Sashe 87
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ur evidence via 07087865788 [6/27, 8:07 PM] Khaleesat Haiydar💖: Usman yayi parking dai dai kofar gidan Maheer, sannan ya kalleta yace "Sae da safe" Tace "Yaya za ka kawo min jakar gobe?" Yace "Kiyi me da shi?" Tace "My handout is inside" Bai kuma cewa komai ba, ganin haka ta bude motar tace "Sae da safe" Yace "Allah ya tashe mu lafiya" Sauka tayi ta kulle masa motar sannan ta nufi gate, yana tsaye har ya ga shiganta compound din gidan kafin yayi reverse, Mayraah na tsaye bakin kofa tayi knocking a hankali ta koma gefe ta tsaya, jin shiru yasa ta sake kwankwasawa, bude kofar aka yi suka yi ido hudu da Haseenah, Haseenah tayi mata wani matsiyacin kallo tare da jan dogon tsaki ta mayar da kofar ta kulle da karfi sannan ta saka makulli, Mayraah bata san sanda ta taɓe baki ba, tayi unlocking wayarta dake hannunta tayi dialing number Maheer, yana fara ring ya daga yace "Kun dawo ne?" Tace "Ehh" yace "Ohk let me open the door for you" Daga haka ya katse wayar, sai ga shi ya fito parlor daga Bedroom, Haseenah dake zaune kan kujera ta bi sa da kallo har ya nufi kofar parlon, budewa yayi yana kallon Mayraah, sai da ta shigo parlon yace "Usman din ya tafi?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk zan baki spare key ki rike a wajenki" Haseenah dae sai girgiza kafa take tana kallon TV fuskarta babu yabo babu fallasa, Mayraah ta nufi dakinta ya bi ta da kallo yace "Ina jakar?" Tace "Ya Usman zai kawo min gobe" Yace "Ohk" Daga haka ta wuce dakinta ta kulle, Maheer ya ɗan kalli Haseenah ya zauna gefenta yace "Where is the black tea i asked you to make for me?" Bata ce masa komai ba, yace "Baby i am talking to you" bayan some seconds ta mike ta nufi kitchen ya bi ta da kallo, sae da ya ga ta shiga kitchen din sannan ya tashi ya tafi dakin Mayraah, tsaye ya ganta tana linke Hijab dinta, ya kulle kofar yayi kasa da murya yace "But why didn't u greet her Mimi?" A takaice tace "She shut the door in my face" Yayi shiru, ta gama linke Hijab dinta zata ciro kayan da zata canza taji yace "Amma da kinyi hakuri kin gaisheta..." Juyawa tayi tana kallonsa, ya ɗan shafa kansa yace "Kinga ai Aunt dinki ce Mimi and she deserves some respect" Mayraah tace "Is that why she should close the door on me? Did she think i want to be here too??" Nan da nan hawaye ya cika idonta, dai dai nan aka bude kofar dakin Maheer ya juya da sauri, Mayraah ta ajiye kayan baccin da ta ciro ta dau pad da inner wear dinta tayi shigewarta bandaki ta bar su wajen, Maheer na kallon Haseenah dake masa wani irin kallo yace "Har kin dafa shayin?" Ta watsa masa kallo daga sama har kasa ta bar bakin kofar, ya bi ta har zuwa Bedroom dinsu. Ko da Mayraah ta fito makulli ta sa ma dakin ta sa kayan baccinta ta kwanta, ko kadan bata bari abinda Haseenah tayi ya tsaya mata a rai ba cause that's not her concern for now, damuwarta yanzu dalilin da yasa Musharraf ya ki kiranta throughout today, dialing numbersa tayi, after ringing for a while ya daga, kamar yana ganinta ta hade rai tayi shiru, daga daya bangaren yace "Ya jikin ki?" Kamar zata yi kuka tace "Sae da na kira ne zaka tambaye ni?" Yayi shiru, kafin yace "I called, not reachable" tace "You didn't" yace "Yanzu dae ba an kula da ke kin samu lafiya ba?" Tace "Toh shikenan, sae da safe" Yace "Wait..." Bata katse wayar ba tayi shiru tana sauraronsa, yace "How are you feeling now?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Kin ci abinci?" Tace "Na ci" yace "Ohk, good night" shiru tayi kamar bazata ta ce masa komai ba, sae kuma a hankali tace "Zaka zo school gobe?" Yace "Yau da kika sa na zo, kin zo?" Ta marairaice tace "Ae don bni da lafiya ne, amma gobe in sha Allah zan je" Yace "Allah ya kai mu, take care of ur self" a hankali tace "Sure" Daga haka ya katse wayar ta dinga kallon screen din. Washegari kafin bakwai da rabi Mayraah ta shirya ta fice daga gidan without anybody noticing her ban da Musa mai gadi, don bata ma ga alamar masu gidan sun tashi ba, ko shayin bata tsaya ta sha ba yau, ta isa har inda zata samu adaidaita sahun da zai kai ta makaranta, takwas dot ta shiga department dinsu, ita da Hamidah da wata Coursemate dinsu Amina suna zaune class don karfe takwas din suke da lectures, amma gashi har takwas da rabi lecturer din bai shigo ba, Hamidah na kallon Mayraah tace "Wai Badiyyah bata nan ne, na ga ta daina zuwa school long ago, ga exam is fast approaching" Mayraah tace "Ni ma ban sani ba kam, kilan tana Bichi, but nasan zata dawo tayi exams ai" Shigowan lecturer din ya sa duk aka nutsu a class din, Mayraah ta bude jakarta ta fiddo littafinta da pen, paying attention to their lecturer... Karfe goma da rabi suka fito daga lecture hall din, ta fiddo wayarta a jaka ta ga miss calls har shidda, uku na Maheer, biyu na Usman sai na Dr Musharraf guda daya, ta dinga kallon calls din, kawai tayi dialing na Dr Musharraf, yana fara ring ya daga ta gaishesa a hankali, ya amsa yace "Are you done with the lectures?" Ta zaro ido tace "How did u know i am in school?" Yace "Kawai na ji kamshin turarenki gaba daya department din" Bata san sanda tayi dariya ba ba tare da ta shirya ba, Hamidah dai na zaune kan gossip chair tana kallonta, ko Mayraah bata gaya mata ba tasan tana cikin damuwa cause it's obvious a fuskarta, Musharraf yayi shiru yana sauraron dariyan nata, can a hankali yace "Ina jiran ki a office now" tace "Sir zan ɗan yi karatu ne fa yanzu" Yace "Yauwa dama ina son in tambayeki, kin canza project supervisor ne ban sani ba?" Zaro ido tayi don ita ta ma mance da batun wani project, a hankali tace "Aa ban canza ba" Yace "Ok na zata kin canza, don naga mate dinki are almost done with theirs ke kuma har yanzu kina chapter 1" Da sauri tace "Aa wllh Chapter 3 ne" Yayi murmushi yace "Uhm i see" Ta marairaice tace "Amma sir ban zo da system dina ba" Yace "In kin gama karatun ina jiranki" Daga haka ya katse wayar. A hankali Mayraah tayi knocking din kofar office dinsa wajen karfe sha daya, sae da yayi mata izinin shigowa sannan ta bude kofar ta shiga, tun da ta shigo yake kallonta, ita kuwa kallo daya tayi masa ta karasa har inda yake ta sunkuyar da kai ta gaishesa da ladabi, ya mike offering her his seat yace "Ga wannan.... Naga kamar na gabanki basu maki ba" Murmushi tayi ta zauna kujeran dake gabanta a hankali tace "Ina kwana sir" Ya koma ya zauna underneath his breath yace "Lafiya lau.... how was ur night?" Ta kallesa tace "Good" Yace "Hope u slept well?" Ta langwabar da kai a hankali tace "Ai baka kira ba" Shiru yayi yana kallonta babu ko kiftawa, bai taɓa tunanin bond dinsu zai dawo haka da Mayraah ba, don kafin faruwan issues din nan har tunani yake if she will ever change ko da sun yi aure sai gashi yanzu she talks to him openly, she expresses her feelings unlike before da yake rasa gane kanta komai kunya, komai shiru shiru, Mayraah dai sai kallonsa take jin yayi shiru, ya sakar mata murmushinsa me kyau yace "To an hana in ganki jiya, and i was sad about that" Ta sunkuyar da kanta tace "Ai saboda bani da lafiya ne shi yasa yaya yaki ya bari in fita, kawai... An ban magani na sha shine nayi bacci har yamma" Yace "Am glad u are okay now, no pains" Tace "There is, but ba kamar jiya ba" Yace "To kin sha maganin?" Tace "Ban yi breakfast ba" Da mamaki yace "Why?" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Ohk akwai abincin da Mami ta zuba min yana mota, kinsan every day in dai ina gida sai ta min breakfast kafin in fito, ni kuma bana ci, wani lokacin in ba cleaners or security...." Makullin motarsa ya dauko ya mika mata yace "Get the food, I don't even know what she prepared" Mayraah dai kallonsa kawai take, yace "Ko in je in dauko maki" tayi murmushi tace "Sir ni bazan iya cin abinci a school ba" Yace "Aa cewa za ki yi, sir ni bazan iya cin abincin gidanku ba" Mayraah ta zaro ido tace "Wallahi sir ba haka bane" zai yi magana aka yi knocking din office door din, Mayraah zata tashi yace "Is there anything wrong?" Ta girgiza masa kai, yace "To koma ki zauna" Komawa tayi ta zauna ta sunkuyar da kanta tana danna wayarta, yayi ma me knocking din izinin shigowa office din, daga bakin kofa ta tsaya bayan ta shigo a hankali tace "Good morning sir" Mayraah ta daga kai jin muryar warce ta ji sai dai bata juya ba balle ta kalleta, Dr Musharraf yace "Morning Badiyyah, how are you?" Tana makale jikin kofar tace "I am fine sir" Yace "You can come in" Ta karaso cikin office din tana tafiya kamar me tsoron taka kasa, ta tsaya ɗan nesa da table dinsa tana jujjuya textbook din hannunta tace "Sir dama plss tambaya nake son zanyi akwai abinda ban gane ba... I don't know if u will have the time...." Dr Musharraf yace "Ohk, is it pertaining to my course?" Ta gyada kai da sauri, ɗan murmushi yayi ganin kamar she looks nervous yace "Why are you tensed Badiyyah? You have all right to ask ur lecturer duk abinda baki gane ba, kawo textbook din in ga" Ta karasa har kan table din ta mika masa textbook din da ladabi, tuni fitinannen kamshinta ya baza office din, sai a sannan suka hada ido da Mayraah, Mayraah ta dauke idonta ta ci gaba