Sashe 168
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ur evidence via 07087865788 Mayraah na tsaye gefe wata Nurse tayi ma Maman Hanan bayanin da Dr Khalil yayi mata a waya na cewar ta bada number mai gidanta sannan ta koma gida ta dauko ma Hanan kayan sa wa, ko minti daya Maman Hanan bata kara asibitin ba bayan ta bada number mijinta bata bi ta kan Mayraah ba ta fita da sauri zata koma gida, Mayraah dai ta bi ta da kallo ciki da tausayinta, tana tafiya a hankali ta nufi kofar fita reception din ita ma, Dr Khalil ya sauko downstairs kenan ganin Mayraah zata fita ya bi bayanta har suka fito haraban asibitin yace "Na kira mijin nata suna hanya yanzu haka..." Mayraah ta gyada kai tace "Toh, Allah ya ji kanta, Allah ya basu hakurin rashi" Yace "Ameen, haka yawanci wasu mutanen suke sai yaro ya jigata ake kawo sa asibiti..." Mayraah tace "Na fa shiga gidan ne nayi insisting mu tafi asibiti amma bata da intention din kai ta asibiti don tace mijin ya siya mata magani a chemist" Dr Khalil yayi murmushi yace "Yanzu ina kika nufa?" Tace "Zan koma gida" Yace "Ohk, bari in baki transport naga ko jaka babu a hannunki" Sai a sannan Mayraah ta lura ashe empty handed ta fito, ta kalli Dr Khalil, sai kuma ta fara fidgeting fingers dinta tace "Wallahi ban ma yi noticing haka na taho ba, i was so disturb with the little girls condition" Yace "Sure haka ne, ai kema kin yi kokari" Ya sa hannu aljihu ya ciro 5k yace "Wannan ai zai kai ki gida" Ta ɗan risina ta amsa tace "Nagode sosai" Yace "U are welcome, yanzu idan na samar maki space a nan din how will i communicate with you?" Tayi shiru don ita ko haddace new number dinta bata yi ba, can ta kallesa tace "Ka bani complimentary card dinka sai in kira da number ta, new number ne, bani da shi a kai" Yace "Ohk, zan ba Nurse su kawo maki yanzu, take care of ur self" Tace "I will, thank you" Daga haka ya juya ya koma cikin asibitin ta bi sa da kallo, bayan some minutes sai ga wata nurse ta fito, ta nufo inda Mayraah ke tsaye ta mika mata complimentary card din Dr Khalil, Mayraah ta amsa tayi mata godiya sannan ta juya ta fara tafiya, after minutes walk saboda girman compound din ta iso babban gate din fita haraban asibitin securities din wajen suka bude mata gate din ta fita. Mayraah na komawa suleja taga maza cike kofar gidansu Maman Hanan ana jiran gawarta, mata kuwa sai shiga gate din gidan suke, jikin Mayraah yayi sanyi sosai ta bude nata gate din ta shiga don baza ta iya shiga gidan taga koke koken da ake ba. Mama Ladi na zaune parlon Ammi tana hada mata kwadon salad tana cewa "Ai tunda har yace maki ana bakin kokarin ganin an nemota kawai ki kwantar da hankalinki, ki cire komai a ranki Mamuda bazai maki karya ba tunda ba gantalalle bane shi, sannan yasan manya manyan mutane a kasar nan, ba gashi ana tafiya da Hajja gidan yan sanda ba sai gashi kawai waya yayi ko zuwa caji opis din bai yi ba aka sako Hajja, to tunda yace maki Mera ma ana ta bakin kokarin ganin an samota to muna nan dake zaki ga an samo ta an sakota w mota an dawo da ita gida" Ita dai Ammi kallon Mama Ladi kawai take, Mama Ladi ta gama hadin salad da take bayan ta cika kuli kuli sannan ta tura shi gaban Ammi tace "Kina fara ci zaki ji bakinki sakayau, daga nan kuma komai ma zaki iya ci don buda maki ciki zai yi" Ganin Ammi bata ce komai ba kuma bata dau salad din ba Mama Ladi ta hade rai tace "Ke ni fa na gaji da maki bauta kina maida ni er banza, kinsan inda naje na samo salaq din nan na kwadanta maki kuwa? anguwan naku duk na yaku bayi wani yakunennen salaq suke siyarwa duk ƙasa, sai da nayi tafiya me nisa na samo wannan wllh, duk kwantar maki da hankalin da Mamuda yayi bai ci ace kin hakura kin fawwala ma Allah komai ba, ita fa wannan shegiyar Meran ba yarinya bace duk mun sani, da gangangan ta mana haka kuma wallahi in muka ce baza mu yafe mata ba ta zaunu, don ta wahal da zuciyoyinmu ta cuce mu, ki saki ranki ki ci gaba da harkokin ki in taga kowa yayi banza da ita zata dawo gidan, amma yanzu tasan duk mun damu shi yasa taki dawowa take gana mana azaba" Ammi ta dau salad din ta fara ci a hankali, Mama Ladi tace "To ko ke fa, ga kaji can an kawo an cika a firiji ina jin Mamuda ne yasa aka kawo, anjima sai in farfesa mana muyi ta ci da bredi abunmu bakinmu alekum" Sallama aka yi kofar parlon duk suka juya, Badiyyah ce ta shigo cikin wasu matsattsun dinki ta rataye gyale a wuya hannunta rike da handbag ta karaso har inda suke ta zauna kan kujera tana kallon Ammi tace "Ammi ina yini" Ammi bata sake kallonta ba tana ci gaba da cin salad din hannunta a takaice tace "Lafiya lau" Badiyyah ta kalli Mama Ladi da ta saki baki tana kallonta, babu yabo babu fallasa tace "Ina yini" Mama Ladi ta rike haɓa tace "Sannu jarabar duniya, wato har kin dawo daga yawon tamɓelen naki kenan kamar akuya, shegiyar marainiya annamimiya shedaniya me tarwatsa zumunci, to uwar me ya kawo ki gidan nan ko ance maki Hajjan tana nan ne, baki san hanyar kuturun gidanta bane kika yo mana nan?" Badiyyah ta wani hade rai tana hararanta tace "Ni gaskiya ki daina zagina Mama Ladi, me na maki? Ko meye ruwana da ke daga shigowata zaki fara zagina haka? Wallahi ki dena ina gaya maki" Bata rufe baki ba Ammi na nuna mata kofa tace "Tashi ki fita" Badiyyah ta kalli Ammi da sauri irin bata yi expecting haka ba, Mama Ladi kuwa ta rarumi spatula da ta gama hadin ƙwado ta jefa mata da karfi tace "Tashi ki fita shegiya guzumar banza kawai, shi sa gashi kin doshi arba'in har yau ba mashinshini saboda mugun hali" Badiyyah ta fashe da kuka ta mike ta fice daga parlon da sauri, Mama Ladi na huci tace "Wallahi ni na raina dangin Sanisa in har suka bari Badiyyah ta ci bulus, haka kawai ta fasa masu kan er su har ana hango ƙwaƙwalwa su kyaleta kuma, a ina aka taɓa haka kamar Sanisar bata da gata, ni Allah da na san gidan dangin Sanisar sai in tashi yanzu in je ince masu Badiyyah ta dawo amma in masu kashedi kar su sake cewa za su kama er uwata Badiyyar dai ta dawo su koma gidan za su ganta" Ammi dai bata ce komai ba sai cin salad din gabanta take Absentmindedly. Direct gida Badiyyah ta koma tana shiga parlon Hajja ta zauna kasa ta mimmike kafa ta fashe da matsanancin kuka tace "Dama sai da nace maki bazan je ba kika ce sai naje duba Ammi bata da lafiya, sai da nace maki wallahi bazan je ba kika takurani, daga dawowata kika dameni sai naje duba Ammi to wallahi duk zagina suka dinga yi ita da Ladi wai suke ce min shegiyar marainiya annamimiya, har da ce min na rasa mashinshini shekarata arba'in" Hajja dake zaune tana kallonta tayi kasa da murya tace "Har ita Ammin?" Cikin kuka Badiyyah tace "Ba ita ta fara ba ma ta koreni daga Parlon, ni wallahi kar wanda ya sake shiga harkata babu hadina da su tunda basa so na, idan ba haka ba zan zagi mutum ba ruwana" Hajja dai ta kasa cewa komai amma gaba daya ranta yayi mugun baci, can tace "Ki rabu da su kowa yayi na gari don kansa, amma na Ammi ya fi bani mamaki, ban yi mamakin na Ladi ba tunda ita dama mahaukaciya ce er iska" Badiyyah ta kalleta da sauri tace "Ita ce ma tace in tashi in fita in bata waje fa nace maki, wallahi Ammi ce ta fara" Hajja tace "Kawai tace ki tashi ki fita??" Badiyyah ta fashe da sabon kuka tace "Eh mana" Hajja ta dau wayarta a hankali tace "Kira min Ammin" Badiyyah ta amshi wayar ta yi dialing number Ammi yana fara ring ta mika ma Hajja, Ammi na share parlonta, Mama Ladi kuma na zaune ta daura kafa daya kan daya tana cewa "Kema sai ki ji kin kara jin kwari a jikinki ba wai ki sakar min komai kamar baiwa ba kina zaune gefe daya kan darduma kamar me takaba, ko mutuwa Mera tayi a yanzu ai ya ci ace mun fara saka ma ranmu salama mun fara hakura" Sai da Ammi ta daga kai ta kalli Mama Ladi da ta ci gaba da kallon tv ko a jikinta maganar da tayi, Ammi dai ta ci gaba da sharan ba wai don tana jin dadin jikinta ba kawai Mama Ladi ce ta tilasta sai tayi shara karfi da yaji, wayar Ammi ne ya fara ring, ta mike ta dau wayar Mama Ladi na kallonta tace "Waye?" Ammi tayi shiru at first, sai kuma a hankali tace "Hajja ce" Mama Ladi ta mike da sauri ta fizge wayar tace "Ina ake dagawa?" Ammi dai ta kasa cewa komai, a fusace Mama Ladi tace "Don Allah ki daga min kar ya katse" Ammi tayi picking call din, Mama Ladi tace "Salama alekum, yaya ina wuni" Daga daya bangaren Hajja tace "Ina Ammin?" Mama Ladi tace "Sallah take shine na daga, ya aka yi ne?" Hajja tace "Ban sani ba, halan wajenki Badiyyan taje da zaki ci mata mutunci Ladi?" Mama Ladi tace "Wacece kuma Badiyyah? Ayyo wai Badiyyah jikar ki? Wato don ba a bar ki kin kwana cikin barayi ba shine har bakinki zai kara furta sunan Badiyyah gatsal Hajja?" A fusace Hajja tace "Kar ki gaya min maganar banza Ladi, ke wace irin munafukar mace ce me hada fitina ne? Ki ba Ammi wayar ba dake zan yi magana ba" Mama Ladi tace "Wallahi bazan bata ba, in