← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 313

Sashe 64

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

kamar zata shige jikinsa tana kallonsa kamar mayya, ya kamo hannunta yace "What will we be taking for lunch" tana shafa beard dinsa tace "Abinda Babyna ya fi so" Yace "Ko muje eatry mu siya abinci?" Ta juya ido tace "Sure dear" Yace "To shirya mu tafi" Hijab dinta har kasa ta saka kan kayan jikinta sannan suka bar gidan, dama bai shigo da motarsa ba a waje yayi parking, duk ita ta zabi abinda za su ci, bayan sun bar eatry din yace "Zan biya gidansu Ahmad in bashi sako" Tace "Ohh bai koma Abujan bane shi?" Yace "Aa ya koma, kaninsa yace in ba zai je Abujan gobe" Tace "Ohk" Suna kusa gidan Haseenah ta kallesa tana murmushi tace "Kamar in shiga gida wllh" Murmushin yayi shi ma, don dole sai ka wuce gidansu kafin ka karasa gidansu Ahmad a layin gaba, saboda yawan zuwa gun childhood frnd din nasa da yake yi ne ma suka hadu da ita a unguwan, yana isa dai dai gate din gidansu yace "Ko zaki shiga ki gaida su Mumy kafin in dawo daga gidansu Ahmad din?" Ta zaro ido tace "Kai Baby dama ana haka?" Yace "Why not, ai kamar yanda kike yawan fada yanzu muna era din civilization and modernization" Tayi dariya tace "Kuma haka ne, to in ka dawo sai ka kirani in fito, amma fa zan ji kunya" Yana kallonta yace "Ba wani kunya baby, ki gaida su Mumy" Bude motar tayi tace "Alright sweet, amma kar fa ka dade don Allah" Yace "Ina mika masa zan juyo ai, kece ma zan ce ma karki ki fitowa da wuri ki shanya ni a nan" Ta sauka daga motar tana dariya tace "Haba ai ni bana ma sha'awan zaman gidan namu yanzu tunda na dandani zaman gidan ka, ae gidan miji daban ne" Kulle masa motar tayi tana masa kallon kauna tace "Sai ka dawo my hubby" Yace "Ohk, but ji mana" Har ta fara tafiya ta juyo tana kallonsa, ya gyara zamansa yace "Go inside and explain to ur parent where u lost ur virginity cause u didn't bring it to my house, after that they should do better akan tarbiya da manners din da suka baki don ya maki karanci, idan kin masu bayanin na farkon wanda shine main issue a nan, sa iya nemana in saka masu convenient lokacin da zan zo su min bayanin da kansu, that is idan ina da lokacin ma kenan, sannan a dawo batun rashin tarbiyyarki da manners dinki, wannan kuma ban san for how long zae dauka a koya maki ba, though my main concern ynxu is how and where u lost ur virginity i really want to know that from ur parent daga nan ne zan iya deciding fate din aurenki a kaina..... ita warce kika kira tsintattciya mara asali i can swear with my life virgin ce, she is intact, cause she is my mum's training, she is my training, i raised her since from when she was a toddler, kin ga kuwa ba standard din ku daya ba" Yana kai wa nan ya tada motarsa yayi zoom off ya bar ta tsaye a ƙame a wajen kamar statue ko kifta ido bata yi.
Chapter 64 · 0% Book details