Sashe 159
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
duk abinda ya samu Mayraah in ma rayuwarta ya lalace to alhaki akan Ammin ku, da ace ita bata juya mata baya ba komin pressure din kakanku da ahalinta Mayraah bazata yi tunanin barin gida, tare da kai muka karanta wasikar da ta bari ai ko? So kar ka kuma ce min Ammi bata yi deserving abinda na mata ba, sabon gidan nan da kake gani ban taɓa tunanin ba ita ce zata fara shiga ciki ba don ita nake gina ma, so do not blame me for my actions, And mind you ni ba jahili bane Maheer nasan abinda nake...." Maheer dai kansa na kasa bai sake cewa komai ba amma zuciyarsa fal yake da tausayin mahaifiyarsa, he felt so really bad, Abba yace "So duk abinda ake ciki a station din i will call and let you know" Daga haka Abba ya juya ya koma cikin gidan, Maheer ya bude motarsa duk jikinsa a sanyaye mai gadi ya bude masa gate ya fita daga gidan. Karfe shidda da rabi Musharraf ya fito station Maminsa na biye da shi a baya, after few seconds Usman ya fito ya nufi motarsa, sai ga Abba ma ya fito bai ko kallesu ba ya nufi tasa motar shi ma, Mami ta bi Abba da kallo har sannan maganganunsa na mata zafi a rai, Maheer ne ya fito ya nufi tasa motar shi ma without looking at them, Mami na kallon Musharraf on a serious note tace "Look at me Musharraf" Musharraf dake saka agogonsa ya juya ya kalleta tace "Babu kai babu yarinyar nan har abada, ni ban san ai guardian din nata marasu mutunci bane marasu daraja...." Musharraf ya katse ta yace "To ba su Kawu Mansur da Aunty Halima bane suka fara masu rashin mutunci ba Mami" Tsawa Mami tayi masa tace "Ina magana kana magana? to wallahi idan kana son kaga bacin rai na Musharraf kar ka fita sabgar er mutanen nan" Da damuwa Musharraf yace "To Mami ina ma take yanxu? Ba ma sai an san inda take ba before all this, we should even pray she is safe" a fusace Mami tace "Oho that's not my problem, ni dai na gaya maka in ba fushina kake so ba babu kai babu ita har abada kuwa, in kuma bakina kake so to bismillah" Kallon Mami kawai Musharraf yake helplessly don bai taɓa ganin Maminsa so angry at him ba haka, truly Abba da Usman sun yi maganganun da ko ma wa aka gaya ma sai ransa ya baci, but shi duk wannan ba damuwarsa bane, matsalarsa kawai inda Mayraah take, Dai dai nan Yayan late father dinsa wato Hon Alhaji Kabir Saminu ya fito daga station din, escort dinsa dake haraban Police station din suka nufosa da sauri, Yana kallon Musharraf strictly yace "Kai..." Musharraf ya juya ya kallesa sannan ya sunkuyar da kai, strictly Alhaji Kabir yace "Babu kai babu er kananun mutanen can daga this very moment, ban da ma kai wawa ne mahaukaci meye zaka ci gaba da bibiyar yarinyar da bata da asali? Are you stupid? Kai mutuncinka ne yanzu police station da suka kawo ka? Wallahi ban da mahaifiyarka da ta hana da babu abinda zai hanani Shari'a da su, mutanen banza kawai mutanen hofi makaryata, su har suna da wani sauran mutunci bayan lamarinsu babu komai facce karya, da mutuncin ka kan wata yarinya can mara asali an kawo ka nan ana tuhumarka sai kace wani Kidnapper ko ɗan fashi, da ban tako tun daga kaduna na zo nan yau ba kana zaton ba cikin barayi zaka kwana a cell ba yau? To wallahi kashedi na farko da na karshe kenan nake maka babu kai babu er su ko da kai ne HOD din department din ba Lecturer din ta ba, nonsense" Shi dai Musharraf kansa na kasa ko sanin abinda kawun nasa ke cewa bai yi ba, don tunanin ta yanda zai fara neman Mayraah kawai yake a ransa, Alhaji Kabir ya kalli Mami yace "Tare kike da motar ki Hajiya" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Ehh da motata nake" Alhaji Kabir yace "Shikenan.... ni zan koma kaduna yanzu" Mami tace "Baza ka bari gobe ba Alhaji" Yace "Ina da appointment da yawa goben, so we will be heading to airport now" Mami tace "Toh shikenan, Allah ya tsare, a gaida su Hajiya da yaran" Yace "In sha Allah" Ko kallon Musharraf bai yi ba ya nufi inda motar sa yake with his escort, sai ga DPO ya fito yace "Honorable tafiyar kenan?" Alhaji Kabir yace "Ehh wallahi zan koma kd yau ne" Har mota suka tafi tare da Dpo din, wanda abokinsa ne for long, Mami ta nufi motar ta without looking at Musharraf, bin bayanta yayi yana tafiya a hankali, ya bude back seat ya shiga, ita dai bata ce masa komai ba, suna kama hanya Mami tace "In dai ban isa da kai ba Musharraf wallahi ka ci gaba da kula yarinyar nan, ni kuma zan nuna maka ba kai kadai na haifa ba" Shi dai bai ce mata komai ba ya jinginar da kansa da kujera abinda ya damesa daban, wato yanda zai fara neman whereabout din Mayraah. Kamar yanda Alhaji Kabir ya kasance abokin Dpo, haka Abba ma Dpo din childhood frnd dinsa ne, kawai aka sulhunta su a wajen don an duba call history din Musharraf don ganin when last ma suka yi communicating da Mayraah aka ga babu communication kwata kwata tsakaninsu for long banda just of recent da ya dinga kiran wayarta baya samu, kamfanin layin da Mayraah ke amfani shi sun yi confirming babu wayar da ya shiga tsakaninsu for more than a month now, sannan asibiti da Musharraf ya kai ta ma an bincika an gano ba shi kadai ya kai ba tare da Dr Asma'u warce ita ma lecturer dinta ce suka je asibitin, har Dr Asma'u sai da aka kira a issue din to confirm. Bayan Mayraah ta idar da sallan Magrib a dakin hotel din da take ta bude jakarta ta ciro wayarta tana jujjuyawa, ciro sim dinta duk biyun tayi, ta mike ta zubar da su a karamin dust bin dake dakin sannan ta saka hijab dinta ta dau Atm card dinta ta fito daga dakinta ta sauka kasan reception, bayan sun gaisa da ma'aikatan hotel din dake zaune reception din ta fita, tsaye tayi bakin titi tana jiran adaidaita sahu, har ta samu tace "Don Allah Malam nearest supermarket nake son ka kai ni" Mutumin yace "I no dey hear hausa madam" Turanci tayi masa ta gaya masa inda zata je, yace ta shiga, tana shiga bayan tafiya me nisa ya tsaya dai dai wani babban shopping Mall ta sauka ta ciro kudinsa ta basa sannan ta shiga ciki. Bangaren mayukam shafawa ta nufa don bata dau cream dinta ba a gida, ta dau cream din da shower gel ta koma side din turarruka tana zaba kamar ance ta juya......