← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 313

Sashe 127

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake* [7/9, 9:07 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer ya jima zaune a parlor bayan ya sauka downstairs, gaba daya kansa ya ƙulle ya rasa wani tunanin zai yi, gashi da yamma yace zai je ya dauko Ammi yasan kuma in dai suka ji wannan abinda Abba yayi ba lallai Ammi ta yarda ya dawo da ita gidan ba, to amma me yasa Abba zai yi haka Ammi bata yi deserving haka daga garesa ba, rike kansa yayi, he is really confuse at this point don gaba daya he was short of idea, mikewa yayi a sanyaye, to wa ma zai gaya ma wannan maganar yanzu, Aunty Mariya ce ta fado masa ya fita compound yayi dialing numberta, tana dagawa bayan sun gaisa tace "Ka kai ta gidan ne Maheer?" Yayi wani ajiyar zuciya me cike da damuwa, duk da Aunty Mariya na kaduna sam bata jin dadin zaman da Ammi take tayi a gidan Hajja ta ki komawa gidanta for more than a month now, kusan kullum ita ke encouraging Maheer kar ya gaji da zuwa gidan Hajja ya dinga ba Ammi hakuri ta koma gidanta, ita dai fatanta ace Ammi ta koma dakinta a ko da yaushe addu'anta kenan, jin Maheer yayi shiru, Aunty Mariya da gabanta ya fadi tace "Ta canza shawara kuma ko?" Maheer ya girgiza kai a sanyaye yace "Aunty Abba ne ke sanar min ya kara aure.... He is just telling me now" a tsorace Aunty Mariya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ya kara aure kamar yaya Maheer? Aure fa kace" Maheer ya kasa ce mata komai, cikin kidimewa tace "Ban gane ya kara aure ba, shi Abban ya gaya maka haka?" A hankali Maheer yace "Yanzu haka daga parlonsa nake Aunty, ya tabbatar min yayi aure jiya kuma yau matar zata tare sannan kuma ni ga yanda muka yi da Ammi kan cewar yau zan je in daukota, akwai fa matsala Aunty, Ammi gani zata yi kamar nasan da auren Abba na mata shiru kuma na tilastata ta dawo, ni kuma wllh he is just informing me now" Aunty Mariya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wannan wani irin fitina ne daga wannan sai wannan duk Mama Ladi da Badiyyah suka ja mugayen abubuwan nan dake faruwa, yanzu ina Mayraah din? last time da na kirata tace min sauran masu 3 papers to ban sake waya da ita ba har yau, is she still in the hostel?" Maheer bai ma son ya furta ma Aunty Mariya kalman da Abba yayi wai zai kara aure saboda Mayraah don shi ma sai da abun ya dakesa, Abba look into his face yace zai auri warce zata rike masa Mayraah ya mance duk rikon da Ammi tayi mata kamar ita ta haifeta wanda ko da wasa su kansu basu san wacece Mayraah ba sai da wannan abun ya faru, kawai ya girgiza kai cikin sanyin murya yace "Sun gama on friday, yau kuma zan daukota daga hostel in maido ta gida" Aunty Mariya ta rasa abinda zata ce duk jikinta yayi mugun sanyi and she felt for her sister, ya da kuruciyarta ba a mata kishiya ba sai yanzu da ta fara ajiye surkai, nan da nan hawaye ya cika idon Aunty Mariya tana girgiza kai tace "Maheer this is seriously getting out of hand, yanzu sake blaming Mayraah din za su yi, dama suna ganin ta dalilinta komai ya dagule to ga uwa da uban dagulewa yanzu kowa zai gani, kaga shkkn sai su tabbatar da abinda suke tunani a ransu don yanzu ma cewa za su yi gashi Abban yayi aure duk a ta dalilin Mayraah, wannan wani irin fitina ce, me yasa Abba bai yi hakuri ba tun da yasan ba halin Ammi bane wannan, me yasa zai saka mata da haka bayan duk gwagwarmayar da suka sha tare a rayuwa, fisabilillahi sai da shekarunta zai kawo mata abokiyar zama saboda shaidan ya shiga tsakani??" Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Maheer dai ya kasa cewa mata komai duk jikinsa yayi mugun sanyi, Aunty Mariya ta matsar da abincin da take ci don gaba daya ya fice mata a rai, hankalinta yayi mugun tashi da batun nan da Maheer ya kawo mata, ko ya Ammi zata dau wannan labarin, ita ma ji yanda taji balle Ammi, da ba don uwa uwa bace da sai tace duk Hajja ce ta ja ma Ammi, duk Hajja ta kara rikita wannan al'amarin haka, kuma Badiyyah ita ce babban silar faruwa komai, hawaye kawai take ta kasa magana tana jin zuciyarta na zafi kamar ita aka ma kishiya, suka yi shirun kusan minti daya ko wannensu da tunanin da yake a rai, Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Yanzu Aunty ki bani shawaran yanda za ayi, bana son Ammi taji haushina in anyway, gani zata yi i know everything, kuma in dai tasan da batun kishiyar nan nasan bazata dawo ba Aunty" Aunty Mariya ta sauke ajiyar zuciya tana share hawayenta tace "Kawai ka bari gobe lahadi zan shigo da safe zan nuna kawai na zo bikina, idan ya so sai in rakata gidan, in mun koma gidan we will sort things out a samu ta fara komawa gidan dai tukunna, don tabbas kana maidata gida Anjima duk bayanin da zaka mata bazata fahimceka ba za ku ma taga kamar da hadin bakinka aka mata haka, ka bari kawai ni zan zo gobe in rakata mu koma gidan, kawai ka basu wani uzurin ko na emergency a asibiti sai kace gobe zaka je ka dauketa ka kai ta gidan" A hankali Maheer yace "To Aunty, Allah ya kai mu goben" Tace "Umar din ya iso ne?" Ya girgiza kai yace "Anyi delaying Flight din nasu gobe zai iso in sha Allah" Aunty Mariya tace "Toh Allah ya kai mu, ita ma Mayraah kar ka maidata gidan yau, it's better gobe ta same mu gidan ba mu sameta ba kilan abubuwan za su fi zuwa mana da sauki" Maheer ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "But Abba insisted sai na maidota yau fa Aunty, instruction din da ya bani kenan" Aunty Mariya tace "Just find a way out Maheer, kayi duk yanda zaka yi sai gobe zata koma gidan, zan kira ka anjima har kaina ya fara ciwo wallahi, wannan wani irin jarabawa ne astagfirullah" katse wayar tayi, Maheer ya fita daga gidan ya shiga motarsa ya wuce gida ransa duk a dagule. Mayraah ta saka hijab dinta ta fito waje ta dalilin kiranta da aka yi, yana tsaye jikin mota ya rungume hannunsa, ɗan murmushi tayi ta karasa kusa da motar tana kallonsa tace "Ina yini Yaya?" Yace "Lafiya lau, how was the final exams?" Tace "Alhamdulillah" yace "Saura project" Ta gyada kai tace "I am submitting on monday in sha Allah, yaya yaushe ka dawo?" Yace "Not long ago" Tace "Ya aiki?" yace "Alhamdulillah" Ta jingina da motar tace "Ya Maheer yace min yau ya Omar zai dawo, is he back?" Usman ya girgiza kai yace "Sai gobe in sha Allah, ki shiga ki dauko kayanki, za mu tafi gida" Sosai gabanta ya fadi nan da nan mood dinta ya canza ta kafesa da ido babu ko kiftawa, shi dai kallonta kawai yake, haka kawai Mayraah taji da ma kawai ita dai ta ci gaba da zama a hostel din in ma na har abada ne, she is tired with the way things are happening all of a sudden, bata awa daya kalaman Ammi na karshe basu fado mata a rai ba, wani lokacin ta ɗan yi murmushi, wani lokacin kuma taji hawaye na sauko mata, sai taga kamar tafi samun rest of mind zaman da take a hostel din duk da ba wai damuwanta ya yaye bane, a'a har yanzu tana cikin damuwan sosai ma but baza ta so ace ta koma gidan nan ba ko a mafarki, Usman dake ta kallonta as if reading her mind yace "Ko nan din gidanku ne da baza ki bari ba Madam?" Nan da nan hawaye ya fara zuba idonta, ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yayi kasa da murya yace "Za ki koma gida Mayraah, it's still ur home baki da wani wajen da ya wuce can, baki san ko ina ba sai can, as far as we are concern bamu da wata kanwa da ta wuce ke, Abba yace in je in dauko ki, ko gida ban karasa ba na taho nan, so go and pack only ur clothes ki bar ma Ummi duk wani foodstuff ki zo mu wuce gida" Mayraah ta share hawayen dake ta sauko mata cikin rawan murya tace "Amma yaya ban gama project din ba fa, don Allah a bari in gama" Yace "Abba yace zaki gama a gida, be a good gal and do as i say" Juyawa tayi a hankali ta koma cikin hostel din ya bi ta da ido, bayan wani lokaci sai ga ta ta fito da jakarta Ummi ta dauko mata akwatinta biyu, har sannan hawaye ya ki tsaya mata, ita kanta Ummi jikinta yayi sanyi don ta zata Mayraah zata tsaya har nan da sati biyu kafin su gama da internal and external defense dinsu, Usman ya bude masu booth suka ajiye boxes din da jakar, Usman na kallon Ummi with smile on his face yace "Thanks for accommodating our sister Ummi, Allah Ubangiji ya baku sa'an exams, hope kun yi exchanging contact" Ummi na murmushin ita ma tace "Ameen, eh mun yi exchanging" Yace "Maa sha Allah, God bless you" Daga haka ya zaga ya bude ma Mayraah front seat yana kallonta, ta daga kai ta kallesa tana share idonta, bai taɓa bude mata mota ba sai ranan, Maheer kam sai dai in ita ta bude ta shiga amma he is never tired of opening the car door for her, bayan ta shiga ya kulle motar ya zaga ya shiga
Chapter 127 · 0% Book details