← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 313

Sashe 89

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

zama frnd dina daga yanzu, and beside i never asked for all this explanation" Kallonta kawai yake, ta kallesa suka hada ido ta fashe da dariya, daure fuska yayi nan da nan ta kama kanta, imagine wai yau ya Usman ne ke taking time trying to explain to her what she neva asked for, ita bata ma san ya iya dogon bayani ba sae yau, wani dariya ya kara zuwa mata ba tare da ta shirya ba, shi dae driving dinsa kawai yake. Mayraah na shiga compound bayan Usman ya ajiyeta taga Maheer bai dawo aiki ba, kawai ta karasa ta zauna kan wani kujera da ta gani a parking space don bata jin zata shiga gidan, tana ta zaune a wajen har kusan karfe shidda sai gashi ya dawo, yana parking ya sauko daga motar, ta mike tana kallonsa tace "Sannu da dawowa" Da mamaki yace "Bata bude maki kofar bane yau ma?" Mayraah ta girgiza kai tace "Aa kawai iska nake sha a nan" Ya mika mata ledan hannunsa ta amsa, sannan ya nufi entrance din gidan tana biye da shi a baya, yana bude kofar parlon hayaki me kama da na turaren wuta da ya turnike ko ina na parlon ya ce masu salamu alaikum, Mayraah na ganin haka ta juya da sauri ta bar entrance din parlon, Ammi na saka turaren wuta amma wnn kam kamar ba turaren wuta bane don wani irin kamshi kamar na yan bori yake, Maheer ya bi ta da sauri yace "Hope u didn't inhale much?" Ta girgiza masa kai still walking away from the vicinity, parking space din ta nufa, shi dai yana biye da ita, ta zauna kan kujera ya duka yana kallonta yace "Kiyi hakuri ki ɗan zauna nan har ya fita, bata san baki so ba" Mayraah dai bata ce komai ba, ya mike ya koma cikin gidan, yana shiga parlon ya fara kwala ma Haseenah kira, ta fito daga kitchen sanye da wani atamfa tayi daurin ture kaga tsiya ga make up a fuskarta ta nufesa ta rungumesa tana taunar gum tace "Oyoyo Baby, sannu da dawowa my husband" Yana yamutse fuska yace "Wannan hayakin meye kika cika a gidan nan Haseenah?" Ta wara ido tace "Turaren wuta mana" Yace "Aa wannan ba turaren wuta bane gaskiya, kuma ba nace maki Mimi is Asthmatic ba? Because of this she can't come inside now" Haseenah ta hade rai tace "And so what? Saboda Mimi kana nufin bazan sa turare gida na yayi kamshi ba kenan?" Yace "Madam!! Ammi tana sa turaren wuta amma ba me hayaki irin wannan kamar anyi gobara ba, beside wannan wani awful smell yake fitarwa unlike wanda Ammi ke using..." Haseenah ta juya ido tace "Toh ni kalan nawa turaren wutan kenan, take it or leave it Maheer" Tana fadin haka ta bar sa tsaye a wajen ta nufi daki, kasa ce mata komai yayi, can ya juya ya fita ya koma wajen Mayraah....
Chapter 89 · 0% Book details