Sashe 30
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ta rike haɓa tace "Ke a haka kike son ki kwace ma yarinya saurayi ko girki baki iya ba goɗe goɗe da ke? Idan ba mantawa nayi fa da shekara biyu ko daya Mashir ya girme ki, amma ace guzuma irinki baki iya sarrafa kwai ba, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to kinyi ma kwai wannan azababben suyan ina ga idan girki za ki yi me gaba daya? Aa Hajja ta cuce ki, me za ayi da mace da bata iya girki ba sai kwalliya a fuska a wannan zamanin, shi saurayin Meran me zai yi da warce bata iya girki ba?" Ammi dai na tsaye ta kasa cewa komai, Mama Ladi ta kalli Ammi tace "Wallahi baki ji kwan ba kamar ba kwai ba Ammi, ni na zata flawa ce aka lafta ma tarugu da maggi da gishiri, ko sati biyu fa ba ayi ba matar nan taje har karaye ta sameni tana kuka wiwi wai Mera ta kwace mata saurayi gashi har za ayi aure kuma babu wanda ya dau mataki a kai kowa ya goyi bayan Mera, wllh ina ta tausayinta nace amma kun ci amanar Rukayya, kuma idan baku yi hankali ba sai wuta ta ci ku, har na kullaci Meran dazu tana gaisheni nayi mata banza ashe masharanciya ce Badiyya ban sani ba, nasan da Mera aka saka wannan suyan da tuni na kusa cinyewa ina neman kari, aa gaskiya Hajja ta cuci Badiyya, kuma nayi da na sanin goya mata baya da nayi da taje wajena" Mikewa Badiyya tayi ta nufi kofa fuuuu ta fice daga dakin kamar zata tashi sama, Mama Ladi tace "Muguwa kawai, Mijin Mera sai gani sai hange tunda ke makaryaciya ce warce bata iya girki ba" Ammi dai ta rasa ma me zata ce, wato karya Badiyya ta musu ta tafi bichi ashe Karaye ta tafi wajen Mama Ladi, Mama Ladi ta koma ta zauna tace "Gaskiya a fitar min da wannan azaban a kira Mera ta soya min kwan da zan iya ci" Ammi ta sunkuya ta dau plate din kwan tace "Kiyi hakuri Mama Ladi, yanzu za a kawo maki wani" Mama Ladi tace "Hakuri ai ya zama dole, munafukar yarinya wai Mera ta kwace mata saurayi, wani saurayin arziki ne zai aureta bata iya girki ba, wanda bai iya soya kwai ba ai babu abinda zai iya kuma a rayuwarsa har ya mutu" Ammi dai ta fita daga dakin. Bayan la'asar Hajja ta tafi sama har zuwa dakin Mayraah wajen Mama Ladi, Rabon Hajja da haurawa saman gidan zai yi shekara bakwai, tun wani rashin lafiya da Ammi tayi, Hajja na tsaye bakin kofa bayan ta shiga dakin tace "Ke Ladi tashi zaki yi tunda kin huta mu tafi gidana don nan baƙi yawa za su yi zuwa nan da kwanaki kadan, gwara mu je inda zaki sake babu takura" Mama Ladi dake kishingide jikin pillow tana sakace hakora bayan ta ci kaza tayi nak tace "Ko yaya?" Hajja tace "Kwarai kuwa, kinga ni ma gida zan tafi Maheer zai ajiye ni yanzu" Mama Ladi tace "Toh shikenan, a kira min Mariya ta zo ta dau min akwatina mu sauka kasa akwai dukiyana a ciki bazan ba yara ba gaskiya" Hajja tace "Toh bari in mata magana" Hajja ta juya ta fita, bayan wani lokaci sai ga ta ta dawo tare da Aunty Mariya, Hajja tace "Akwatinta zaki dauka a saka mata a mota za mu tafi gida" Aunty Mariya ta shigo dakin da sauri ta nufi inda akwatin yake ta duka zata dauka Mama Ladi tace "Munafuka algunguma wato daukar akwatin zaki yi, to babu inda zanje ina nan tunda ba gidanki bane balle na mijinki, har zaki je ki wani ce ma Hajja ta lallabani ta tafi da ni tunda gani barbadaddiya, to ina nan har sai an gama biki tunda ba wajen Hajja na zo ba, ke har kin manta irin azabar da kika min kina yarinya da zaki dinga kakkabi da ni? To wallahi babu inda zan je, ai ba gidanki na zo ba, babu wanda ya isa ya hanani zama gidan nan har sai bayan biki" Aunty Mariya was sooo shock, don kasa motsawa tayi a inda ta duƙa, Hajja tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wannan wani irin magana kike Ladi, a ina kika ji wannan maganar haka?" Mama Ladi tace "Badiyya ce ta zo nan ta gaya min, kuma wllh bazata maku sharri ba ji tayi an fada ne, in dai an ga na bar gidan nan to Mamuda ne ya koreni, amma ita kanta Ammin tayi kadan Al-qur'an, ai bikin jikokina biyu na zo Mera da Mashir" Tana kai wa nan ta juya masu baya ta ci gaba da kwanciyarta, Hajja dai ta kasa cewa komai balle Aunty Mariya da ta kasa dagowa kamar kasa ya bude ta shige, Ammi da ke kokarin shigowa dakin dama a kan kunnenta aka yi komai, ta juya sum sum sum ta bar wajen ba tare da ta bari an ma san tana wajen ba.... Hajja na saukowa parlor ta dau er jakarta tace "To da Alkhairi na tafi gida ni kam" Ammi dai na zaune kan kujera banda dariya babu abinda take, sai ga Aunty Mariya ta sauko kasa kamar wanda ruwa ya cinye tace "Wallahi wallahi sai na yi ma Badiyya abinda bata taɓa tunani ba, ba tace ita magulmaciya bace munafuka, Ni zata je ta hada da wannan matar?" Hajja tace "A dai dinga tunawa marainiya ce" Daga haka ta bar masu parlon, Nan Aunty Mariya ta hau shiga dakunan gidan ranta a bace tana neman Badiyya, Sabira tace "Ai Aunty Badiyya ta bar gidan nan tun dazu fa Hajiya" Musharraf yayi parking kofar gidansu wajen karfe shidda na yamma zai shiga ya gaida Mami don bai da intention din kwana a gidan ranan, throughout today wayarsa a flight mode ya bar sa yasan Mami ta nemesa har ta gaji, balle kuma Mayraah, duk yau ita ma basu yi magana ba, yanzun ma da ya taho gida ba kunna wayar yayi ba still, kawai baya son Mami ta daga hankalinta ne, Yana sauka motar ya nufi gate din gidan, ya amsa gaisuwan da Mai gadi ke masa without looking at him, zai shiga ciki Mai gadin yayi kasa da kai cike da ladabi yana biye da shi yace "Yallabai an samu akasi fa" Musharraf ya juyo da sauri yana kallonsa yace "Akasin me?" Mai gadi yayi kasa da murya kamar munafuki yace "Wallahi dazu Hajiya za su fita da Dreba sai ga dai wannan mutumin da ya kawo takardan nan wancan ranan...." Musharraf ya katsesa a rikice yace "Sai me ya faru??" Mai gadin da har ya tsorata ya fara kame kame, a fusace Musharraf yace "Malam ka gaya min ya aka yi??" Mai gadin yace "Wallahi a kan idonta mutumin ya bani irin wannan takardan na ranan nan, don dreba ya fito da motar kenan daga cikin gidan za su tafi... Shine Hajiya ta sauke gilashin mota ta amshi takardan a hannuna, kaga ai bazan ce mata a'a ba ranka shi dade" Musharraf da yaji wani zufa na keto masa yace "Ita da waye a motar??" Mai gadin yace "Aa ita kadai ce, ina jin Check up zata je" Musharraf bai sake sauraronsa ba ya shige cikin gidan da sauri, cikin few seconds sai ga shi a parlor, babu kowa a parlon ya haura zuwa bangaren Mami, a parlonta ya sameta da mai aikinta dake shiga tayata hira a kai a kai, Mai aikin ta mike ganin Musharraf ta gaishesa da ladabi sannan tayi ma Mami sallama ta fita, Musharraf yayi kokarin calming kansa down yana kallon Mami dake kallonsa ita ma, A hankali yace "Good evening Ma" Mami ta sauke idonta daga kallonsa tace "Evening, me yasa ka kashe waya tun safe?" Ya zauna saman kujera zuciyarsa bai daina bugawa ba yace "Ina hutawa ne yau" Mami tace "Okay" Daga haka ta mike ya bi ta da kallo gabansa na mugun bugawa, bedroom dinta ta shiga sai ga ta ta dawo rike da Envelope a hannunta tana kallonsa, kadan ya rage Musharraf bai samu heart attack ba a lokacin, don sai da yaji komai nasa ya tsaya for some seconds....