Sashe 166
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
kai ta Dr?" Ya kalli Mayraah dake tsaye ta kasa cewa komai yace "Ki taho da ita asibiti can Abuja" Daga haka ya shiga motar da likitan suka zuwa cikin Abuja, Mayraah har gajiya tayi da lallashin Maman Hanan a hanya har suka karasa Abuja, bata mance sunan asibitin ba wanda is so popular duk da asibitin masu kudi ne, suka hau adaidaita sahu ya kai su har asibitin, Sun fi minti ashirin zaune a katon reception din hospital din, bakaken fata da fararen fata sai kai koma suke a reception din, everywhere is just so organized kamar a kasar waje, suna kuma da lokacin zuwa duba mara lafiya ba anyhow ake shigowa ba, Mayraah ta kalli Maman Hanan for the countless time tace "Maman Hanan kiyi hakuri da kukan nan addu'a kawai za kiyi mata, in sha Allah zata samu lafiya kin ga nan babban asibiti ne" tausayinta kawai Mayraah take don ta san ko da an kwantar da Hanan to ko ita baza a bari ta zauna da ita ba sbda infection din is contagious, don su inda ake kwantar da masu cutar ma daban ne ba kowa ke shiga ba sae ma'aikatan asibitin, After another 20 minutes wata nurse sanye da cute uniform dinta ta nufosu tana kallon Mayraah da turanci tace likita na bukatarta a office, Mayraah ta mike tana kallon nurse din ita ma da turanci ta tambayeta ina office din, Nurse din tace "First floor, office number 1, Dr Khalil" Mayraah tace "Ohk" Maman Hanan ta mike da sauri cikin rawan murya tace "Tare za mu je?" Mayraah tace "Aa ki jira yanzun nan zan fito ai" Daga haka ta wuce sama ta isa har office number din da nurse din tace mata tayi knocking, sai da aka mata izini ta shiga, the office was large and organized, ko ina fes fes ga Ac a kunne, yana zaune kan office chair dinsa ya canza kaya alamar har yayi freshen up, ta karasa har front din table din ta zauna tana kallonsa tace "Dr ya jikinta?" Ya kalleta yace "Ina mance sunanki, pls remind me" A takaice Mayraah tace "Ilham" Yace "Ilham, how did u know it's Diphtheria?" Ta ɗan buda ido thinking of what to say sai kuma da sauri tace "Na taɓa koyon aiki a wani karamin asibiti" Yace "Really, kina da experience kenan in haka ne" Ta ɗan yi murmushin karfin hali bata ce komai ba, yace "Kin samu hostel din?" A hankali tace "Aa ina wajen aunt dina a suleja" Yace "What about ur parent" Tayi shiru tana kallon sa, kawai ta samu kanta da cewa "They are late" Ya ɗan sauke kansa sai kuma yace "Allah ya ji kansu" Tace "Ameen" Yace "But idan baki samu hostel ba ai akwai off campus da zaki samu cikin gari, isn't suleja too far for you? Yayi nisa fa zuwa school din" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yayi shiru da ya tuna ba fa kowa ake haifa da silver spoon ba barin ita da tace iyayenta sun mutu, probably bazata iya affording off campus ba, can yace "Wani course aka baki admission yanzu?" Mayraah ta rasa ma me zata ce masa, can dai "Microbiology" Ya gyada kai yace "That's good, i guess ur Aunty isn't financially stable ko?" Nan ma kawai tayi murmushi, ya sauke ɗan ajiyar zuciya yace "Mu kinga nan ba a daukan health workers sai da Qualified medical certification, infact ba mu da vacancy ma yanzu haka, we are dealing with just qualified medical staffs don wasu daga likitocin mu ma turawa ne da indians, so i will see if it will be possible in san yanda zan yi inyi attaching dinki ko during weekend ne as an auxiliary Nurse don ki samu ki dinga fending for ur self kar ki sakar ma mutane burden dinki su gaji da wuri" Mayraah kallonsa kawai take da mamaki and she couldn't believe her ears, aiki a babban asibitin nan?? can tace "Zan ji dadi idan ka min haka" Yace "But fa dole sai ta bayan gida zan yi maki wannan abun don we have strict orders a asibitin nan...." Mayraah tayi shiru tana kallonsa, Calmly yace "Kar ki damu, i will try my best zaki fara aiki a nan in sha Allah" Cikin sanyin murya tace "Toh Allah ya sa, but i am sorry about that admission da nace na samu da naje makarantar ba haka bane" Yace "I don't get you" Ta sunkuyar da kai tace "An ban admission din da dadewa ne, sai yanzu muka tara kudin makarantar ban san ashe ba a haka ba, da naje makarantar shine suka ce anyi cancelling admission din long ago" Yace "Subhanallah" Daga haka bai sake cewa komai ba, ita dai kallonsa kawai take, yayi kasa da murya yace "Kar ki damu Ilham, zaki fara aiki a nan, and the salary is good sai kiyi ta saving ki sake sabon jamb ki nemi wani admission din" Ta ɗan yi murmushi tace "Toh Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi" Yace "Ameen" Da sauri tace "Plss ya jikin yarinyar??" A hankali yace "She is late already, before we could do anything" Mayraah da gabanta ya fadi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Yace "Ya ku ke da matar?" Nan da nan hawaye ya kawo idon Mayraah tace "Neigbor dinmu ce a Suleja" Yace "Sai hakuri, yarinyar ta rasu" Ta masa wani kallo tace "Shine tun dazu baka gaya min ba??" Mikewa tayi tana share idonta ta nufi kofa yace "Wait Ilham" Ta juya ta kallesa yace "Ce mata za kiyi nace ta bada number baban yarinyar ita kuma ku tafi gida a kawo ma yarinyar abinci, so i will communicate with the father, bama son ta hada mana commotion a nan" Cikin sanyin murya Mayraah tace "Sai dai nurses din su gaya mata ni bazan iya ba" Ya dau waya yace "I will tell dem now" Kiran nurses din yayi downstairs, Mayraah kuma ta fita a sanyaye.