Sashe 153
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
bin ward din da kallo, it's so big and clean, daga gani kasan ba karamin asibiti bane ko daga gadon da take kwance zaka gane hakan, Receptionist din tace "Bari in masu magana ince kin tashi...." Daga haka ta fita daga babban ward din, Mayraah ta bi ta da kallo, sai kuma ta kalli Cctv camera dake ward din, maida dubanta tayi kan drip da aka makala mata a hannu, dai dai nan aka bude kofar ward din ta daga kai da sauri, wani mutumi ne ya shigo tare da wani dake biye da shi a baya with white lab coat da stethoscope a wuyansa, ita dai duk kallonsu take har suka iso bakin gadon da take, mutumin da ya fara shigowa dakin ya ɗan duka ya dafa gadon yana kallonta yace "Baiwar Allah ya jikin?" Mayraah tace "Alhamdulillah naji sauki" Likitan ya karaso ya kara gudun drip din kafin shi ma ya kalleta yace "Hope you are feeling much better now?" Tace "Sure" Yace "To Maa sha Allah" Receptionist din tace "Manager yace ta kira yan uwanta sai ni in koma bakin aikina" Sosai gaban Mayraah ya fadi, likitan yace "Eh gaskiya ne, ai kun ma yi kokari for such hospitality" Sai kuma ya kalli Mayraah yace "Ki kira yan gidanku yanzu ki sanar masu kina asibiti" Da sauri tace "Ai wayar na dakin hotel din" Mutumin da ya kawota hospital ya ciro wayarsa ya mika mata yace "Za ki iya amfani da nawa" Sosai gabanta ya fadi, ta amshi wayar tana tunanin yanda zata yi, nan da nan dubara ya fado mata tayi dialing din layinta dake kashe ta sa handsfree, duk suka dinga kallonta jin switch off, a hankali tace "Number Abbanmu ne, bari in kira yayana" Daga haka ta sake dialing other line dinta nan ma aka ce switch off, Mayraah ta kalli receptionist din tace "Za ki iya tafiya, Nagode sosai, nasan zuwa anjima zan samesu a waya" Receptionist din tace "Toh Allah ya kara lafiya, ga Atm card dinki" Mayraah har ta mance da Atm card din, ta amsa tana juyawa tace "Nagode" Receptionist din tayi mata Allah ya kara lafiya, zata fita mutumin da ya kawo su yace "Ko za ki jira mu koma tare in 30mins time" Tace "Ayya, kar ka damu zan samu Cab idan na fita, kaga instruction din manager dinmu kenan, yace tana farkawa in dawo bakin aiki" Yace "To ba laifi" Daga haka ta fita daga ward din. Mayraah na gyara Hijab din jikinta a hankali tace "Naji sauki fa, kawai za a iya sallamata in biya bill din" Dr Khalil ya kalli abokinsa Ahmad kamar yanda Ahmad din ma ya kallesa, can Dr Khalil yace "Ae ba a gama baki proper medications ba, kuma kinga ko rabi drip din hannunki bai kusa ba" Mayraah tace "Ni fa i am okay, kawai jinina ne yayi kasa, but i am better now" Ahmad yace "Ohk then, ka sallameta Dr, sae kawai a rubuta mata drugs" Dr Khalil yayi kasa da murya yace "To ae kasan ka'idar hospital din nan...." Ahmad yace "To tace zata canza hospital, It's not ur fault" Dr Khalil yace "Ohk then"