabbatar juya kuɗin zaki yi ba wasa dasu ba. Altine ku tafi da'ita" Altine ta ɗaga Hadiza suka fita aka kaita ɗakinta. Barinta akayi ita da ƙawayenta sunata hirarsu. Ƴan uwan Shafa kuma sai jere suke yi mata dan a gaskiya Shafa tafi Hadiza kaya musamman kayan ƙawa na ɗaki, dangin samiru da kwalla. Kuma sai da aka mata bango guda na kwalliyar tasa, sai ɗaukar idanu suke yi. Duk labari ya isarma Hadiza, sai taji babu daɗi domin ba hakan taso ba. Ƴan kuɗaɗen data samu na gudunmawa ta ɗungume ta ba Aminiyarta suka ƙaro mata kumbula da kwalla. Kafin magriba har sun dawo, suka kuma sherawa, tare da sake ma ɗakin fasalin daya dace.

Ta bangaren angwaye ana fitowa sallar magriba ko wanne ya jaye abokanshi suka nufi cikin gida domin gabatar da WATSI. Inda ake ma ango watsin alawa, da kuÉ—i. Ana samun kuÉ—aÉ—e sosai. Ko wanne ango dangin mahaifiyarshi ne suka shimfiÉ—a musu taburmai. Akaita watsin kuÉ—i da cingam. A wannan rana angwayen sun samu kuÉ—i na mamaki domin wannan ranar tana daga cikin ranakun nuna bajintar dangi, da amfanin tarin dangi.
Su Gwadabe sun samu kuɗi sosai a wannan rana dan dangin Baba Fhatsima masu kuɗi rabinsu da kwata suke Aure, uwa uba ga Yaya Tasi'u shima ya nuna bajintarshi, da yarsu Zarah. Wankan kudi kawai akaita musu, lokaci ɗaya kallo ya dawo wajensu Gwadabe. Mata sai ihu da guɗa suke yi. Dangin Baba Fhatsima sukaita musu ɓarin kuɗi kawai. Kiran sallar isha ne ya dakatar da abun. Nan suka kwashe kuɗaɗensu a buhu suka yi gaba. Nan kuma aka shiga kawo amare ɗakunansu, tare da bataliyar ƙawayen Amare. Da misalin sha ɗayan dare gungun motocin ƴan kawo Amarya suka iso ayari guda. Bus biyu, da karamar mota biyu, ƙaramar mota ɗaya ta amarya da ƙawayenta ce, ɗayar ƙaramar motar ta abokan Gwadabe ce, Bus ɗinnan kuma yaran mata da tsofaffi, da yara ƙananu ne aka kwasosu, kunsan dai yanda ƴan ƙauye suke tafiya raɓaɓe _raɓaɓe da bataliyar yara. Cikin gida aka shiga da iyaye tsofaffi, da yaran mata. Ƙawayen Amarya da amarya kuma aka barsu a ɗakin amaya. Su Bara'u kuma suna waje sun haɗe cikin samarin maraɗi sai shan gahawa da gashasshen nama suke yi. Kofar gidan malam kamar rana tsabaragen taron maza abokan angwaye, kowa ya haɗa dabarshi da abokanshi. Ga almajiran malam sai daudalar cin tuwo suke yi anata nishaɗi. Cikin gidanma haya_haya duk inda ka kutsa. Duk an zube a tsakar gida sabida yanayi na zafi ga tarin jama'a.
Ƴan Takai sun samu tarba da abinci lafiyayye da soyayyun ƴaƴan shila harda lemun limca, da 7up.
Ƙawayen Amarya nama da shayi aka tarbesu dashi, sai bireɗensu suke yi.
A tsakankanin Amare Takwas da suka tare a ɗakunan mazajensu. Ko wacce an zuba mata kaya wannan na wane wannan, ga gara ta ban mamaki da akayo musu, ko wacce ɗan ƙaramin kitchen ɗinta cike da kayan masarufi, wasu harda miyoyin kaji aka haɗosu, wasu kuma dambun nama. Ko wacce Amarya tana a tsakankanin ƙawayenta sunata farin ciki. Saɓanin Hadiza da Shafa da zuchiyarsu take cike da zulumi gami da fargabar haɗuwa da juna. Ko wacce a zuchiyarta tana fatan tafi ƴar uwarta ko da da abu ɗaya ne ta fannin halitta. Hadiza tafi Shafa shiga cikin damuwa dan ita hakan ya taɓa mata annurinta, sai tayi laƙwam ta yi tagumi tana kallon ƙawayenta zaurawa da matan auren da suka nace sai sun tayata kwanan ɗakin miji. Su kuwa sai dariya da bada labarin kishiyoyi, da irin makirce_makircen wasu matan suke yi. Ta bangaren Shafa kuma ita tsoronta ɗaya ne kawai, yanda take ji da ganin budewar idanun zaurawa da ilimin zaman aure da suka fi ƴan mata dashi, shine tsoronta, dan ta fahimci tamkar Gwadabe yafi bata lokacinshi fiye da ita. Amman da tamai ƙotafi sai ya nunar mata ba hakan bane yanayin aikine kawai ke hanashi kiranta a waya.
Da Waɗannan tunane_ tunane dare ya tsala. Maza a ƙozar gida suka kwana. Ƙawayen Amarya da zafi yayi zafi a tsakar gida suka kwana abinsu.
Washe gari aka tashi da buɗar kai kenan. Tun sassafe Amare sukaita kacaniyar wanka, ƙawayen Amarya kuma ko wacce da abinda take yi dai.

Cikin gida:
Kukan yara da hayaniyar mata kawai kake ji. Amaryar Malam da Baba Asshi suna daga gefe suna gulma.
"Malam ya sakar mata kuɗi sai wadaƙa take yi dasu. Da anyi magana Malam yace ɗanta ne mai kuɗin gidan. Kinga wata sarƙar zinare da ta saka jiya kuwa, kuma bata sa ko ɗaya daga kayan da akayi mana na fitar biki ba. Shaddoji take ta sakawa masu tsada." Cewar Baba Asshi wacce takai wuya tun sanda aka soma biki, da irin abincinnan da dangin Baba Fhatsima sukaita dafawa na alfarma dan basa ko cin abincin bikin, nasu abincin suke girkawa daban. Da kuma irin kayan ɗakin da Tasi'u yaima Hadiza ba irin na sauran yaran ba, dan hatta gara na Hadiza yafi yawa. Ga watsi da kuɗi da su Baba Fhatsima sukaita ma su Auwala, ga irin suturu da Baba Fhatsima take ta ketawa. Waɗannan abubbuwa sune suka haɗi suka tsaya ma matan Malam. Yaran gidan sai gulmar abubbuwa suke taima iyayensu mata, su kuma sai tauna lamarin suke, suna dagon maganganu masu nauyi da suke shirin fesarma Malam in an gama bikin.

Baba Fhatsima:
Tana tsaye cikin farar shadda da ɗan kunnen azurfa, da Ƙannenta suke maganar abinda ya dace a dafa ma baƙi. Altine tace.
"Ga farfesun naman rago sukutum tun asubar fari Lamiso ta ɗaura. Wanda za a shigar ɓarayin Amare baki ɗaya. Sai ruwan shayi da burodi inaga ya isa haka. Ni batun abincin buɗar kaima zanyi miki Yaya. Anan ɓangaren naki ne za ayi yau dai biki zai ƙare?" Baba Fhatsima tace.
"Yauwa Altine kinyi kyan kai, dama na fison a basu lafiyayyen kayan kari. Dangane da abincin buɗar kai matar wannan yaron Badi'a komai yana hannunta ita zata yi, abincine nasu na yaran zamani zata yi dake ba mai yawa bane, Amare kaɗai za a ɗibarma sai ƴan uwana dake ɓarayina, sai abokan Malam. Goggo Mairo tace.
"Amman Yaya tun jiya Asshi take takalarmu da faɗa, sai ni nake ta daddanne Altine akan kada ta sake tayi magana. Yaron Saminu ɗazu suna alwala a ƙofar ɗakinta tana fitowa ta shiga ƙunduma musu ashariyar da duk wanda yaji yasan da iyayen yaran take yi ba dai waɗannan kuca _kucan yaran ba." Baba Fhatsima tace.
"In banda ke da abinci Mairo. Ai Asshi ba zata canja ba, mai hali baya taɓa fasa halinshi. Ku dai ku yi watsin ruwan tsarki dasu, maza a tabbatar an sallami baƙi kowa ya samu Abinci. Ke Altine ki dubo mana kwanan Amare" Baba Fhatsima tana gama faɗar haka ta wuce turakar Malam. Goggo Altine ta nufi ɓarayin Amare ta dubo lafiyarau. Ko wacce tana tare da danginta, Amare anci ado, ko wacce tubarkalla kyakkyawa da'ita gwanin sha'awa. Haka dai aka gwangwaji buɗar kai, akaci aka sha harda kiɗan ƙwarya a tsakankanin matan. Zuwa bayan Isha taro ya watse gida ya rage daga baƙi sai ƴan gida.
Chapter 86 · 0% Book details