Sashe 191
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ur evidence via 3276052019 Mayraah tayi knocking din office din a hankali ta koma gefe ta tsaya, jin ba a amsa ba bayan some seconds ta sake knocking, Sai da tayi knocking sau uku sannan taji ya bada izinin shigowa, ta bude kofar a hankali suna hada ido tun kan ta saka kafarta cikin office din yayi saurin cewa "I am occupied Madam, leave and come back tomorrow 8am prompt" yana fadin haka ya ci gaba da sipping juice dake hannunsa yana operating laptop, kallonsa ta dinga yi babu ko kiftawa, a karo na farko tun barin ta gida Musharraf ya fado mata a rai, don last day da ta je kai masa project work dinta a office dinsa da yanda yace ta tafi ta dawo 5:30pm prompt ne ya shiga rotating a kanta, ganin bata bar bakin kofar ba ya daga kai ya sake kallonta ya hade rai yace "Are you daft?" Wani tsinannen kallo ta jefa masa, wanda hakan yasa ya ajiye juice din hannunsa ba tare da yasan yayi hakan ba cause he was taken aback by her reaction, tuni ta kulle kofar office din ta bar wajen fuskarta daure, har ta sauka second floor ta kasa kauda tunanin Musharraf da ya mamaye ranta wanda hakan yasa kuzarinta ya ragu, office din Dr Khalil tayi knocking ta shiga bayan yayi mata izini, da mamaki yake kallonta ya mike tsaye yace "What happened again?" Ta kirkiri murmushi tace "No, na samesa yana cin abinci ne, shine yace in bari gobe karfe takwas na safe idan Allah ya kai mu" Dr Khalil yace "Are you sure Mayraah?" Ta gyada masa kai tace "Da gaske fa, yace gobe da safe in sha Allah" Dr Khalil ya koma ya zauna yace "Ohk" Daukar handbag dinta tayi tana kallonsa tace "Na gaji, ina son in tafi" Yace "Toh ki gaida su Ummi, inna dai na gidan Baffan su Mimi, cousin din Zainab zata yi aure next week" Tayi murmushi tace "Allah sarki, pls idan twins sun tashi kace masu sai mun sake haduwa i will miss them" Yace "To zan gaya masu" juyawa tayi ta fita daga office din ta sauka downstairs, sallama tayi da Nurse Hafsat sannan ta fita haraban asibitin, zaunawa tayi karkashin wani bishiya ta ciro wayarta a jaka, a hankali ta fara dialing number Musharraf da ake samunsa not his private line dake kulle, tafi minti uku tana kallon numbers din ta runtse ido kawai ta goge ta maida wayar cikin jakarta ta mike walking slowly ta fita daga asibitin, tana taran adaidaita sahu ta gaya masa inda zai kai ta sannan ta shiga, after many minutes ride yayi parking inda tace ya tsaya sannan tace "Don Allah ka jira ni zan amshi sako ne sai ka kai ni wani wajen daban" Yace "Toh" Karasawa tayi ta shiga shagon Aminu, gaisawa suka yi da fara'a yace "Ya makarantar Hajiya" Tace "Alhamdulillah ya kasuwa?" Yace "Lafiya lau wallahi, kin ga na kwana biyu ma ban shiga Sulejan ba ni" Tace "Allah sarki, don Allah SIM card nake son zan kara siya" Yace "Toh wani network kenan?" Tace "Ko wanne, sai ka hada min da katin dubu daya" Dauko mata yayi ta ciro dubu biyar a jakanta ta basa tace "Ka saka katin waya da sauran canjin" Godiya ya mata sosai bayan ya amsa, tayi murmushi ta yi masa sallama ta koma cikin adaidaita sahun dake jiranta. Mayraah na sauka kofar gidan Ummi bayan ta ba mai adaidaita sahun kudinsa ta shiga gidan, Ahmad na zaune compound making a phone call, kawai ta ɗan masa murmushi not wanting to distract him ya bi ta da ido har ta shiga gidan, karime kadai ce a gidan bayan sun gaisa karime tace "Ai ko awa daya yan gidan basu yi da fita ba in gaya maki, kinsan aminiyar Hajiya ke aurar da er ta, to can Hajiya ta tafi da Mimi, gobe asabar ne daurin aure ranan lahadi kuma ayi taron biki, ina jin ranan lahadin za su dawo, Hassan da Hussaini kuma sun je gidan baffansu tare da Inna tun jiya, Baffan zai aurar da er sa satin nan da za mu shiga" Mayraah dake zaune parlon tana danna wayarta tace "Allah sarki" Karime tace "Ai gobe baki da aiki ko?" Mayraah ta daga kai ta kalleta ta ɗan yi murmushi, Karime tace "Sai mu je gidan bikin kawai tare, Hajiya ta ce in je gobe, ina jin bata san za ki dawo ba tunda mun san can Suleja kike weekend dinki" Mayraah tace "Zan je aiki goben in sha Allah" ta fada haka ne ba don tana da intention din zuwa asibitin gobe ba sai don kawai bata son bin karime gidan bikin, Karime tace "Allah sarki, to bari in zubo maki abinci" Daga haka ta mike ta shiga kitchen Mayraah ta bi ta da kallo, Karime zata yi shekara kusan arba'in da biyu, kuma ta fi shekara bakwai tare da Ummi sai dai taje ganin yaranta da iyayenta a kauyensu ta dawo don ta zama kamar wata er uwar Ummi, Karime na kawo mata abincin ta ajiye Mayraah tace "Nagode sosai" Karime tace "Kin ga da daddare ba sai mun yi girki ba, tun da akwai burodi kawai soya kwai za mu yi mu sha shayi don shi yallabai dama shayi yake sha da daddare" Mayraah dai ta ɗan yi murmushi ta dau plate din abincin ta fara ci, sama sama take biye karime da ta cikata da hira a parlon don duk ta kagu ta wuce daki ta saka sabon sim card da ta siyo, kiran la'asar ya sa Mayraah ta mike ta tafi kai plate din kitchen ta wanke sannan ta dawo ta tarar har Karime ta shiga daki ita ma zata yi sallah, Mayraah ta dau jakanta ta wuce nata dakin da take sauka a gidan, alwala tayi, bayan ta idar da sallah ta dau sabon sim din ta saka a wayarta, ganin ya hau ta loda katin, dialing din number Musharraf tayi da sabon Sim card din, tana ji ya fara ring sai da gabanta ya fadi, ta daura goshinta saman knees dinta har sannan zuciyarta na bugawa tana jiran ya daga, sai da ya kusa katsewa taji ya daga, shiru tayi shi ma yayi shiru bai ce komai ba, after few seconds taji ya katse wayar, murmushi tayi don tasan dama bazai ce komai ba in dai bai san number ba haka yake, sake dialing number tayi duk da a ranta tasan ba lallai ya sake dagawa ba ai kam har ya gama ringing bai daga ba, kawai ta kashe sim card din cikin wayar ta ajiye wayar ta kwanta. Mama Ladi ce zaune gefen Hajja dake jingine da bango tana zaune kan shimfidar da aka mata a parlonta wajen karfe biyar na yamma, Mama Ladi na washe baki tace "Alhamdulillah jiki ai ya fara kyau, gashi har kin kusa shanye shayin, tun jiya fargabana ta ina zan fara jinyarki idan shanyewar barin jiki ya sameki, wallahi hankalina yayi matukar tashi bazan boye ma kowa ba" Ammi dai na zaune parlon tana kallonsu, Aunty Mariya kuma na kitchen tana dama ma Hajja kunu, Mama Ladi ta kalli Ammi tace "Ke fa nace maki ki tashi ki tafi gida kar Mamuda ya ga rashin hankalinmu ya sake tabbatar da mu kananun mutane ne, tun shekaranjiya fa kike nan ko mutuwa aka yi ya ci ace kin koma dakinki barin ma ga Hajja har ta fara tashi zaune ga kuma shayi tana sha, nima zuwa anjima in sha Allahu zan taho sai Mariya ta zauna tayi jinyar Hajjan da me laulayin can, don gaskiya bazan iya jure ƙarnin aman da Badiyyah take kirba mana ba, in tayi aman ƙarnin har nan malam, to a kan me, ɗa ba ɗan sunna ba ta dinga cutar mu da ƙarni, bazan iya ba wallahi" A karo na farko Hajja ta bude baki a hankali tana girgiza kai tace "A fitar min da ita daga gidana dama jira nake in gama shan shayin inyi magana, a tafi da ita duk inda za aje da ita, in ko ba haka ba in bi Mariya mu tafi kaduna ta sauke ni gidan yahanasu" Tana magana ne hawaye na sauka idonta, Mama Ladi ta saki baki tana kallon Hajja da mamaki, can tace "A fita da ita a kai ta ina Hajja? Ko dai baki gane wa nake nufi ba, Badiyyah fa nake magana, Badiyya guda fa taki" Hajja na gyada kai wani bakin ciki na kara tokare mata makogwaro tace "Ita Ladi, bazata kwanar min a gida yau ba ta tafi duk inda za ta, ni ma kaduna zan tafi gun yahanasu" Ammi tayi kasa da murya tace "To ina za ta Hajja? Da dai kin yi...." Dakatar da ita Hajja tayi cikin rawan murya tace "Wallahi tallahi bazan kwana da Badiyyah gidan nan ba yau kun ji har na rantse, dama ina ta addu'ar in samu karfin yin magana tun jiya Allah bai bani iko ba sai yanzu, to Allah ya isa tsakanina da ita, Allah ya isa, Allah ya isa wannan abun gorin da ta ja min har karshen rayuwata, duk soyayyar da na nuna mata saboda tausayin maraicinta duk jan ta jiki da nayi don kawar mata da maraici a rayuwarta sakayyar da Badiyyah zata min kenan, da haka zata saka min? ta cuce ni, ta ja min abun kunya, ta ja min abun magana, ta ja min abin gorin da har in koma ga mahaliccina...." Kasa ci gaba tayi saboda tarin da ta fara kamar zata shide tana gwalo ido, Mama Ladi tayi saurin mikewa tana kallon Ammi tace "Kin ga tun da tace a fitar mata da ita daga gidan nan bazata kwanar mata ba to gaskiya ki shiga ki temaka mata ta hada kayanta a akwati a dora ta motar Bichi ta tafi wajen dangin ubanta, haka kawai bakin cikinta bazai kashe min yayata ba in shiga uku, maza a fita da ita ba ruwana, ko kuma ni in je in hado mata tsummokaran nata da kaina" Hajja na kuka tana tari tace "Ku fita da ita ko ni in tafi, ku fitar min da ita nace" Mama Ladi ta nufi dakin Badiyyah da gudu tana