← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 313

Sashe 151

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fa kawai hakuri za kuyi ayi sulhu Fauziyya, don yanzun nan wani officer da nake jin nauyinsa don gaba ma yake da ni gun aiki kawai dai na fi sa sanin Officers dinmu ne ya bugo min wai surkar abokinsa ce ita matar da yan sandan suka kama, yana kuma neman alfarman a rufe case kawai aje gida ayi sulhu" Hajiya Fauziyya na huci tace "Ban gane ba Abban Ikram, kana nufin an doki er mu an fasa mata kai a banza kenan? Wai kai kaga uban raunin da ta ji mata ne kuwa? Ko don ban dauka a hoto na turo maka ba?" Yace "Na dai gaya maki, ayi hakuri a je ayi sulhu don gaskiya ina bala'in girmama Mutumin nan kuma ina jin nauyinsa, don haka ni har na kira Dpo din division din nace masa a saki matar kawai....." Cikin daga murya Aunty Fauziyya tace "In mun yarda shegiya nake, in mun yarda Allah ya tsine mana, wallahi baza mu yarda ba, a tura mu kotu kawai alkali yayi mana Shari'a...." Katse wayarsa yayi, Aunty Farida tace "Lallai Baban Ikram, a saketa fa yace??" Aunty Fauziyya na huci tace "Kyaleni da shi kawai, a tura mu kotu a kwatar mana hakkin er mu kawai, babu wani sulhu da za ayi a gida, idan ko ba haka ba idan ban kira Yaya Abdurrahman soja an kai Badiyyar barikin sojoji ba sun kakkarya mana shegiya ku ce ba ni bace......." Haka Ammi ta dinga yawon police stations tana neman Hajja, in ta hau wannan adaidaitan ta sauka ta hau wannan a haka dai har Allah ya kai ta division din da aka kai Hajja, Hajja na zaune gaban yan sandan sai zare ido take, tana hango Ammi ta fashe da matsanancin kuka, Ammi ta nufeta ita ma ta fara kuka, wata police woman tace "Ku tun dazu an kawo tsohuwar nan station amma babu wanda ya biyota kamar bata da gata kusan awa biyu kenan......" Ammi na kallonta cikin kuka tace "Tun dazu na fito wllhi, nayi ta duba stations don ban san wanda aka kawota ba, da muna gidan ai sai dai ko ni a tafi dani baza mu bar haka ta faru ba" Police woman din ta taɓe baki tace "To za ku iya tafiya kawai an rufe case din, wai ku je gida ku sulhunta kanku" Ammi tace "Toh mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Ammi ta kama hannun Hajja dake kuka har sannan saboda takaicin wai yau ita ce a motar yan sanda har police station, adaidaita sahu Ammi ta samar masu, ta dinga bata hakuri amma Hajja ta ki daina kuka don kamar ma dada tunzurata take, cikin rawan murya Hajja tace "Kar ma ki maida ni anguwan nan don yanxu ban san da idon da zan kalli yan anguwan ba wannan abun kunya har ina? Da tsufana da mutuncina a min wannan cin mutuncin Ammi, wallahi ko yarinyar nan kadai ta rage a duniya Maheer bazai zauna da ita ba" Ammi ta rasa ma me zata ce jin furucin Hajja na cewar kar a maidata gidanta, to yanzu ina zata kai Hajja, da ace da ne dama gidanta kawai zata tafi da ita amma yanzu ba da bane, tunanin hakan yasa hawaye ya kawo idon Ammi ta rasa tunanin da zata yi kuma, tana kallon mai adaidaita sahun kawai ta gaya masa unguwan Maheer tace "Can zaka kai mu kawai" kafin su karasa ta kira Maheer, yana dagawa tace "Kana ina ne?" Maheer da har a sannan ya kasa motsi yana rike da takardan da Abba ya basa cike da karfin hali yace "Gida" Ammi tace "Wani gidan, mu gashi muna hanyar gidanka da Hajja yanzu tace bazata koma gidanta ba, ya za ayi da makulli?" A hankali yace "A bude gidan yake" Ammi ta katse wayar, wato bazai ma tambayeta ya aka kare ba, a haka suka isa gidansa ranta a bace, babu wanda ya nuna concern din abinda aka yi ma Hajja daga shi har uban nasa, suna shiga parlon Hajja ta zauna kan kujera ta fashe da sabon kuka, cike da damuwa Ammi tace "Don Allah kiyi hakuri Hajja" Cikin kuka Hajja tace "Ni abinda ya ban takaici da aka ki bin ba'asin ma abinda ya hadasu tun asali, wllhi da muka shigo nan da Ladi shake Badiyyah matar tayi tana neman kasheta har Allah ya ba Badiyyar sa'a ta bugata da bango, da kuma Badiyyar bata yi haka ba da ta dade da mutuwa a hannunta wllh, yanzu da ita matar ce ta kashe Badiyyar sai ace yaya? Ban shiga uku ba idan hakan ta kasance me zance ma dangin ubanta daga sun bar min amanar yarinya? Ashe matsiyaciya ce matar Maheer duk bamu sani ba tace Mayraah kaza, Mayraah kaza, Mayraah ta zageta, Mayraah ta ci mutuncinta, Mayraah ta tara mata kawaye a gida ita da kawayen su yi ta shewa, bayan ni dai nasan ba tarbiyyar da muka yi ma Mayraah ba kenan, yarinyar da kowa ya shaida nutsuwarta amma azzalumar matar nan ta dinga mata sharri tana kawowa kunnenmu, to wallahi Maheer ya gama zama da ita har abada kuwa, muna zaman zaman mu lafiya ta shigo ta tarwatsa mana Pamily, ta lalata komai, ashe ita ce ibilishiyar cikinmu daga aurota ko wata uku ba ayi ba ta tarwatsa komai, idan an bibiya wllhi ita ta dinga zuga Badiyyar ma take ta kawo wasu mugayen maganganu kan Mayraah, don da ai ba haka Badiyyah take ba, to yaushe ma ta zauna dindindin a kano balle ta shiga sabgar Mayraah har tace ta mata wani abu, tsakaninsu fa gaisuwa kawai ba wani shiga harkan juna suke ba duk mun sani, suna zaune lafiya kuma, Tun a sannan sai abun yayi ta daure min kai don nasan Mayraah dai da na sani a baya ba haka take ba, amma sai nake tunanin canzawa tayi kawai don ta gano ba mune asalin jininta ba bari ta gwada mana halin ɗan Adam, ashe shegiyar matar Maheer din nan ce duk ta hada komai, duk ita ce ta hada fitinar nan ta rikita mana komai, to da yake Allah me gafara ne sai gashi cikin gaggawa asiri ya tonu tun bamu shiga hakkin Mayraah ba, to wallahi sai Maheer ya saki annobar nan, ya rubuta mata takardanta kawai a gadon asibitin ya bata ba sai ma anje da nisa ba, a duk duniya babu cin mutunci da ya wuce wanda dangin Haseenah suka min yau don har in koma ga mahaliccina bazan manta ba wallahi, da mutuncina da girmana wai yau ni aka saka cikin motar yan sanda" Tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka ta ci gaba tana cewa "Wai fa a haka Allah ya rufa mana asiri an dauke Mayraan daga nan gidan bata kasheta ba, a yanda naga ta shake Badiyyah wllhi zata iya kisa matar, Allah dai shi yasan dalilin faruwan komai wallahi" Ammi dai kanta na kasa duk tana sauraron Hajja, lokaci daya hawaye ya kawo idonta, Hajja na share idonta tace "Duk ma abinda kika ma Mayraah ai er ki ce halaq malaq babu me ce maki don me tun da ba shi ya maki rikonta ba ya sha wahala da ita har zuwa yau, kuma 'ya bata fushi da uwarta koma me zata mata dole dai uwarta ce bazata canza haka ba, nakudarta ne kawai baki yi ba amma babu wanda ya kai ki sanin zafinta, ba kuma wanda zai nuna maki ya fi ki sonta daga 'ya yan naki har uban nasu, shi kuma Mamuda dama can da niyyar aurensa kece kawai baki sani ba, a yawace yawacensa ya samo Bazawararsa suke tadi ke kina gida kin saki baki, shine da ɗan matsalan nan ya faru yayi maza ya aureta ya fake da matsalar, ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba yana da niyyar auren ya dai rasa yanda zai gaya maki ne, ni fa ba yarinya bace" Ita dai Ammi bata ce komai ba kuma har sannan bata dago kanta ba, hawaye kawai ke zuba idonta, Hajja ta cire dankwalinta ta share hawayen fuskarta tace "A samo min ruwan zafi in je inyi wanka in hadiyi panadol, wallahi duk jikina ciwo yake" Ammi taji baza ma ta iya shiga kitchen din ba, banda lalura me zai kawota gidan matar Maheer har ta zauna, rabonta da gidan tun ba a gama gini ba almost a year ago da ya kawota ta gani, ta dau wayarta ta mike ta fita balcony hawaye na sauka idonta ta sake dialing number Maheer, yana fara ringing ya daga, sai da tayi controlling kanta sannan ta iya cewa "Ka taho da Mayraah" Duk da Maheer ya ji ta ya kasa ce mata komai, kuma yana dai dai gate din gidansa ta kirasa, bude gate din yayi Ammi na ganinsa ta katse wayar, zata juya ta koma parlor kira ya sake shigowa wayarta ta duba taga Abba ne ke kiranta, sai da gabanta ya fadi don wata daya kenan rabon da kiransa ya shigo wayarta, ta daga kiran ta kai kunne ba tare da ta ce komai ba. Abba yace "Na kira ne in sanar maki burin ke da danginki ya cika a kan Mayraah, You and ur relatives have succeeded into pushing her, dama duniya ae kuke so ta shiga ko? To hakan ya faru sai ku zuba ruwa ƙasa ku sha..... amma ina son ki sani, idan wani abu ya samu yarinyar nan a duk inda take bazan taɓa yafe maki ba, i will never forgive u, duk halin da ta shiga ke da danginki ne sila saboda selfishness dinku, alhaki a kanku kuma ina me tabbatar maki Allah bazai bar ku ba....." Abba na kai wa nan ya katse wayarsa, Ammi dai ta ƙame a inda take tsaye as if trying to assimilate all what Abba is saying, after few second da katse wayar da Abba yayi ta juya a hankali tana kallon Maheer da ya iso balcony din, Har a lokacin bata cire wayarta a kunne ba, tana kallon Maheer ko kiftawa babu cikin karfin hali tace "Ina Mayraan?" Maheer bai yarda sun hada ido da ita ba ya mika mata takardan hannunsa, Ammi ta amsa da sauri tana duba takardan,
Chapter 151 · 0% Book details