← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 216 OF 313

Sashe 216

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kawai, don zuwa jibi za su bi jirgi in sha Allah, kayan sawansu kawai za su dauka..." Sake baki Mama Ladi tayi tana kallon Abba bata ko kiftawa. Mama Ladi na gyara shimfidar da zata kwanta bayan ta ci kukanta ta gode Allah tace "Toh ma sai kace wata gantalalliyar tsohuwa mara makabuli ina ni ina bin ku wani Habuja, sai kace ban san me nake ba da zan kwashi kafa in bi ku kamar a garin gaɓa gaɓa, ai da wayo na kuma ni ba mahaukaciya bace nasan me nake, amma abinda yayi min ciwo har na zubda hawaye dalilin da zai sa Mamuda yace in dauki Badiyyah mu tafi karaye, a dubi girman Allah a gaya min me na hada da Badiyyah da Mamuda zai ce min haka? To wannan cin mutuncin da yayi min shi ya min ciwo har nake ta kuka amma ba wani abu ba" Ammi dai dake zaune parlon ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba, Mama Ladi tace "Kuma a gaskiya ni ba a taɓa ci mun mutunci irin yau ba ma tunda uwata ta haifeni, wai in tafi da Badiyyah karaye ashe ma ni na mata cikin, to wallahi ki ja masa kunne ya fita harkata ya bar hada ni da Badiyyah, babu abinda na hada da ita haduwar bariki rabuwar bariki, kakarta ce fa yayata amma ko a lahira ni bazan ga Badiyyah ba, in zuciyata ta debeni sai in iya ja masu Allah ya isa daga Mamudan har shegiyar Badiyyan da yake hada ni da" Daga haka tayi kwanciyarta tana matsar wasu sababbin kwallan tace "Dama da asussuba Mashir ya zo ya kai ni tasha, maganina ma kenan da nayi ta zama nan kamar wata mara galihu" Ammi tace "Kiyi hakuri Mama Ladi duk bai kai...." A fusace Mama Ladi ta mike zaune tace "Rufe min baki, ke da kika ji yana cewa in koma karaye baki da bakin magana ne? Ni na cancanci Mamuda yayi watsi da ni? Da ba don ni ba ai gidansa fanko ya so komawa amma ɗan Adam me mance alkhairi, kullum fa sai an bugo min waya daga karaye ana tambayar Baaba ladi yaushe za ki dawo, da gata na kaca kaca a can, to kafin ku tattara ku koma Habujan ni gobe da Asuba zan bar gidan, kuma ki mayar masa da shegen kudinsa da ya bani bana bukata, ban rasa komai ba a karaye wallahi" Daga haka ta sake komawa ta kwanta tana matsar sabbin kwalla, Mikewa Ammi tayi ta shiga bedroom dinta don for almost an hour Mama Ladi ke ta mita da koke koke ita dai hakuri kawai take bata, wajen karfe sha daya da rabi ta sake fitowa parlon rike da wayarta ta ga Mama Ladi kwance ido biyu, Mama Ladi da bata wuce karfe tara da rabi da ta ci ta koshi take bacci, Ammi dai bata ce mata komai ba ta fita daga parlon ta sauka downstairs, Maheer ta ganin kwance kan 3 seater idonsa rufe, Ammi ta karasa kusa da shi ta taɓasa tace "Maheer" Bude ido yayi, ya mike zaune tace "Baka tafi ka kwanta ba kake bacci a nan" Ya kalli agogo sannan ya mike zaune, Ammi ta zauna daga side dinsa tana kallonsa tace "Ka ci abincin ma kuwa?" Yace "Na ci" Sai kuma ya mike yayi mata sai da safe ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita, Number Aunty Mariya ta fara dialing sanin mijinta baya gari, yana fara ring kuwa ta daga, tace "Baki yi bacci ba Ammi" Ammi tace "Ban yi ba" Aunty Mariya tace "To ya gidan? Ya su Mayraah?" Ammi tace "Alhamdulillahi" Shiru Aunty Mariya tayi tana sauraren dalilin kiran Ammi don tasan tunda ta kirata by this time akwai magana ne, Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta sanar ma Aunty Mariya abinda ake ciki, Aunty Mariya tayi farin ciki da samun aikin Mayraah da kuma garin Abuja da za su koma, she was so happy, tace "To yanzu Ammi ya za ayi da Mama Ladi?" Ammi tace "Mama Ladi? Badiyyah dai.... tambaya za kiyi ya za ayi da Badiyyah tunda ita Mama Ladi tana da inda za ta, Shi kuma yace babu inda za aje masa da Badiyyah, i am confuse ban san ya zan yi ba kuma" Aunty Mariya tayi shiru, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Amma dai Ammi shawaran da aka yanke tun farko shine a kai ta Bichi...." Ammi tace "To bari kiji tunda na kirasu na sanar masu abinda ke faruwa buden bakin shi yayan baban nata wai sun kwana biyu su basa Bichin sunyi tafiya, ita kuwa autarsu baban nata ita ma da na kirata bayan kwana biyu ce min tayi tana wajen mijinta a portharcourt yaranta ma na gun kakarsu, Kinga ai sun hada baki kenan, ni kuma gaskiya ban wani ga laifinsu ba, babu wanda zai karbi Badiyyah ko waye ma haka zai yi, ko don na bar zancen ban gaya maku ba? ita kanta Mama Ladi bata san yanda muka yi da yan Bichin ba ai har yau, to yanzu ga abinda Mai gidan yace i don't want to have any issues with him, don da farko cewa ma yayi Mama Ladi ta koma karaye da ita shine ta dinga rusa kuka wai an cuceta an hadata da Badiyyah" Aunty Mariya tace "Kinsan me zai faru Ammi, ai Hajjan yanzu jikinta da sauki don ko jiya naje gidan Baaba Yahanasun dubata don haka kawai ki tattara Badiyyar ki sa ta a mota ta koma can wajensu ai ta san gidan, kuma ba sai kin gaya ma kowa ba kawai su ganta, idan ya so ki kashe wayarki kawai, ni dai Hajja bazata fara cewa Badiyyah ta zo wajena ba tunda tasan yanda yanayin gidan nan yake, in kuma kince ba haka ba to ni kam ban san yanda za ayi ba kuma" Ammi tayi shiru tana nazari, Aunty Mariya tace "That is the only way out fa, infact don ma mun samu Abbansu Maheer din ne amma wallahi ba ko wani namiji ne zai yi tolerating haka ba, ko mai gidana nasan bazai fara yarda Badiyyah ta zauna gidana ba, dama Mama Ladin ce dai dai tafiya da ita karaye ni ko nasan ko daura ma Mama Ladi Badiyyah aka yi a kafa sai ta kunceta" a hankali Ammi tace "To shikenan, zan sa Maheer ya kai ta tasha gobe ya saka ta a motar Kadunan tunda babu wani mafita bayan wannan" Aunty Mariya tace "Shine kawai magana, yanzu yaushe za ku koma Abujan?" Ammi tace "Ya ce jibi..." Aunty Mariya tace "Kai maa sha Allah, wallahi nayi murna sosai Ammi Allah ya sanya alkhairi, dama duk mahakurci bazai taba taɓewa ba, sannan Ammi ina ta son zan maki magana akan matar Maheer, yanzu shikenan ana nufin haka zai ci gaba da zama da ita? Wato ta ci bulus duk abubuwan nan da suka faru uwa uba ga bin bokaye da malamai, asiri har a dakinki?" Ammi tace "Mariya, the girl is pregnant" Sai da Aunty Mariya ta mike zaune daga kwancen da take, tace "Pregnant kuma Ammi?" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Har wata uku kuwa, shi dai yace bai san da shi ba, shine Abban nasu yace a jira ta haihu ayi DNA, wannan dalilin yasa muka hanasa sakinta tukunna, yanzu ma nasan kawai suna zaune under same roof ne babu yanda zai yi tunda kinsan baya ketare maganata amma ba da son ransa suke waje daya ba, ai ko da ɗan sa ne ni bazan yi supporting ya ci gaba da zama da ita ba wallahi, for now dai we just have to be patient a jira ta haihu ayi DNA din, kinji dalilin da yasa take gidan nan har yanzu" Aunty Mariya jikinta yayi sanyi, a ranta kuwa har ta fara addu'a Allah sa Maheer have nothing to do with the baby, Allah ya rabasa hada zuri'a da irin Haseenah, can dai tace "Amma Ammi an tabbatar kuwa, anje anyi scan ko kawai da baki ta fadi? Yarinyar nan fa makira ce babu abinda bazata iya aikatawa ba wllhi, sai ta iya forging cikin ma ko a asibiti" Ammi tace "Kin manta shi likita ne Mariya? Anyi scan, ai shine nace maki har wata uku with few days" Aunty Mariya ta tabe baki tace "Ai shikenan, amma what if the DNA result comes out negative after still keeping her for 7 months Ammi?" Ammi tace "Ta cuci kanta ba mu ba" Aunty Mariya ta girgiza kai tace "Allah Ubangiji ya shirya mana zuri'a" Ammi tace "Ameen, sai da safe" Sallama suka yi Ammi ta katse wayar ta wuce sama zuwa part dinta, har a sannan Mama Ladi bata yi bacci ba, Ammi ta kalli agogo da mamaki tace "Baki yi bacci ba Mama Ladi?" Banza Mama Ladi ta mata, Ammi ta karasa cikin bedroom dinta. Washegari da sassafe Ammi ta kira Maheer ta sanar masa yanda suka yi da Aunty Mariya kan cewar ya dau Badiyyah ya kai ta tasha, shi dai yayi shiru yana kallonta, tace "Ko ya ka ga Maheer?" Maheer yace "To ya za ayi dama, tunda relatives din babanta na denying dinta and they are not to be blamed, kawai hakan shine mafita" Ammi tace "Dama nima ban yi blaming dinsu ba" Maheer bai sake cewa komai ba, Ammi tayi kasa da murya tace "Da zaka taimaka ma tunda yau Saturday da kayi dropping dinta a kadunan saboda situation dinta" Maheer yace "Ai yau din ma ina zuwa aiki Ammi, kawai dai ina dawowa da wuri ne" Ammi tayi shiru, sai kuma tace "Toh shikenan" Yace "In ba dai Barrister za ki ma magana ba tunda yana nan" Ammi ta rike haɓa tace "Wani Barrister din?" Maheer yace "Usman mana, shi da ya maida zuwa kaduna kamar zuwa cikin gari" Ammi ta taɓe baki tayi murmushi kawai bata ce komai ba, Maheer ya mike yace "Ko ni sai inje in masa magana yanzu" Ammi tace "Ka dai san dama ba Badiyyah bace, amma ko me zaka ce masa in dai Badiyyah ce bazai je ba" Usman ne ya sauko downstairs zai je kitchen ya hado shayi, Ammi ta bi sa da kallo, ya karaso
Chapter 216 · 0% Book details