← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 313

Sashe 36

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yace yana waje, ta dau jakarta ta lallaba ta fice daga gidan babu wanda ya lura da ita, tana zuwa inda tace ya tsaya ya jirata ta bude jaka tana kokarin fiddo gold taga wayam, da farko ta zata idonta ne ya nuna mata haka, ta kikkifta idon ta sake wangale jakar still taga wayammm, wani azababbun zufa ne suka hau keto mata tana gwale ido tace "Hamisu, duba min jakar nan ka ciro Gwal din a ciki ni na kasa cirowa" tana fadin haka ta manna masa jakar a hannu tana zare ido, Hamisu ya mayar mata jakar da sauri yace "Ke me jakar baki gani ba sai ni Hajiya" Zazzage komai na cikin jakar ta hau yi a kan titi a rikice amma babu gold bBu alamar Gold, da karfi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku da Badiyya" Hamisu yace "Gaskiya Hajiya kin bata min lokaci ne kawai, ai da kin fara dubawa kafin ki kirani.... Gashi customers can na ta jirana na bar su na yo nan wajen ga Unguwan nisa, kawai ni bari in tafi kasuwa yanda ake ciki sai ki kirani" Yana fadin haka ya buga machine dinsa ya kara gaba. Kiris ya rage Haseenah ta saki fitsari a titin, ko ina na jikinta rawa yake tsabar tashin hankali, ta dai samu ta ruga cikin gida ta shige visitors toilet dake cikin compound tayi fitsarin, tana fitowa ta tafi can backyard din gidansu ta zauna zufa wani na bin wani a goshinta, ita ba abun tayi raising alarm ba asirinta ya tonu Mummy ta gano abinda ke faruwa, dazu fa kafin ta fita da Maheer sai da ta duba jakar yana ciki kuma tunda suka dawo bata ajiye jakar nesa da ita ba balle tace a dakinta aka dauke, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ko dai wajen siyan kayan ne aka mata sata da taje gwadawa?? Sai a sannan ta fashe da matsanancin kuka ta daura hannu a ka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace me zan ce ma Badiiya" Ammi ta kasa motsawa daga inda take zaune tana kallon abinda Maheer ya ajiye masu saman gado ita da Aunty Mariya, Aunty Mariya ta mike a gigice tace "Ina ka samo wannan Maheer?" Shi dai bai ce komai ba ya koma gefe daya ya rungume hannunsa yana bin su da ido, Ammi ta kallesa tace "Maheer wannan daga ina? Ko sabo ka siyo ne?" Yace "Babu wani sabo, tsohon da ku ka sani ne dai" Ammi ta buda ido with shock tace "Daga ina??" Maheer ya ɗan yi shiru yana tunanin abinda zai ce masu don bai son fara painting Haseenah black wajen Ammi, he just have to cover her up in other not to create doubt tsakaninta da iyayensa, Aunty Mariya ta hade rai tace "Dallah ka mana magana ka yi wani shiru, where did u find this?" Ya shafa kansa yace "Ita warce Ammi bata son laifinta ta kai ma Haseenah ajiya, shine Haseenan ta bani dazu da naje gidan, Badiyya ta kai ma Haseenah sarkan ta ajiye mata" Ammi ta dafe kanta cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Aunty Mariya kam buda baki tayi hangangan tsabar mamaki, Maheer ya juya ya fita daga dakin, Ammi ta fara hawaye tana girgiza kai ta kasa cewa komai, Aunty Mariya ta mike ta dau Gold din ta adana shi inda babu wanda hankalinsa zae kai wajen a dakin Ammi ita ma ta fita daga dakin. Mami ce zaune parlonta a sama tare da yan uwan mijinta maza su biyar, Kawu Mansur yace "Maryam da girmanki da hankalinki bai kamata kina biye Halima kuna maida maganganu haka ba, shi sa muka ja ki muka dawo nan sama dake ayi magana ta fahimta...." Mami dai wani direction din daban take kallo kawai zuciyarta na tafarfasa, Kawu Mansur yace "Tsakaninki da Allah Maryam me kika sani game da gidan nan da Abdallah yake neman aure?" Mami tace "Au ashe ma yan uwana ne kenan da har zan san wani abu game da gidan, ka ga fa Yaya Mansur yanda ku ka samu wannan labari sama ta ka to nima haka nan ya riskeni, yanda duk aka bi ku da Envelope nima haka aka kawo min nan, sannan ina ganin ai ba wani zai zauna ma Musharraf da yarinyar nan ba, ko ma menene tunda yace yaji ya gani yana so ina ga a bar yaron kawai, he is old enough to make decisions for himself, shi ma ai an basa takardan kafin ma a kai maku and he wasn't bothered about it...." Kawu Faisal na kallonta kasa kasa yace "Tunda auren wasan yara ne da har zai bude baki yace yaji ya gani ba? Mu kuma gamu a banza, To abinda ke da shi baku sani ba shine, bai isa ya yanke ma kansa decision kansa tsaye as far as mu iyayensa muna raye, don haka ba shi da wani say a wannan lamari sai abinda mu manya muka ce, in kuma bashi da manyan ne sai ki gaya mana yanzu mu ji...." Mami ta masa wani kallo kafin ta kai ga cewa komai Kawu Mansur yace "Yanzu dai duk ba wannan ba, wannan lamarin da ake ta cukuikuyawa abu ne me sauki wllh, mu fa muka kai kudin nan ba wasu suka kai mana ba, mafi sauki shine mu sake komawa gidan don a warware mana abinda ya shige mana duhu daga bakin iyayen yarinyar nan da suka amshi kudi hannunmu, ai ba sai an tsaya ana cece ku ce ba, ga best alternative kawai na kawo" Mami tace "Ohh da an san da haka za a zo nan a daga min hankali saboda an raina ni? To wallahi ku ja ma Halima da Rumaisa kunne idan basu fita harkata ba ina me tabbatar maku hukuma ce zasu min iyaka da su, nan ba da dadewa ba kuwa" mikewa Kawu Saleh yayi ya fita daga parlon sauran ma duk suka mike suka bi bayansa parlon ya rage Kawu Mansur kawai, Kawu Mansur yace "Yanzu dai kiyi hakuri Hajiya, duk abinda ake ciki za ki ji kira anjima, ko kuma in zo da kai na" Daga haka ya mike ya fita daga parlon.... Abbansu Maheer na Bedroom dinsu yana duba wasu takardu, dawowarsa kenan daga Abuja saboda daurin auren 'ya yan nasa da za ayi gobe, Ammi ta shigo dakin tace "Yallabai wai kayi baki fa" Abba ya kalleta yace "Daga ina?" Ammi tace "Maheer yace kamar dangin yaron nan ne Musharraf, yace su suka kawo kudi" Abba ya ajiye takardun hannunsa yace "Toh lafiya, Allah sa dai ba cewa za su yi a daga bikin ba" Ammi tace "In hakan shine mafi alkhairi ai babu yanda aka iya" Abba ya dau wayarsa ya fito daga dakin ya fito compound don a nan parlon baƙin yake, yana shiga parlon duk aka gaggaisa, Maheer ya shigo ya ajiye masu carton din ruwa da lemo, Abba yace "Ya shirye shiryenmu?" Duk suka amsa da "Alhamdulillah mun gode Allah" Abba yace "To Madallah" Kawu Mansur yace "Dama wata magana ce ke tafe da mu Alhaji, sai dai za mu so kayi mana uziri kuma ka fahimce mu, don ko kaine a shoes dinmu iyaka hakan kai ma zaka yi" Abba da yayi jim, can yace "Ikon Allah, to ina sauraronku Alhaji, Allah sa dai lafiya" Maheer dake kokarin fita daga parlon jin abinda Uncle din Musharraf yace sai ya kasa fita lkci daya jikinsa ya basa all is not alright, Alhaji Faisal ya ciro takardan aljihunsa ya mika ma Abba, Alhaji Mansur ma ya ciro ya mika masa, Alhaji Sale shima yayi haka Abba dae sae amsan takardun yake yana bin su da kallo cike da mamaki yace "Na menene wannan din?" Alhaji Mansur yace "Mu ma duk haka suka iso gidajenmu a yammacin jiya, ka duba ka gani Alhaji" Abba ya maida dubansa kan takardun baya ko kiftawa amma ya kasa duba ko daya ya karanta, Maheer ya karaso kusa da Abba zai amshi takardun Abba ya daga masa hannu, calmly yace "Zan duba" Yana fadin haka ya shiga duba content dinsu gaba daya, daya bayan daya yabi har ya gama karanta su, a hankali ya linke su duk ya ajiye gefensa yana kallon Uncles din Musharraf da suka zuba masa ido gaba dayansu, Abba ya ɗan kwantar da kansa jikin kujeran da yake zaune, trying all possible best to be calm yana kallonsu yace "Haka ne.... Duk abinda ke rubuce jikin takardun nan gaskiya ne amma banda abu daya zuwa biyu ..." Yana kai wa nan yayi shiru, Alhaji Faisal yace "To Alhamdulillah, sai dai fa Alhaji abu dayan nan zuwa biyu da kace is of no importance to us right now, don tun asali baka bi ka'idar da ya kamata ka bi ba while giving out the girls hand in marriage tunda kasan da wnn babban issue din a kasa, in other words an yaudaremu an kuma yi playing with our intelligence an mayar damu kananun mutane, sannan an cuci ɗan mu, a lamari na aure babu amfanin shigowa da rashin gaskiya cikinta saboda gudun abinda zai je ya dawo, domin haka muke son sanar da kai cewa a yanzu mun janye daga wannan auren da muka nema ma ɗan mu ake kokarin daura sa gobe, sadakinmu da duk wani abu da aka kawo gidan nan za mu aiko a amsar mana in sha Allah, gatan da ko wani uba zai yi ma ɗan sa kenan a issue irin wannan, mun bar ka lafiya Alhaji" Abba was speechless, har duk suka mike suka fara fita daga parlon, Maheer da gaba daya ya dinga jin maganganun Uncle din Musharraf kamar a mafarki yayi saurin daukan takardun da Abba ya ajiye a gefensa yana dubasu daya bayan daya, kallon Abba yayi, lkci daya ya duka nan gabansa hankali a tashe yace "Abba ban gane ba, what is all this? Me yake faruwa??" Abba ya kasa ce masa komai don yayi nisa tunanin da ya tafi, Maheer that is getting impatient don har wani zafi yake ji duk da AC dake kunne parlon yace "Don Allah kace min wani abu Abba, i am loosing my self, I can't stand this
Chapter 36 · 0% Book details