← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 199 OF 313

Sashe 199

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Mayraah is 500 via 3276052019 Fcmb Hauwa bello jidda

Ur evidence via 07087865788

INA MATA MASU AJI, BA ‘YAN RAKIYAR MATA NAKE NEMA BA. SHIN KINA DA LABARIN COMPANY DINNAN NA APHRODISIAC MA’ANA KAYAN MATA WATO *HONEYDROPS* DA KE GARIN *SOKOTO* SUNA DA INGANTATTUN KAYA DA BA SU DA NA BIYU WANDA SUKE DAWO MIKI DA MARTABARKI TA MACE KI DAWO TAMKAR BUDURWA ‘YAR SWEET 16, SUNA DA ZAFAFAN KAYA DA SUKA HA’DA DA *INFECTION FLUSHERS, BREAST FIRMING AND ENLARGEMENT PRODUCTS, HIPS AND BUTTS PRODUCTS, DIFFERENT TYPES OF WETNERS, VARIETIES OF SWEETENERS, VIRGINITY BACK PRODUCTS WATO TIGHTENERS *(MA’ANA AKWAI KALOLIN KAYAN QARIN NI’IMA, QARIN DADI, QARIN DANDANO DA KUMA MATSI NA BAN MAMAKI), SANNAN KAYANMU NA DA HADIN SINADARAN DA KE SAKA MALLAKA DA SOYAYYA A ZUCIYAR MIJI*

KAYANMU SUN HA’DA

*INFECTION FLUSHER*
*ORIGINAL SABAYA*
*ECHOES OF FOREVER*
*MOWA’S SECRET*
*HER ROYAL HIGHNESS*
*ETERNAL FLAME*
*SUGAR QUEEN* DA SAURANSU. KI HANZARTA SAVING LAMBATA KI KUMA YI MIN MAGANA DON SIYE KO SARI KO KUMA KASANCEWA CIKIN MASU SA’AR SAMUN KAYANMU A KYAUTA YAYIN DA MUKA YI GIVEAWAY. ZA A IYA TUNTUBARMU A LAMBOBI KAMAR HAKA 08167888934 KO KUMA 07026039714. KO A SHIGA LINK DOMIN MAGANA DA MU KAI TSAYE wa.me/+23481678888934

*MUNA MARABA DA KU, MUNA GARIN SOKOTO MUNA AIKE KOWANI GARI KOWACCE QASA CIKIN AMINCI*
Bayan wani ɗan lokaci Mayraah ta dawo bakin gate din, tayi gathering courage duk da yanda gabanta ke faduwa tace "Sorry... brother na yace i shouldn't open the gate till he comes" shiru duk ta ji sun yi bayan ta gaya masu haka, sai kuma taji mutumin yace "Ki bada number brother din naki" Mayraah tayi tsuru tsuru jin abinda yace, sake maimaita maganar yayi, cike da karfin hali tace "Aa ni bazan bada ba sai na tambayesa tukunna" Mutumin yace "Kirasa yanzu kice we are requesting for his number, call him immediately" Komawa cikin gidan Mayraah tayi ta sake kiran number Dr Khalil, yana fara ring ya daga yace "I am on my way now kar ki bude gate din" Kamar zata yi kuka tace "Wai sun ce in basu numberka kuma" Ya ɗan yi shiru sai kuma yace "Number na?? ohk ok basu kawai, but do not open the gate, just call out the number for them" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, yace "Kin ji me nace?" A hankali tace "Toh" Komawa gate din tayi bayan ya katse wayar, cikin karfin hali tace "Yace in baku number din, zan kira maku digit din yanzu" Mutumin dake bata amsa yace "Ohk, do so now" Kiran numbers din khalil ta shiga yi har ta gama, mutumin yace "Good" Ji tayi kamar sun bar bakin gate din, ita dai sai zare ido take har taji tafiyar motarsu, duk da haka bata yarda ta bude gate din ba ta koma cikin gidan duk hankalinta a tashe, gaba daya ta rasa wani tunani ma zata yi, tana ta zaune cikin fargaba har wayarta ya fara ring wajen karfe biyar da wani abu taga Dr Khalil ne ke kiranta, dagawa tayi ta kai kunne da sauri, yace "Fito ki bude gate din" Tace "Ka zo ne?" Yace "Eh ina waje" mikewa tayi dama har sannan bata cire hijab din jikinta ba ta fita zuwa bakin gate din, bugun zuciyarta ya tsanata cike da karfin hali ta makale jikin gate din tace "Ka kadai ne?" Yace "Ni kadai ne mana Mayraah" a hankali ta bude gate din with throbbing heart, tsaye ta gansa bakin gate din, ta marairaice masa tace "Did they call u pls?" Yace "Yea they called, but it's not even something serious" Tace "Toh me suka zo yi? Me ya faru? Did commit any offense?" Yace "Za mu je station din yanzu, kawai tambayoyi za su maki...." Ta fashe da kuka sosai tace "Toh ba sai mutum yayi laifi ba ake kai sa station, ni me nayi? Don Allah kar ka boye min ka gaya min" Yace "Nace maki it's not something serious Mayraah, yanxu haka daga station din nake, kawai suna daukan statement dinki zan dawo da ke gida, kar ki wani daga hankalinki" Cikin kuka tace "Statement of what? What wrong have i committed?" Yace "Na fa ce ki kwantar da hankalinki, i am with you, yanzu ba daga Abuja nake ba saboda ke?" Share idonta tayi tana kallonsa, yace "Dauko wayarki mu tafi lokaci na wucewa" A hankali ta juya ta koma cikin gidan, wayarta ta dauko da handbag dinta ta fito, a cikin motarsa ta samesa yana jiranta, bayan ta kulle gidan ta tafi ta bude front seat ta shiga motar, kana ganinta kasan duk jikinta yayi sanyi sosai kuma a tsorace take, bayan sun bar layin ya kwantar da murya yace "Pls calm down Mayraah, kema kinsan bazan bari ayi harming dinki ba, beside i told u it's not something serious, u need not to worry kar ki je jininki yayi kasa" Ta fashe da kuka tace "But i want to know what i did, ina son sanin menene ya sa suka zo za su tafi da ni, wani laifin nayi? I know kasani tunda kaje station din, definitely u are aware, you are just hiding it from me, don girman Allah ka gaya min menene ko zan samu relieve" Dr Khalil ya ɗan kalleta, sai kuma yace "Ohk bazan boye maki ba, kinsan me ke faruwa?" Ta girgiza masa kai da sauri zuciyarta na bugawa, ya ɗan yi shiru sai yace "Kinsan ko wani society or rather community, da irin ka'idarsu ko kuma ince da irin way of life dinsu, da yanda suka ba al'adarsu da addinin su muhimmanci, right??" Shiru tayi tana kallonsa waiting for him to go straight to the point, ya sauke ajiyar zuciya yace "To kin dai ga garin nan da kike ciki yawanci majority dinsu musulmai ne, sannan akwai Hausawa babu laifi, so the community are against gidan da kika kama kina zaune ke kadai kina zaman kanki don suna da yara kuma suna duba tarbiyar yaransu suna tsoron kada yaransu suyi tunanin hakan abu ne me kyau mace ta kama babban gida irin wannan tayi zamanta, sannan sunce ke kince kina karatu amma sun gano ba karatu kike ma a garin Abujan ba, iyaka idan kinje kinyi abinda za ki yi a Abuja sai ki dawo nan ki bude gida ki shiga bayan kwana biyu ki sake komawa cikin Abuja, sannan a complain dinsu sun ce akwai saurayin da ma yake zuwa ya sameki a nan din" Sake baki Mayraah tayi tana kallonsa har zuwa sanda ya dasa aya, she was so shock and speechless, yace "To ban san ko bayan zuwan da nayi last week ko akwai wani wanda ke zuwa wajenki ba" Mayraah bata san sanda ta fashe da kuka ba tace "Allah ya saka min, wallahi bazan yafe masu ba, tunda na dawo nan babu wanda ya taɓa zuwa wajena sai kai, bazan taɓa yafe wannan kazafin da suka min ba" Dr Khalil ya langwabar da kansa yace "Kinga abinda nake gaya maki ai ko, mutuncin ya mace gaban iyayenta, in ko ba gaban iyayenta ba to gidan mijinta, in dai a arewa ne duk inda za ki je to wallahi kallon da za a maki kenan baza ki taɓa canza su daga maki kallon nan ba, a takaice gani suke sharholiyarki kike shigowa kiyi a Abuja sai ki dawo nan Suleja ki fakee, let me tell u something.... kiwon mutane ake yanzu ba fa dabba ba, duk footstep dinki a kan idon mutane yake" Mayraah dai ta kasa cewa komai sai kukan bakin ciki da takaici take, har suka iso garin Abuja ta kasa daina kukan da take har ya ma daina lallashinta, wani station taga sun zo, bayan yayi parking a waje yana kallonta yace "Kiyi hakuri in sha Allah komai ya zo karshe daga yau, wipe off ur tears and trust me I will be by ur side" A hankali ta goge idonta tana kallonsa cikin rawan murya tace "Toh yanzu me zan ce masu idan mun shiga?" Yace "Kar ki damu, na riga na masu bayanin komai, iyaka Statement dinki za a dauka, shikenan" Daga haka ya sauka daga motar ita ma ta sauka har lkcn hawaye ya ki tsaya mata, she felt so hurt da irin kallon da mutane suke mata, ga Ahmad, Zainab, and now sulejan da take, calmly yace "Na fa ce ki daina wannan kukan" Ta gyada masa kai da kyar tana kara goge idonta, ya nufi cikin station din tana biye da shi a baya. Dr Khalil ya gaisa da yan sandan cikin station din yace "Za mu iya shiga office din Dpo din?" Police officern yace "Ehh suna ciki har yanzu, You can go in...." Ya kalli Mayraah dake tsaye gefensa kamar warce tayi ma sarki karya gaba daya a tsorace take don bata taɓa shigowa police station ba, calmly yace "Mu je" Bin bayansa tayi har xuwa office din Dpo din, ya bude kofar ya fara shiga da sallama sannan ita ma ta shiga gabanta na faduwa sosai, makalewa tayi jikin kofar tana kallon wanda ke zaune kan Sofa a office din babu ko kiftawa, can ta juya a hankali ta kalli Dr khalil kamar idanuwanta za su fito, Dpo ya daure fuska yace "Kee, shigo ki kulle ma mutane office" Ji tayi kamar ta zura a guje, ta dai kulle kofar da kyar ta sunkuyar da kai, amma ta kasa karasawa ciki don gaba daya tayi shock a wajen, tuni Dr Khalil ya tafi ya zauna kan kujera, Dpo ya bata thumbs up yana gyada kai cikin jinjina yace "The runaway girl!!" Kasa daga kai tayi, cikin daga murya yace "Ya sunanki?" Da kyar ta daga kai ta kallesa cikin karfin hali tace "Mayraah" Yace "Mayraah the runaway girl.... to nemi kujera ki zauna" Ta saci kallon wanda ke zaune kan sofa din, ai tana ganin irin kallon da yake mata tayi saurin dauke kai kamar munafuka ta tafi ta zauna kan kujera ta takure waje daya, shi dae Khalil murmushi kawai yake, Dpo yace "Kin san wannan da yake zaune?" Sunkuyar da kai tayi, ya mata tsawa yace "Ke..." Cikin rawan murya tace "Yayana ne" Yace "Ya sunansa?" saboda tsoron kar ya sake mata wani tsawan cikin rawan murya tace "Ya Usman" Dpo yace "Yau kwananki nawa da barin gida?" Ta fashe da kuka ta kasa cewa komai, yace "Ba kuka nace ki min ba malama, warce ta iya tsallakawa ta bar gida ai zuciyarta ya kekashe kenan babu wani batun kuka, kwananki nawa yau da barin gida?" Cikin rawan murya tace "Kamar 3 weeks" Yace "Kuma baki da intention din komawa anytime soon ko?" Daga kai tayi tana kallonsa hawaye na sauka idonta, Dpo din yayi shiru, sai kuma ya nuna mata kujeran dake gaban table dinsa yace "Dawo nan ki zauna" Mikewa tayi tana kuka ta tafi ta zauna kan kujeran, yace "Mayraah" Ta daga kai ta kallesa hawaye na sauka idonta, yace "Abinda kika yi kin kyauta kenan? Saboda wasu unforseen circumstances sun faru that doesn't mean it is the end of life my dear, what if hannun mutanen banza kika fada? Did you know the type of era we are in now? Kinsan irin munanan cases da muke dealing da kullum a wajen nan? me yasa za ki zabi kawai ki bar gida saboda an samu matsala? pls nan gaba ko wani kika ga zai yi abun nan da kika yi ki basa shawaran kar yayi ba shi da amfani, ita dama rayuwa kowa da ƙaddararsa taki a haka ta zo sai kiyi hakuri ki zama me imani ki amshesa hannu bibbiyu, ko da wasa karki sake tunanin wannan shine solution dinki ke macece, leaving home is never a solution, ke baki tunanin halin da iyayenki da yan uwanki za su shiga saboda abin nan da kika aikata? Ko ke ba musulma bace? Don duk musulmi an san sa da tawakalli ne" Ita dai kanta na kasa hawaye sai sauka idonta yake, yace "Yanzu kin san ta yanda aka bi ki har Suleja?" Ta girgiza masa kai, ya dauko wani kwali ya ajiye mata a gabanta, kallon kwalin ta dinga yi sai kuma ta saci kallon Usman dake kallonta tayi saurin dauke kai, Dpo yace "Ko da wasa next time do not try this nonsense again pls" Sai kuma ya kalli Dr Khalil yace "Kai kuma Allah ya saka maka da alkhairi for all ur effort, ni yanzu zan fita, za ku iya tafi Allah ya tsare gaba....." Har suka fito daga office din Dpo Mayraah bata yarda ta kalli Usman ba, sai makalewa kusa da Dr Khalil take, bayan sun fita daga police station din, Dr Khalil na kallon Usman yace "Ina kuka nufa yanzu, don naga it's almost magrib" Ita dai Mayraah na can gefe tsaye gabanta sai faduwa yake, ta saci kallon Usman yafi a kirga, Usman yace "Ba komai, na saba driving din dare, i will drive to kaduna in sha Allah" Dr Khalil yace "Toh ba damuwa, idan ka isa kadunan sai mu yi waya" Usman yace "To in sha Allah, thank you so much Dr" Dr Khalil yayi murmushi yace "You are welcome" Daga haka Dr Khalil ya koma gun Mayraah yace "Ki je ku tafi..." Ko rufe baki bai yi ba Mayraah ta fashe da kuka tace "Wallahi ni dai tsoronsa nake ji, na shiga uku" Dr Khalil ya buda ido yace "Saboda me?" Cikin kuka tace "Zai iya marina na sani, dama yaya Maheer ne" Dr Khalil yayi murmushi yace "Haba dai, ba abinda zai maki" Cikin kuka tace "Wallahi zai iya, me yasa ba Yaya Maheer bane ya zo" Juyawa Dr Khalil yayi ya kalli Usman da ya rungume hannu yana tsaye jikin mota fuskarsa babu yabo babu fallasa, komawa yayi wajensa yana ɗan murmushi yace "Barrister don Allah ayi mata hakuri, tace tsoro take ji zaka bugeta" Usman ya girgiza kai yace "Not at all.... Ka tambayeta ko na taɓa dukanta, she is waisting our time, muna da tafiya a gaba" Dr Khalil yace "To plss ayi hakuri barrister" Sai da Dr Khalil yayi da gaske da Mayraah sannan ta tafi ta shiga motar Usman, amma tana shiga sai ta wani tsuke fuska tana makale da handbag dinta, Usman ya kara yi ma Dr Khalil sallama sannan ya bude driver seat ya shiga ya tada motar, Dr Khalil ma ya nufi motarsa, har suka hau kan hanya bai ce mata ba ita ma bata ce masa ba.
Chapter 199 · 0% Book details