Sashe 47
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muna gama ci sai ga Yaya Hamma ya shigo. Yana saye da wani yadi mai ruwan bula ɗinkin ƴar shara, yadinnan duk ya gaji yayi laushi sosai sai laɓewa a jikinshi yake yi. Wandon jikinshi kuma na koren yadi ya saka ya ɗauko hular tashi ka fiye naci irin hular da fulani suke mugun so ɗinnan ƴar madina mai fara da baƙa a jiki, ƙafarshi kuma saye da takalmin roba mai ruwan bula duk ya fashe, sai ƙamshin wani turare mai gafin ƙamshi yake yi, daya isa wajensu Yafendo dake akwai fitilar aci bal_bal na gango kwalli rambaɗe a fararen dara_daran idanunshi har zazzagowa yayi. Bayan ya gaisa dasu Yafendo yayi ma Baba bayanin yazo ya kaimu dandaline, sai ya fita waje ya bamu sarari dan mu kintsa. "Daso maza ku tashi ku shirya abun nema ai yau ya samu ko?" Dariya mu ka yi mata kawai. Ni dai mayafi kawai na ɗauka, saye nake da koɗaɗɗen riga da zane. Saɓanin Daso da sai da ta shafa kwalli harda janbakin majigi tasa ma labɓanta. Cikin zaulaya nace. Harda kwalliya ko za'a samo mana bazawari ko?" Dariya tayi kawai tace. "Kayya, ai tunda na rasa Chubaɗo ban sake tsaiwa da kowa ba. Ni abunma wani iri ba fasali yake yi mini" E dole zaki ji banbarakwai wai namiji da suna Hajara. Amman ya muka iya haka Allah ya zaɓar mana. Fatan shine Allah ya sadamu da mazajen da zasu ji tausayin rauninmu. Gara ma ke Daso mijinki rasuwa yayi fa. Ni fa Gwadabe yana doron duniyarnan rabamu akayi a bisa tursasawar mahaifiya da danginshi" Siraran hawayene ban aune ba suka biyo kan kuncina. Dafa kafaɗata Daso tayi jikinta a mace tace. "Mu yi haƙuri kawai mu rungumi ƙaddararmu. Allah yana sane damu, bai mance mu ba. Ta yiwu ya shirya mana kyakkyawar rayuwa a gaba. Ta yiwu kuma wahalar rayuwarmu ne zai fara. Amman duk abinda ya samu bawa ya fauwala shi ga Allah " Wannan gaskiya ne. Muna fatan kyakkyawar rayuwar a gaba. Allah ya sadamu da mazajen da dan so zasu ji kamar su mallaka mana numfashinsu dan mu daɗe mu yi ƙarko. Mu je mun bar Yaya Hamma a waje yana ta faman jira" Kafinma in rufe baki muka jiyo Yafendo tana kwaɗa kiran sunanmu tana yaren Fullanci. Ba shiri muka fito tare da ficewa a gidan. Ko da muka kama hanya, sai cin karo muke yi da mata da samari suna nufar dandali. Ina gefen hannun daman Yaya Hamma, Daso na gefen hagunshi mun sanya shi a tsakiya. Sai hira yake janmu dashi, Daso ce ke bashi amsar duk abinda ya tambaya. Ni tunanin Gwadabe da yarana, da kuma tunanin ta wacce hanya zanbi dan ganin na sanya Dada a farin ciki dariya da walwalarta ta dawo kawai nake. Wani shashe na zuchiyata sai kawai katsaham yace. "Me zai hana ki nemi Uwani in dai bata tafi ba, kema tayi miki hanya ki tafi. In kika tara kuɗi ne kawai zaki iya ɗauke mahaifiyarki ki rabata da azzalumin mijinta, ki kuma rabata da tallan Nono. Wannan shine hanya mafi sauƙi. Tunda ba kya kashe mata aure ba tare da kin shirya mata gidan da zata rayu da yaranta ba, kuma ba zaki hanata tallan nono ba har sai ke kin samu abun yi, ko kuɗi a hannunki da zaki ma rayuwarta hidima kamar yadda mahaifinki yayi mata kafin ya rasu" Nan take sai nake ganin kamar ma na samu mafitar cire Dada cikin ƙangin rashin ƴancin da take ciki. Dan a shirye nake ko matakin shari'a ne zan bi muddin yaƙi sauwaƙe mata igiyar ƙaddararran autenshi. Lokacin dana kwanta jinya take yawan sintirin zuwa dubani. Cubu ranar ta shigo da kuka take labarta ma Yafendo cewar Dada tana gida Baffansu ya daketa ya kumbura mata fuska, sabida sintirin zuwa dubani da take yi wai ya isheshi sai kace nice kaɗai ƴar data haifa. Lamarin da yasa ƙannena suka haɗe kansu suna kuka, tare da adda'ar Allah ya kawo ma Dada mafita ya cireta a wannan ƙangin. Daga ranar kullum ƙwaƙwalwata cikin tunanin sama ma Dada mafita nake, ko da kuwa zan rasa tawa mafitar. Sai yau Allah yayi na tuna abinda nake ganin zai iya kawo ƙarshen hawayen Dada. Tafiya Kano ya kamani gobe da izinin Allah, dan bahaushe gwanin iya tsara zance cikin hikima da azanci yakance da zafi zafi ake dukan ƙarfe, ko kuma yace da safe ake kamun fara" "Jabu tunanin me kikeyi haka mai zurfi har mun iso dandali baki sani ba? Na lura jefa ƙafafuwanki kawai kike yi" Cewar Daso wacce ta kafeni da idanu, Yaya Hamma shima ido ya zubamun, suna sauraren abinda bakina zai furta da sunan amsa. Iska na jawo daga huhuna na furzar kana nace. Tunanin rayuwa kawai nake yi Daso. Ai baka isa ka raba zuchiya da tunani, ko da ayyane_ayyane ba" Na ja bakina na tsuke. Na kura maa wutar karar dake ci bal_bal a tsakiyan dandalin ido, wajen yayi haske sosai ina iya hango kwalliyar mata da maza. Wutar nake kallo yanda take tartsatsi. Amman abinda zuchiyata take ciki yafi ƙarfin tartsatsin wutarnan, jin zafi nake yi daya wuce doka da oda. Hannuna Daso ta kama muka nemi wani benci da babu kowa muka zazzauna. Ƴan berorin ƴan mata sai wasannin gaɗa da waƙe_waƙen su na fulani suke yi. Samari sun kewayesu sai tafi da ɗaga sandunansu suke yi. "Kinga dandalinmu ko Jabu?, Allah yasa wasannin al'adunmu sun burgeki?" Cewar Yaya Hamma wanda yake zaune kusa dani. Murmushi kawai nayi mishi na sauke kayina ƙasa ina kallon yatsun ƙafata. "Jabu tunanin menene ya bujuro miki duk ya sauya kamanninki? Kinga lafiya abun tattalawace ga duk wani rayayye. Me zai hana ki tausaya mana ki dena wannan tunanin ko dan lafiyarki da farin cikin masu son ganinki cikin ƙoshin lafiya?" Kallonshi nayi na mai murmushi idanuna cike da ruwan hawaye. Shima murmushin ya bini dashi, kafin ince wani abun sai ga wani matashi ya ƙaraso gabanmu da sandarshi rataye bisa kafaɗunshi. "Hamma in babu damuwa inaso ka bani dama mu zanta da Daso. Na jima ina bibiyarta domin ta bani damar ko sauraren abunda ke tafe dani taji amman ta ƙi ya" Yaya Hamma ya dubi wannan matashin, ya dubi Daso wacce ta turɓune fuskarta kamar bata dariya. "To jeka zata zo yanzu. Kuma ni Hamma na baka damar zuwa zance wajen Daso Manga daga yau kuma yanzu. Daso tashi kije Manga zai yi magana dake" Nasan ganin rashin wasa gami da murtukewar fuskane yasa ta bishi ba dan ranta ya so hakan ba. Tafiyarta ke da wuya Yaya Hamma ya ce. "Bani labarin abinda yake damun zuchiyarki. Nayi miki alƙawarin magance miki matsalar duk girmanta" A'a Yaya Hamma babu komai. Ni dai inaso gobe zan je garin Kano. Amman nayi maka alƙawarin kwana biyu rak zanyi zan dawo." Da sauri ya kalleni har tsoron da yake son ɓoyewa ya kasa ɓoyuwa. "Kano kuma, ba dai wajen tsohon mijinki kike son zuwa ba, ko ganin yaranki ba? Kinsan yin hakan a wannan halin da kike ciku ka iya fama miki ciwon dake zuchiyarki" Da sauri na katseshi da cewa. Ko ɗaya ba abinda zai kaini Kano ba kenan. Akwai wani shiri da nake son in yi ne a can Kanon. In abun ya tabbata kaine mutum na biyu da zan faɗa ma bayan Daso" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace. "Au ashe Daso ta fini matsayi a wajenki? Sai ta sani kafin ma in sani ko. Nagode" Yanda ya turɓune ƴar kyakkyawar fuskarshi sai ya bani dariya ainun. Ba haka nake nufi ba. Sabida ita ɗakunmu ɗaya da'itane. Amman kana da matsayi a wajena gaya. Ko tafiyar nan da zanyi gobe babu wanda na sanarma sai kai. Sai mun koma gida zan sanarma da Yafendo" Daɗi yaji sosai, sai kuma naga damuwa ta maye gurbin daɗin. "Allah yasa ba ƙauyenmu bane ya isheki kike son komawa maraya ba, sai da muka shaƙu dake kike son ki gudu ki barmu da kewa." Daso ce ta dawo ta zauna jagwab a gefena tana rishin kuka. "Ni Yaya Hamma bana son Manga. Bazan iya rayuwar aure da abokin Chubaɗo ba, gani zanyi kamar naci amanar Chubaɗo ne. Gashi kai kace ka bashi izinin zuwa zance, kuma kab garinnan waye baisan zafin kishin matar Manga ba. Ni ban shirya jefa rayuwata a cikin haɗari ba gaskiya " Dubanta yayi ranshi a bace, ko me ya tuna oho sai ya shiga aikin rarrashinta gami da yi mata nasiha. Mijintane dai ta rasashi har abada, ya zame mata dole yin sabon aure ko ba dan sha'awa ba ko dan tsira da mutunci. Ya ɗaura da cewa. "Kuma kinsan Baba ba zuba ido zaiyi ya barki kita zama a gabanshi babu aure ba ko. Lokacin da zai matsa miki da fito da miji nake jiye miki, dan in baki fitarba al'ada zata haɗaki aure da wani ɗan uwanki ko kina son hakan, ko bakya so. Ni abinda nake jiye miki kenan. Sannan Manga kab Rugar nan ansan mutumin kirki ne, gashi da yawan shanu, kuma jarumine sosai. Ko wacce bafulatana burinta auren jarumin namiji." Zaman dandalin dai haka muka ƙareshi babu armashi, Yaya Hamma ya mayar damu gida. Muna shiga a daren na sanar ma Yafendo inaso zanje Kano in Allah ya kaimu gobe, kwana biyu zanyi. Sai da ta ɗanyi jim kamar ba zata yarda ba, kamar tana son tambayata Allah ya soni bata tambayeni ba, sai cewa tayi dani. "Allah ya kaimu goben cikin rayayyu, sai ki shirya da wuri tafiyace mai nisan gaske" Da tunanin tafiyar na kwana a raina harma da mafarkin wai naje amman ban samu Uwani ba sai Hafizu mijinta. Washe gari tun asussuba nayi wanka. Ina yin sallah na fito da ƴar jakata ta hannu da kuɗaɗena a ciki. Kaya ko kala ɗaya ban ɗauka ba, nayi musu sallama akan zan biya wajen Dada da Boɗdo mu yi sallama. Daso ce ta fito domin yi mun rakiya. Muna fitowa muka ci karo da Yaya Hamma a zaune a bakin wata bishiyar darbejiya yana kallon ƙofar gida yaga yaushe zamu fito. Ba Daso ba ni kaina nayi mamakin ganinshi a wajen. Dan sai da nayi turus. Tasowa yayi ya nufo inda muke. "Yaya Hamma kaine da sassafe haka