← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 283 OF 313

Sashe 283

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammi na komawa bangarenta ta nufi Bedroom dinta direct tare da Mayraah ta kulle dakin ta zaunar da ita gefen gado ita ma ta zauna tana kallonta a sanyaye, Mayraah ta sauke idonta hawaye masu zafi na zubo mata, Ammi ta share mata idon muryarta na rawa tace "Bana son kina kukan nan daughter, this is our destiny altogether, don ba jarabawanki bace ke kadai, har mu, kuma dole mu amshesa hannu bibbiyu" Mayraah ta dake tace "Kawai kukan farin ciki nake Ammi, na kuma amshi kaddarata hannu biyu don being a muslim is one of the greatest thing that have ever happen to me in my life regardless of ta yanda aka sameni, ni nasan bazan taɓa iya canza kaddarar yanda Allah yayi zan zo duniya ba, who am i ti change that? it's already written, kuma ina farin cikin da Allah ya kaddara min rayuwa tare da ku har na zama cikakkiyar musulma, ina alfaharin kasantuwar ku iyayena da bazan taɓa replacing ba no matter what, Alhamdulillah ala kulli haal.... Alhamdulillah ala ni'imatil Islam.... Don da ace na tashi tare da warce ta haifeni duk da ance tana musulunci probability dina na zama musulma will be very low don yayarta zata iya fin karfinta a kai na, ko wannan kadai na tuna zan ci gaba da godiya ga Allah, and now i will have rest of mind nasan wacece ni...." Rungumeta Ammi tayi tana kuka tace "That is just it daughter, Allah Ubangiji ya maki albarka, and i am proud of ur faith, In sha Allahu daga yau kin daina kuka" murmushi Mayraah tayi tana rungume jikin Ammi. Bayan azahar Mayraah na zaune kan darduma a dakinta Usman ya shigo da sallama, ta daga kai tana kallonsa bayan ta amsa, kasa kallonta yayi ya karaso cikin dakin ya zauna, ita dai kallonsa kawai take, bayan few seconds ya sauko kusa da ita ya zauna saman carpet din a hankali ya kamo hannunta murya can kasa yace "You know what Mimi?" Tace "Sai ka fada yaya" Ɗan murmushi yayi jin reply dinta, a hankali yace "I want you to know that no matter the situation, no matter the circumstances you still remain our little Mimi, we still sees you as our blood" murmushi kawai take tana kallonsa, Bude kofar dakin aka yi duk suka juya, Maheer ne ya shigo dakin da sallama, yana ganinsu ya wara ido yace "Really?? What are my siblings up to?" Yana fadin haka ya karaso kusa da su shi ma ya zauna ya tankwashe kafa yana kallonsu both yace "Me ake yi babu ni?" Usman na kallonsa yace "I am just reminding her that we still sees her as our little cute sis, we still sees her as our blood... And all in all, we still love her as our lovely intelligent Mimi" Maheer ya daura hannunsa kan nasu yana murmushi yace "Ayi reminder din da ni" Er dariya Mayraah tayi cikin sanyin murya tace "And i see u both as my shield! today, tomorrow, next tomorrow, and forever.... I am proud to have u both and Ya Umar as my big brothers, ina alfahari da ku yayyina a ko da yaushe" Duk murmushi suke suna kallonta, ita ma tayi murmushin tayi pecking din hannunsu gaba daya. Sosai Ammi tayi mamakin yanda Mayraah ke ta harkan gabanta throughout ranan a gidan kamar babu abinda ya faru, hakan ya sa hankalin Ammi ya kwanta, sai dai fa can kasan zuciyar Mayraah tana jin tausayin mahaifiyarta amma ba wai don tana son kasancewa tare da ita ba. A ranan da daddare MD ya tura ma Maheer Flight ticket na Business class da Ceo ta sa yayi har kujeru takwas na tafiyar da za su yi washegari, flight din kuma na karfe taran safe ne, Mayraah na tare da Maheer da Usman a dakinsa tana basa labarin yanda ta ji a sanda ta ci poison, Usman dai danna wayarsa kawai yake yana sauraronta, Maheer dake kallonta attentively ya dau wayarsa jin shigowar message, ganin wanda ya turo masa message din ya shiga WhatsApp dinsa, Mayraah ta hade rai tace "Yaya kai ma danna wayar zaka yi baza ka saurareni ba" Dariya ta ba Maheer bayan yaga ticket MD ya turo masa ya mayar da wayar ya ajiye gefe yanw murmushi, Usman ya daga kai yana kallonta yace "Wa yace maki bana jin abinda kike cewa" Ta turo baki tace "Toh gaya min me na fada last in ji" Yace "Oho" Abba ya gama shan shayin cup din hannunsa ya kalli Ammi, sai kuma ya ɗan yi murmushi yana girgiza kai yace "Sai kuma nace maki zan je in gaya ma Hajiya Amina wannan magana" A takaice Ammi tace "I don't know, and I don't even care to know, kawai ni dai nace maka in ma kana da niyya kayi hakuri kar ka fara, don wannan babban sirrin daughter na ne da ma mu kan mu gaba daya, bana kuma son zancen nan yaje ko ina, ina son ya kasance mun binnesa ne a inda muka ji sa har a tashi duniya babu wanda zai kara tada sa after tomorrow, duk da nasan halin yarana maza hakan bai sa na fasa jaddada masu ba" Abba yace "To kafin ki jaddada masu ni na fara jaddada masu, kuma na fi ki sanin muhimmancin binne maganar a inda muka ji sa, fadan ta ma a wani waje bashi da amfani ba kuma shi da fa'ida" Ammi tayi murmushi tace "Toh Allah ya sa mu dace" Washegari da safe wajen karfe bakwai da rabi Ammi ta shigo dakin da Aunty Mariya da Mama Ladi suke, Ammi ta zauna ta gaida Mama Ladi, sannan suka gaisa da Aunty Mariya, Mama Ladi na kallon Ammi tace "Kin ji fa yau Mariya zata koma, nace mata ina lefin ta ɗan kara kwanaki kafin nan Mera ta ji kwarin jikinta, naga dai ko kwana biyu ba ayi da sallamanta a asibitin ba, ke ba miji ba yana can Legas sai sanda Allah ya kado sa" Aunty Mariya tace "Mama yau satina fa biyu a Abuja, banda muna asibiti ni na so ma mu koma tare da Hajja a sanda ta tafi, Mayraah kuma ai jiki sai dai mu ce Alhamdulillah" Mama Ladi ta kyabe baki ta gyara kwanciyarta, Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Nima yanzu shigowa nayi in ce maku za mu kaduna amma in sha Allahu yau za mu dawo, kin ga gidan ba kowa Mariya kiyi hakuri ki bari in mun dawo sai ki tafi" Mama Ladi ta mike zaune tace "Me za ku je yi a kaduna kuma?" Ammi tace "Alhaji ne yace za mu je kaduna, ina jin ziyara za mu" Mama Ladi ta gyara zama tace "To wa gareku a Kadunan? shi Mamuda ba mu kadai ne danginsa ba a halin yanzu? waye bai san bai da kowa ba, kullum mu ne dai ke fadi tashi akan matsala idan ta ɓullo a gidansa" Ammi ta mike tace "Bari in je in shirya Mama, jirgin namu na karfe tara ne" Mama Ladi tace "Toh Allah dai ya tsare, kilan wani sirrin za ku je kuyi a can bakin ku alekum, Allah de ya kyauta, dazu ma naga ai kun fita, dama fatanmu Mera ta samu sauki kuma ta samu, nan da kwana biyu in sha Allahu nima sai in san inda dare yayi min, na lura yanzu Mamuda kora da hali yake mana, banda haka ni dai wllhi nasan bashi da kowa a Kaduna" Ammi tace "To ziyara za mu je gidan abokinsa sun samu karuwa, yanzu dai hankalin ki ya kwanta dai ko" Mama Ladi tace "To Allah ya tsare" Ammi tace "Ameen" Kofa ta nufa Mama Ladi tace "Kin dai ji Badiyyah na can ranga ranga asibiti rai a hannun Allah wai ta zame wajen shiga bandakin Yahanasu, kinsan bandakin gidan Yahanasu ko na kasuwa albarka, ga uban gansa kuka, har wani yauki yauki bandakin yake wllh, abun dai ba arziki ko dake duk kun sani ai, ita fa Yahanasu tun muna yan mata take kazanta gashi ya bi ta har tsufa, ko ruwa baka iya sha in ka shiga gidanta sai in kai ma kazamin ne" Ammi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yaushe hakan ya faru?" Aunty Mariya ta numfasa tace "Da asuba aka kirani, ashe tun jiya da daddare abun ya faru" Ammi tace "Amma jikin da sauki dai ko?" Mama Ladi tace "Wuyarta ace mana tayi ɓari, kilan ma da gangan ta zame, ko da yake cikin shege ai kowa yasan naci ne da shi, ba wani zancen barewa" Ammi na kallon Aunty Mariya tace "Wa ke tare da ita a asibiti?" Aunty Mariya tace "Wai babbar jikar Yahanasu, sun kira Hajja tace masu ai ita bata garin ma, Yahanasun ma taki bin su asibitin, dole haka ni nayi masu transfer dazun nan wai za a kara mata jini, sannan she is unconscious, wannan ne ma yasa nake son in koma kadunan yau" Ammi tayi shiru ta ma rasa me zata ce, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Shikenan, in sha Allahu zan karasa asibitin in mun je kadunan" Aunty Mariya tace "Toh Allah Ubangiji ya kai ku lafiya, wai har su Maheer?" Ammi tace "Eh har su" daga haka ta fita daga dakin. Ammi na kallon Abba bayan ya gama shiryawa, cikin sanyin murya tace "Yallabai ga wani suggestion da ya zo raina yanzun nan" Abba ya juya yana kallonta yace "Na me fa?" A hankali tace "Ni a nawa tunanin Yallabai why not mu bar Mayraah kawai ba sai mun je da ita kadunan nan ba, wallahi bana son abinda zai sake daga mata hankali duk da dai naga tun jiya bata saka damuwa a ranta ba, yau ma naga da walwalarta ta tashi ba wani damuwa, to kar mu je kadunan nan kuma ta samu heartbreak din da ya fi na jiya, i don't want my daughter to be hurt" Abba ya ɗan yi shiru yana kallonta, bayan wasu dakikai yace "Kar ki damu, in sha Allah abinda kike tsoro bazai faru ba, tun da kin ji me asibitin tace mutumin na ta bibiyanta a kasar waje yana tambayarta ita uwar Mayraah din, so wannan ne nima ya bani karfin gwiwan
Chapter 283 · 0% Book details