← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 313

Sashe 131

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.* [7/10, 9:17 PM] Khaleesat Haiydar💖: Duk yanda Hajja ta bi da Mama Ladi a kan kar ta bi su Ammi gida ƙin yarda tayi, don bata sake sauraron Hajjan ba ta sake fita da akwatin nata zuwa motar Maheer tana cewa "Ji min tsohuwa dai, to wajenki na zo da zaki ce min sae na zauna wajenki, bayan ni nasan me ya dawo da ni, ko kin zata yawon banza na zo yi Kano, kina zaune kara zube babu neman taimako babu komai sai surutu da isa da gadara, gashi da hannunki da bakinki kina neman tarwatsa zuri'arki" Bayan fitar Mama Ladi Aunty Mariya na kallon Hajja da ta cika tayi fam, ita a dole Mama Ladi baza ta bi su gidan Abba ba, Aunty Mariya tayi kasa da murya tace "Ae kafata kafarta Hajja baza ta zauna gidan ba in sha Allah, ko awa daya baxa mu yi a gidan ba za mu dawo nan tare da ita, haba ai yanzu kuma ba da bane da za ayi hakan" Ita kanta Aunty Mariya sae da taji wani iri da kalmarta na karshe, su kuma baxa su gane ma'anar yanzu ba ɗa bane da ta fada, Ita dai Ammi taki cewa komai a parlon amma sam ita ma bata son Mama Ladi ta bi su, shikenan ita danginta basu da zuciya kenan, me ma zai kara burgesu da gidan Abba, me Mama Ladi zata bi ta gidan su yi after all this that happened, Maheer dama bai bi ta kansu ba ya dinga danna wayarsa daga tsayen da yake kamar baya jin ma me suke cewa, haka kawai baza a dinga daura masa pressure daga wannan sae wannan ba, A fusace Hajja tace "In ban da ma rashin zuciya me kanwata zata sake koma yi gidan Mamuda, mutumin da har yau bai sake bi ta kanmu ba, wallahi in nace maku nayi farin ciki da dawowar Ladi garin nan to nayi ma Allah karya, sam bata da hankali bata da zuciya bata san inda ke mata ciwo ba, ta wani kwaso rubabben akwatinta ta kara dawo mana to me za mu mata??" Aunty Mariya dai tace "Ke dae Hajja kawai ki bar ni da ita nasan yanda zan bi da ita in sha Allahu" Aunty Mariya na kai wa nan ta mike ta dau handbag dinta, Hajja ta kalli Ammi tace "Ki tashi ku je Allah ya tsare" Ammi ta mike ta dau karamin jakarta tace "Ameen" Sai a sannan Maheer yayi ma Hajja sallama ya juya ya fita daga parlon, Mama Ladi na tsaye jikin mota tana ta jiransu sai ga shi sun fito, Mama Ladi tace "A saman motar za a daura akwatin Maheer?" Ya ɗan yi murmushi ya bude mata booth yace "Ai nan ba karaye bane da ake daura akwati a saman mota" Mama Ladi tace "Ƙul ɗan nan, wllhi karayen nan ba kauye bace" Shi dai bai ce mata komai ba ya dau akwatin karfen ya saka bayan motar ya bude mata kofar baya, ta shiga sannan Ammi ma ta shiga, Aunty Mariya ta shiga gaba, sai da suka bar layin Mama Ladi ta sauke wani ajiyar zuciya me karfi tace "Maganganu dai sanka sanka, babu dadin ji.... huhuhu" Babu wanda dai ya tanka Mama Ladi a motar, can ta kara sauke ajiyar zuciya tace "Mutum ba kyau, ku ji tsoron mutum, amma dai ba komai Allah ya kai mu gidan lafiya" Maheer na kusa gida duk jikinsa yayi sanyi, bai san yanda Ammi zata dau wannan lamarin ba, bai san yanda zata yi reacting ba, ita kanta Aunty Mariya tayi nisa tunanin da take, ita dai tasan koma meye bazata yarda ta bar Ammi tace zata sake barin gidan ba, she just have to let her stay by all means, tsoronta yanzu Mama Ladi tunda ba alkibla gareta ba kar ta kara ɓata abun ta rikita komai, Maheer yayi parking bayan mai gadi ya bude masu gate din gidan, nan bugun zuciyarsa ya fara tsananta, baya ma tunanin zai zauna gidan bayan ya ajiye su gwara kawai ya bar gidan duk ma abinda za ayi ya kasance baya nan, he is just tired of everything, ya kashe motar, Aunty Mariya ta fara sauka sannan Ammi, Mama Ladi ma ta sauko tana kallon Maheer tace "Fiddo min da akwatina Maheer, abubuwan ciki ba na wasan yara bane" Maheer ya bude booth din ya sauko da akwatin nata, Aunty Mariya da gabanta ke faduwa ita ma ta kalli Ammi da ta tsaya kamar tana jiran Mama Ladi tace "Ammi mu shiga akwai rana kamar ba safiya ba" da fara'a Ammi ta amsa gaisuwan Mai gadi da ya taho yana gaisheta cike da girmamawa, sannan ta bi bayan Aunty Mariya zuwa cikin gidan, Mama Ladi na biye da su a baya, shi dai Maheer na rike da akwatin Mama Ladi yana tafiya a hankali, Aunty Mariya na shiga parlon Ammi taga Haseenah da Badiyyah zaune parlon ko kadan ganinsu bai mata ba, Ammi ta karasa cikin Parlon ita ma, Haseenah na ganin Ammi ta zamo kasa daga kan kujera tana sinne kai tana ma Ammi sannu da zuwa tare da gaisheta, Ammi ta amsa da ɗan fara'arta, Haseenah ta gaida Aunty Mariya ma, Aunty Mariya ta amsa, Badiyyah ma duk ta gaishesu, Mama Ladi ce ta shigo parlon ta gwale ido tana bin ko ina da kallo tace "Nan gidan ne kuwa naga kamar ba nan ba fa, ko idona ne? auuu kamar dai fenti aka canza da kujerun gidan fa" Aunty Mariya na kallon Ammi a sanyaye tace "Ina makullin part din ki Ammi?" Ammi ta mika mata handbag dinta, Haseenah dai sai wurga ido take kamar warce tayi ma sarki karya, Mama Ladi ta cire gyalenta ta jefar kan kujera tace "Ina Salibar ta kawo min abinda zan ci" Aunty Mariya ta wuce sama jiki duk ba kwari Ammi na biye da ita a baya, Mama Ladi ta bi bayansu tana cewa "Salibar ta kawo min kumallon saman bene kawai, kai amma Mamuda ya kyauta yanzu duk saboda dawowar naki yayi wannan gyaran haka?" Haseenah na ganin sun haura sama ta mike da sauri za ta bi bayansu ita ma taji ance "Me kike yi a gidan nan Haseenah? Da izinin wa kika fito?" Strictly yake tambayar, Haseenah ta juya tana kallon Maheer da ya shigo parlon da akwatin Mama Ladi ta ɗan hade rai tace "Yan gyare gyare na zo taya Ammi mana Maheer, zuwa muka yi ni da Badiyyah mu tayata kaga baxa mu bar ta tayi aikin ba ai" Maheer ya wani hade rai yace "Zo ki fita ki bar gidan nan kar ki tunzura ni, baki da hankali ne zaki kwaso kafa without informing me kice kin zo taya Ammi gyare gyare? To ba a son gyaran naki, sae kece zaki mata gyara aka gaya maki, i am giving u 5 minutes ki bar gidan nan kada ranki ya bace wllhi" Ransa a bace yake maganar, Haseenah ta wani taɓe baki tace "To ai ba don saboda kai na zo ba Maheer, don in ta kai ne ma bazan yi ba wallahi, gani nayi kawai ya kamata tunda Ammi abinda take min ko Mumy sai haka, sannan da hankalina ni ba yarinya bace ba sai wani ya sa ni ba shi yasa na zo kawai, kuma naga Mahaifiyarka ce Ammin nan kyautata mata kawai na zo yi kamar yanda zan yi ma tawa Mahaifiyar, to meye kuma abun tashin hankali a nan" Bata tsaya ta sake sauraronsa ba ta wuce sama da sauri, Badiyyah dai sai tauna chewing gum take tana jin su a parlon, Maheer da yaji zuciyarsa na tafarfasa ya bi bayan Haseenah sama da sauri dolenta kuwa ta bar gidan nan, Badiyyah ta kyabe baki, to ita bata ma ga amfanin biyo Haseenah da tayi ba gashi bata da kudin motar komawa banda haka yanxun nan ma sai ta tashi tayi tafiyarta, ko minti ashirin basu yi da isowa gidan ba amma tun da suka zo basu ga gilmawar kowa ba ga ko ina tsit, har sama Badiyyar ta tafi ta murda kofar dakin Mayraah a hankali ta bude duk da tasan bata gidan, zaro ido tayi ganin wasu tsadaddun furnitures masu shegen kyau cikin dakin, zanin gadon saman katifar ma kadai abun kallo ne ga wani kamshi dake ta tashi a dakin, ko ina na dakin ya canza ya dawo sabo fil kamar na amarya, ga sabbin akwatina da ta gani, a ranta tace to kuma dakin waye wannan haka, har zata karasa ciki ta yi ɗan hali ganin handbag ajiye a dakin sai kuma ta tuna ta fa ga motar Usman a parking space, a hankali ta jawo kofar ta kulle tana tabe baki ta nufi bangaren Ammi ta murda kofa taji a kulle, sauka downstairs tayi tace ma Haseenah ai fa gidan daga Usman sai Abba tunda motarsu ne kadai parking space sai na Ammi da ake kai ta anguwa a ciki, Haseenah na kallonta tace "Kuma bangaren Ammin ba a bude yake ba?" Badiyyah tace "Ai fa kamar ta kulle ne ta tafi da makullin" Ko kadan Haseenah bata ji dadin jin haka ba, amma dai tayi shiru suna ta zaune parlon suna jira, a haka ne su Ammi suka shigo gidan suka same su. Aunty Mariya na bude part din Ammi suka shiga ciki gaba daya har Mama Ladi, Aunty Mariya ta kaƙƙabe masu kujerun parlon suka zauna, Mama Ladi na girgiza kai tace "Mutum mugun icce" Bude kofar Parlon aka yi duk suka juya, Haseenah ta shigo tana ɗan murmushi tace "Ammi akwai abun shara a nan kuwa?" Mama Ladi ta tsuke fuska tace "To sai aka yi yaya in akwai? Don Allah ki rufa mana asiri kiyi tafiyarki za mu share da kanmu, ko ni kadai na isa in share ai" Aunty Mariya da bata ji dadin
Chapter 131 · 0% Book details