← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 313

Sashe 95

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ur evidence via 07087865788 [6/29, 9:05 PM] Khaleesat Haiydar💖: Badiyya ta yi wani tsalle ta finciko kwalar rigar Haseenah ta ja ta zuwa cikin parlon tana huci ta cire gyalen jikinta da handbag tayi cilli da su cikin daga murya tace "Fito min da gold dina kar in maki shegen duka, yau karyar ki ta kare kuma tunda har Allah yayi na shigo gidan nan" Zaliha ta riko Badiyya da sauri tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una meye haka Badiyyah? Dama abinda yasa kika dage mu zo kenan, dama abinda kika shirya kenan salon ki sa Haseenah ta fara min wani gani gani, ni wllh da na san abinda za ki zo kiyi kenan bazan yarda mu taho tare ba, meye haka don Allah" Duk da tashin hankalin ganin Badiyya da Haseenah ta shiga a lokacin ko da wasa bata yarda ta nuna hakan a fuska ba, sai wani dakewa da tayi tana kallon wani wajen daban, Badiyya na huci tace "Zaliha kin san tun yaushe nake bin matar nan ta ta bani kayana amma ta maida ni er iska er wahala? To wallahi ko ta fito min da gold din nan yau ko kuma in nakada mata shegen duka yanda mijinta bazai ganeta ba idan ya dawo, haka akwai daga abun arzki? Tana da gado na ne ko kuma akwai bashi ne tsakaninmu? Har kofar gidan nan na zo ranan mai gadi yace ba kowa a gidan kuma jikina ya bani tana ciki kilan Maheer ne kawai baya nan, sannan in dai na kirata sai in ji waya a kashe, duk sanda na ci sa'ar samunta kuma sai taki daga kiran, kin ga alamar rashin gaskiya kenan ko? to wallahi bazan yarda ba tunda ba uwarta ta min hustling gold din ba, don haka a yau ta bani kudina ko gold, idan ba haka ba duk abinda nayi mata ita ta ja ma kanta" Haseenah ta wani kyabe baki tace "To cikani in dauko waya in kira mai siyan gold din yanzu a gabanki, idan ya kama in hada ku ma sai ki amshi number sa kawai" Cikin daga murya Badiyya na jijjigata tace "Ina ruwana da me siyan gold da za ki hadamu? Saninsa nayi ko meye hadina da shi? kawai abinda na sani shine a bani gold dina ko kuma kudi, idan ba haka ba hukuma ta rabamu" Zaliha ta rike hannun Badiyya tace "Don Allah kiyi hakuri ki saketa ta dauko wayar tukun Badiyya, kin fi kowa sanin halin Haseenah fa, wllh Haseenah bazata cuce ki ba...." Da kyar Zaliha tayi convincing Badiyya ta sake Haseenah tana huci, Haseenah ta juya ta nufi dakinta, da farko niyya tayi ta kulle dakin da makulli tayi zamanta a ciki idan sun gaji da jiranta su tafi, wata zuciyar tace kai in dai Badiyyah ce sai ta iya zama har magariba a gidan in kuma hakan ya faru Maheer zai iya dawowa ya sameta, ta san tsaf Badiyyah zata iya mata sharri tace ita ce ma tace ta dau gold din, ita kam tsoron Badiyya take... Haseenah ta dau wayarta tana zaga dakin tana tunanin yanda zata yi, nan da nan idea ya zo mata tayi dialing number wani tsohon saurayinta da sauri ta shige bandaki ta kulle, babu bata lokaci ya daga yace "A'a Big gal an tuno da ni kenan yau" Haseenah tace "Wani big girl Biliya ina cikin tashin hankali, na kiraka ne ka taimaka min" Yace "To faa, kar ki ji komai Big gal fadi abinda ke tafe da ke kanki tsaye...." Cikin minti daya biyu ta gama yi masa bayanin duk abinda ke faruwa tsakaninta da Badiyyah sannan ta sanar masa plan din da take so su yi tare da shi, yace "Ba ki da case, ina jiran kiran naki" Katse wayar tayi ta fito daki da sauri, a bakin kofa suka kusa cin karo da Badiyya zata shigo dakin, Badiyya na mata wani kallo tace "Dauko wayar ce kusan minti biyar??" A takaice Haseenah tace "Aa Malama ki saurara min, mijina ne ya kirani na tsaya nayi attending masa, kuma ni kin ban mamaki da har za ki bar Zaliha ta ji tsakaninmu, na zata abotanmu ya wuce haka da ke" Bata tsaya ta saurari Badiyya ba ta fito parlor ta fara dialing number Bilyah tana tsaye, Badiyya ta karaso parlon tace "To Zalihar uwata ce ita da zan ji tsoron gaya mata abinda ke tsakaninmu da ke, da kin bani Gold dina ta yaya ma Zaliha zata ji kanmu har za ki ce na baki mamaki da Zaliha ta ji kanmu??" Haseenah ta kasa cewa komai jin abinda Badiyyah ke cewa, Zaliha dake kallonta tace "Ohh gani bare ko Haseenah? To ai shikenan bari inyi tafiyata" Haseenah ta rikota tace "Aa Zaliha ba haka nake nufi ba, ki tsaya ayi komai gabanki ki zama shaida" Har kiran da Haseenah take yi ya katse Bilya bai dauka ba, Badiyya ta fara girgije girgije tace "Heheee, let it not be what i am thinking Haseenah, don wllh wllh bazan yarda ba, ko da uban wa kike yawo sai kin bani Gold dina ko kudina" Haseenah ta sake kira nan ma bai daga ba, hakan kuma duk yana daga cikin plan din nasu, sai da ta kirasa sau uku sannan ya daga yace "Ke wai ya zaki ta damuna kullum da kira kamar wanda zai gudu ne?? Why are u disturbing me plss sai kace bamu saba harka da ke ba" Haseenah tace "Ni dai ka dawo kasar ko baka dawo ba?" Yace "Ban dawo ba, nace maki ina dawowa za a bada kudin ko, kina abu sai kace ban san ki ba baki san ni ba" Haseenah tace "Me shi ne ta takurani wllh, tana ga kamar na cinye mata kudi ko wani abu..." Bilya yace "Ita da aka samu za a siya stuff din nata babu reciept, wa ya sani ma ko sato sa tayi za mu yi taking risk mu siya saboda ke shine kuma zata yi ta takura mutane, wllh ko wa zata kai ma gold din nan bazai siya babu reciept ba, sannan ba pure gold bane wllh, kinsan gold din step by step ne to nata karami ne" Zaliha ta zaro ido jin abinda Bilya ke cewa, Haseenah tace "Kai dai babu ruwanka da wannan kudinmu muka sani kawai, nawa ne kudin ma kace?" Yace "Sau nawa zan ce maki miliyan daya da rabi za a siya, kawai account zaki ajiye ina shigowa kasar inyi transfer" yana fadin haka ya katse wayar, Badiyya da tayi mitsi mitsi da ido tace "Kan uba, shi gold din da kika ce min ya kusa miliyan biyar ne naji ake cewa miliyan daya da rabi, ni za a cuta??" Haseenah na kallonta da kyau tace "Ke bari kiji in gaya maki Badiyyah, an fa daina siyan Gold babu reciept a garin nan, wannan ma alfarma kawai ya mana saboda ni, kuma ni kudina na yin har wata daya biyu a wajensa, ko kwandala bai taba cinye min ba" Badiyyah ta girgiza kai tace "Inaaaa, bazai yiwu ba gwara kawai a bani Gold din na fasa siyarwa wllhi tallahi, in ya kama ma sai in sa abina inyi kwalliya kawai" Haseenah tace "Toh sai mu jira ya dawo kasar, ina jin Umra ya tafi, wannan wani irin rayuwa ne, Cousin dinki ya daura min pressure, tsinanniyar yarinyar da aka kawo min gida ta daura min pressure, kema yanzu ga shi kin zo da naki, ke da ya kamata inji dadi ta wajenki, wai ya ake son inyi ne??" Badiyya ta zaro ido tace "Ita Mayraahn kika bari take daura maki pressure?" Kamar jira Haseenah take ta fashe da kuka amma ba hawaye tace "Badiyya da za a bani wuka ina jin babu abinda zai hanani kashe yarinyar nan in huta, ban taɓa jin tsanar mutum kamar yanda na tsaneta ba, ki tambayi Zaliha ko da ta kirani dazu ai kuka nake saboda abun duniya ya isheni" Zaliha tace "Kwarai kuwa, kuma na gaya ma Badiyyar haka amma da yake bata da mutunci ji abinda ta zo tayi maki" Badiyya ta nemi waje ta zauna tace "To ai ni na zata duk zance Zaliha ke min, ban san da gaske bane, wai sai kika yi shiru kika zuba mata ido Haseenah?" Haseenah ta zauna kasa tace "To bari ki ji me kankat Badiyyah, yau breakfast na tashi tun asuba nayi mana ni da shi, wallahi gari na wayewa ya kwashe ya bata kun ga sauran nan ko taɓawa ban yi ba saboda takaici, yanda kika san zai yi worshipping dinta a gidan nan haka yake yi, gashi tayi mugun raina ni bata ganina da mutunci, babu gaisuwa tsakanina da ita, sannan ko cup bata dagawa a gidan nan komai ni nake yi, kuma in nayi girki ya kwasa ya bata" Badiyyah tayi wani dariya tana tafe hannu tace "Wargi ma ai waje ya samu, da ace kin daidaici ranan da baya nan kin kama shegiya kin nakada mata shegen duka wallahi da kafafuwanta zata gudu ba sai wani yace ta tafi ba, ai ni na ma ga kokarinki da kike ta zaune da ita har yanzu under the same roof, kina fa koranta a gidan nan bata da inda zata je da ya wuce ta shiga duniya kuma, don har yanzu Hajja na kan bakanta wallahi, ko kiran Ammi sai nace ta daga take dagawa in ko na zugata nace kar ta daga to wllh baza ta daga ba, kin ga kuwa duk ranan da kika kori Mayraah bata da wajen zuwa a duniya" Haseenah ta marairaice tace "Wallahi dukan nayi niyyar mata yau naga ashe tare suka fita ina daki ina ta haukana, tun fa da ta zo bamu taɓa yini tare da ita a gidan nan ba, kullum sai taje makaranta, yau kuma naji tace bazata je ba daga baya kuma naga bata gidan kilan asibiti ya tafi da ita, kawai sun mayar da ni er iska a gidana, Babban tashin hankali na yanda kowa yasan da aure tsakaninsu yanzu, wallahi in na tuna hakan kasa bacci nake da daddare, har abinci sai in ji ya fita raina, kar wataran...." Kasa ci gaba tayi kawai sai ta fashe da matsanancin kuka, Badiyya ta
Chapter 95 · 0% Book details