← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 313

Sashe 137

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

"Aa ban san komai ba wallahi, wani sabon abun ya faru ne bani da labari? Ke ni fa ba yarinya bace Mariya da zaki kawo min raini zan ci uwarki la'ada waje wallahi, shi kansa Mamudan sai da ya tambayeni yace amma zan kwana biyu kafin in koma ko, nace masa to tunda yace haka bari in zauna zuwa kwana biyun kuma shine zaki zo min da rainin wayo da maganar banza, ina ruwanki da sabgata, gidan uwarki ko gidan mijinki?" Ajiye akwatin Aunty Mariya tayi ta fice daga Parlon ta bar gidan, Mama Ladi tace "Yau naga fitinanniyar yarinya kai, haka zan kama hanya in tafi in bar Ammin cikin wannan damuwan bazan zauna in dinga kwantar mata da hankali ba, sannan ga maganganu cike cikina da zan gaya mata game da tsinanniyar surkarta warce ni da kaina zan ja Hajja mu je gidan Mashir din da sassafe bayan na laka ma Hajjan karya Sanisar bata da lafiya rai a hannun Allah daga nan zan turketa ta fadi mugun abinda tayi da bakinta dama ga turarena da kasko na taho da shi a jaka, to ga dai na kishiya ya tabbata ko daga nan ai bai kamata a dinga shashantar da lamarina ba, ni ba boka nake bi ba Malaman gaskiya da suka san addini nake mu'amala da" Mama Ladi ta kare tana huci ta jawo bowl din fruit dinta tana sha..... Throughout ranan sai bayan magrib Maheer ya shigo gidan tun da ya fita da Haseenah da Badiyyah, dawowar da yayi yanzun ma don Ammi ta kirasa yafi sau uku tana son ganinsa ne amma da bazai zo ba, yana shigowa parlor ya tadda Mama Ladi da Hajiya Amina zaune parlon ga malmalan tuwo biyu a gabanta da miyan vegetable da yaji nama, Maheer ya karasa ya gaishesu, Hajiya Amina ta amsa, Mama Ladi tace "Ta zubo maka tuwon ne kai ma?" Maheer yace "Aa ai daga gida nake" Sama ya haura, direct ya nufi bangaren Ammi, zaune ya ganta a Parlon da Usman da Umar, alamar dai shi kadai ake jira, zaunawa yayi don tun dazu sun hadu da Umar a gidansa, sai da ma Usman ya fara kai sa gidansa har suka sanar masa abubuwan dake faruwa kafin su taho gida tare da Usman, a hankali Maheer ya gaida Ammi yana kallonta, duk wanda ya ganta yasan ta ci kuka ba na wasa ba ranan, Maimakon ta amsa gaisuwarsa sai cewa tayi "kun san dalilin kiranku nan?" Duk suka yi shiru suna kallonta, Banda Usman da kansa ke kasa, Ammi tace "To kun ga Mayraah?" Sai a sannan Usman ma ya daga kai yana kallon Ammi, ta girgiza kai as if counting her words tace "Babu ku babu ita har abada, ko magana ya sake hada ku da ita ban yafe maku ba, you 3 should just assume baku taɓa saninta ba, baku taɓa rayuwa waje daya da ita ba" Gaba dayansu kallonta suke babu ko kiftawa, da wani expression Umar yace "How Ammi? It's not her fault all this happen...." Tsawa Ammi tayi masa tace "Questioning dina zaka yi?" Yace "No, amma bai kamata ki ce haka Ammi ba, ni har yanzu zuciyata bata yarda ba ke ce kika haifi Mayraah ba to be sincere" Ammi ta mike tana kallonsa da kyau tace "To ba ni ce na haifeta ba Umar gashi ina gaya maka da kaina yanzu, ban hada komai da ita ba, don haka ina sake jaddada maku ko gaisuwa ya kara hadaku da Mayraah wallahi ban yafe maku ba gaba daya, sannan har yanzu ina kan bakata bazan zauna gidan ubanku ba, it's better ku samar min gida in koma don gidan Hajja ma bazan je ba" Tana kai wa nan ta shige Bedroom dinta.
Chapter 137 · 0% Book details