← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 313

Sashe 109

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* [7/3, 9:26 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer was speechless and so weak, ya ma rasa me zai ce mata, lumshe ido yayi yana jin kukan nata har ransa, sai dai bai hanata kukan ba cause he want her to feel relieve ko yaya ne, sun fi minti goma zaune a wajen, ya dago kanta yana kallonta a hankali yace "Kiyi hakuri Mimi, komai zai wuce, u still remain our lil sis, we still remain together, babu inda za ki je, i know Ammi is not okay, bata san ta fadi duk maganganun nan ba" Kai kawai ta gyada masa hawaye na sauka idonta tana kallonsa, ya sa hannu ya share mata hawayen cikin sanyin murya yace "I assure you, that's not Ammi" ita dai kawai ta gyada masa kai, ya dagata suka tashi a wajen suka koma ciki, babu kowa Parlon ya wuce sama da ita zuwa dakinta, Mama Ladi na zaune tana tura bread dinta da kwai da sauri ga akwatinta a kusa da ita, tana ganin Maheer tace "Ina gama karyawa ka kai ni tasha Mashir, bazan iya ci gaba da zama ina kallon rashin imanin nan dake wakana ba, zan je ina da wani Malami a karaye, shi yake bani kaikayi koma kan mashekiya da dai itatuwan tsari, shi sa ka gan ni fess da ni da lafiyata, duk wanda yayi min mugun abu kansa yake komawa wllhi, to zan je in sanar masa abinda ke faruwa sannan ya taimaka yaga me ya samu er uwata Hajja, wa ya jefeta take abubuwa haka? don in na bar ta a haka wallahi wuta Allah zai ajiyeta, gwara in je tun wuri in nemo mata taimako, kai kana jin maganganun Ammi kasan zugota aka yi ba yin kanta ba, yaushe har bakinta ya bude zata yi wannan tabargazan, Aa wllh zugota aka yi kuma ba kowa zai zugota ba sai Hajja da tsinanniyar jikarta wanda sai ta kusa ajalinta, ke Hajja tsofe tsofe dake baza ki koma ga Allah ba sai kawai tayi ta hada bamm ke da jikarki Badiyya?? Ai ko zanje ko nawa ne in bada in ceto ta daga shiga wuta, ai ba kyau ace ina aljanna ita tana wuta, er uwata ce uwar mu daya ubanmu daya" Maheer dai bai ce ma Mama Ladi komai ba ya zaunar da Mayraah gefen gado yana kallonta cikin sanyin murya yace "Ki jira ni a nan" Ta gyada masa kai tana kallonsa ya juya ya fita, makullin kofar ya cire bayan ya fita ya kulle kofar ta waje, Mama Ladi ta rushe da kuka ta ajiye bread din hannunta tace "Toh nace masa mu tafi karayen dake yace zaki yi jarabawa, to shi jarabawan baza a iya kai maki karayen kiyi ba?" Ita dai Mayraah kallonta kawai take babu ko kiftawa amma bata ma san me take cewa ba, Mama Ladi tace "Toh ma jarabawan banza ba sai da kwanciyar hankali ake jarabawa ba, su ajiye maki duk randa kika dawo a baki kiyi mana, bari kawai in gama karyawa ya bamu kudin mota mu yi wucewar mu, ranan laraba da juma'a kadai Malamin ke shigowa karaye yafi zama a Maradi" Maheer na zaune parlon Abba tare da Usman ta dalilin kiransu da Abban yayi, they've never seen their father this angry kamar ba shi ba, he was really vibrating and raising his voice kamar zai ari baki, rai bace ya ci gaba yana cewa "In ma ta zauna gidan nan da Mayraah ko ta tattara ta tafi duk inda zata tafi i don't care, bata isa tace Mayraah bazata zauna a gidana ba, i am not tolerating that nonsense again, all this while na kauda kai nayi hakuri na bi su a yanda suke so, ba wai don ban san abinda nake bane, yanzu kuma babu wanda ya isa ya canza min tsarin gidana, Mayraah will keep on staying as comfortable as she was before in this house, babu wani wanda ya isa ya canza haka, duk wanda bazai zauna ba ya bar gidan" Daga Maheer har Usman were quiet, bude kofar parlon aka yi Ammi ta shigo, duk tana jin abinda Abba ke cewa tun daga part dinta cause he was raising his voice so high, tayi wani murmushi tana kallonsa da kyau tace "Ai ba sai ka zaunar da su kana ci min mutunci a gabansu akan Mayraah ba Mahmud, ga ku ga ta ai kai da 'ya yan ka sai ku zauna da ita ni kuma zan bar maku gidan" Abba yace "Ai ban hanaki tafiya ba, so ki tafi duk inda zaki, sai yanzu na kara fahimtar ke da iyayenki ba kwa son gaskiya, i repeat in dai kan Mayraah ce ki tafi duk inda zaki, she remains in this house tunda gidana ne nan din ba gidan uban kowa ba" Juyawa Ammi tayi ta fice daga parlon, Maheer ya ji kansa ya sara, Usman was also short of words, Abba na kallon Maheer strictly yace "Duk kayan Mayraah da ka kai gidanka ka kwaso ka dawo mata da shi gidan nan" Maheer yayi kasa da murya a hankali yace "Abba ku yi hakuri abun duk bai kai haka ba, yanzu Mayraah tana bukatar nutsuwa sosai, her final exams is in just 2 weeks time, i think it will be better ta zauna hostel don tayi concentrating...." Shiru yayi don gaba daya ya ma rasa yanda zai yi composing word din yanda zai yi making sense a kunnen Abba, bazai so ace Ammi ta bar gidan akan Mayraah ba, the issue is just taking another dimension, Abba yace "A gidan nan nace zata zauna ba hostel ba, all this years ai ba a hostel take karatun ba...." Usman ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya yana kallon Abba yace "Abba wannan final exams ne, she needs all the concentration, with what is happening now bazata samu nutsuwa ba, plss ka bari ta zauna hostel har after the exams, it's just for 3 week" Usman ya fadi haka ne shi ma saboda exactly tunanin da Maheer yayi shi ma yayi, it won't make sense Ammi ta tafi saboda Mayraah, Strictly Abba yace "Nace baxata zauna a hostel ba a gidan nan zata xauna tayi exams dinta" Duk suka yi shiru suna kallonsa, ya juya yayi wucewarsa daki, mikewa Usman yayi ya fita daga parlon, Maheer ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, gaba daya ya rasa tunanin me zai yi. A hankali Maheer ya bude kofar dakin Mayraah ya shiga, tsaye ya ganta bakin kofar dakin, Mama Ladi ta mike tace "Kai ya zaka kulle mu a daki kamar barayi kayi tafiyarka, sannan anya baxa ka duba ƙwaƙwalwar yarinyar nan ba tunda dae naji ance kai likita ne, tun daxu fa nake mata magana yanda kasan da bebiye nake, ni wallahi ta ban tsoro kawai dakewa nayi" Maheer ya tafi dakinsa da Mayraah, after letting her sit, ya duka gabanta a hankali yace "Kina ji na Mimi" kallonsa kawai take, yace "Do you have any frnd or Coursemate dake hostel?" Mayraah tayi shiru tana kallonsa, yace "Say something Mimi" Ta gyada masa kai, mikewa yayi yace "Abba zae maki magana, tell him hostel kike so ki zauna for ur final exams" Daga haka ya tafi Parlon Abba tare da ita.... A tare Maheer da Usman ke kokarin su yi convincing Abba to let Mayraah be in hostel har bayan exams dinta, Abba ya nuna sam bai amince ta je wani hostel ba, ita dae Mayraah na zaune parlon duk tana jin su, Abba yace "Kuma kada wanda ya sake kawo min maganar hostel" Sae a sannan Mayraah ta daga kai tana kallon Abba cikin sanyin murya tace "Abba dama a can nake so in zauna inyi exams din, many of my Coursemates are also coming back to hostel till the final exams, i will concentrate more" A ranan da yamma Maheer ya maida Mayraah hostel nan kusa da makarantarsu bayan yaga Abba ya fita daga gidan don Abba na iya cewa sae ana gobe exams, shi kuma tun da Ammi ta fita gidan da safe hankalinsa yayi mugun tashi kwata kwata bai so abun ya kai haka ba, tare Mayraah zata zauna da kanwar wata colleague dinsa wajen aiki, ita yarinyar tana level 200..... ya sauko mata da duk kayanta da zata bukata tana kai wa cikin dakin sabuwar roommate din nata tana ajiyewa, all this while Maheer na tsaye jikin mota yana bin ta da kallo, kawai tausayinta yake ji har cikin ransa, he wish he can't take away all this sad moment for her, handbag dinta ta dauka lastly a motarsa, a hankali yace "Mimi" bata yarda ta kallesa ba, nan da nan yayi noticing hawayen dake makale idonta, dawo da ita yyi jikin motar yace "Mimi i trust baxa ki ce zaki je ko ina ba shi yasa na kawo ki nan, i trust you Mimi, i know 24/7 karatun exams dinki za ki yi a nan because ur 5 years over everything for now, pls Mimi do not betray my trust, kar ki bari zuciyarki yayi leading dinki zuwa yin abinda bai kamata ba, Ammi and Abba are still ur parent, we are ur brothers, in sha Allah all this will come to pass very soon, ki cire komai a zuciyarki kiyi concentrating kan exams dinki to make Abba and Ammi proud, kinga da kyar muka shawo kan Abba ya yarda ki dawo hostel idan wani abu ya sameki a nan mu Abba zae yi blaming, mu kuma muna son ki maida hankali ne yasa muka ce ki dawo nan, duk sanda kike son wani abu just give me a call.... Usman is on his way now with ur foodstuffs" ko rufe baki bai yi ba sae ga motar Usman, bayan yayi parking Maheer ya nufi motar tasa, ita dae tana tsaye tana kallonsu, babu abinda
Chapter 109 · 0% Book details