← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 246 OF 313

Sashe 246

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

infact baya ma da lafiya tun da ku ka dawo har drip sai da na sa mashi, but he is around today, ko zuwa karfe daya ne sai driver ya kawo ki, nasan duka duka baza ki wuce minti talatin ba a asibitin, kin ga driver din ma zai iya jiranki" Mayraah da gaba daya mood dinta ya canza don bata son fitan, a hankali tace "Ohk" Bayan ta katse wayar ta mike ta je ta samu Ammi a parlorn ta, bayan ta sanar mata abinda Dr Khalil ya kirata ya gaya mata, a hankali Ammi tace "Mimi, ina ga fa hakura za kiyi da aikin nan" Mayraah ta daga kai tana kallon Ammi babu ko kiftawa, Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Wallahi hankalina yaki kwanciya har yanzu, i am so disturb this past days na rasa dalili, ina ji a jikina kamar akwai abinda zai faru" Mayraah da jikinta yayi sanyi tayi shiru tana kallon Ammi, can ta sunkuyar da kai, Ammi ta mike ta koma kusa da ita ta jawota jikinta, nan da nan hawaye ya kawo idonta amma bata bari Mayraah taga hakan ba ta goge idon da sauri tace "I don't know why i am afraid Daughter, duk kwanan nan wasu irin mafarkai nake da ban gane kansu ba" Mayraah tayi karfin halin cewa "In sha Allah Ammi na bar aikin since you are not comfortable with it" Ammi dai tayi shiru tana rungume da ita wasu hawayen na taruwa idonta. Bayan azahar Mayraah na kwance dakinta taji wayarta na vibrate, mikewa zaune tayi sanin bazai wuce Dr Khalil ba, to me ma zata ce masa, kai tsaye dai bazata ce masa Ammi tace ta bar aikin ba, a hankali ta jawo wayar bayan ta gama tunanin abinda zata ce masa, amma sai taga wani layi with special digits ne ke kiranta, ta dinga kallon screen din babu ko kiftawa, babu wanda ya fado mata sai Musharraf, lkci daya taji jikinta yayi sanyi and she just believe shine ke kiran nata tunda babu wanda ke da layin bayan yan gidan da Dr Khalil, picking call din tayi kafin ya katse ta sa hands free gabanta na faduwa tana jiran jin muryarsa, "Didn't Khalil pass my message to you?" Mayraah tayi shiru, ko kadan bata yi wani mamakin inda ya samu numberta ba bayan da ta ji muryarsa, after some seconds ta langwabar da kai tace "A gidanmu ance sai gobe zan je tunda kowa yasan yau ai bana zuwa aiki" Jin yayi shiru tace "Hello" Yace "No bari nayi ki gama rashin kunyan" Ta dan tabe baki tace "Abinda aka ce a gidanmu fa nake gaya maka ai ba rashin kunya bane" Yace "Za ki sani" Daga haka ta ji ya katse wayar, ta ajiye a hankali ta koma ta kwanta maganganun Ammi na dawowa kanta, lkci daya hawaye ya cika idonta. Bayan la'asar Mayraah ta je kai bowl din da tayi ma Ammi fruit salad a ciki taga Maheer zaune parlor yana kallo, throughout yau bata gansa ba, bayan ta gaishesa ta tafi kitchen da bowl din ya bi ta da kallo, ba a dau lokaci ba ta fito ta xauna kujeran dake facing dinsa tace "In maka girki yaya?" Ya dan buda ido yace "In baxan takura Mimi ba" Murmushi tayi ta mike ta wuce kitchen.... Kafin karfe shidda Mayraah ta gama girka masa favorite dinsa, bayan magrib ganin bai shigo gidan ba ta dau wayarta tayi dialing numbersa yana fara ring ya daga a hankali yace "Mimi" Tace "Yaya na gama kuma naga baka shigo ba" Yace "I am having headache Mimi ki kawo min nan" Da damuwa tace "To bari in kawo maka yaya, Allah ya sauwake" Daga haka ta katse wayar ta dau hijab din da tayi sallah ta mayar jikinta sannan ta fita, downstairs ta sauka zuwa kitchen bayan ta dau abincin iya wanda zai iya ci ta fita ta kai masa chalet, dukawa gabansa tayi ta ajiye masa abincin tace "Idan ka ci sai ka sha magani" Yace "Yes dear" Mikewa tayi ta fita daga parlon, Haseenah da ta shigo kitchen take tsaye tun farkon da Mayraah ta kirasa yace mata ta kawo abincin, tana jin alamar Mayraah ta fita ta kwala wani kara me karfi, Maheer dake kwance ya mike zaune yana kallon kitchen din, banda zuciyar musulunci babu abinda zai kai sa kusa da kitchen din nan, but because of the kind of heart he have haka nan ya tashi ya tafi kitchen din, ƙasa ya ganta a kitchen din tana sauke numfashi, ya karasa yana kallonta ta dinga nuna masa kirjinta, tun dawowarsu gidan sai ranan yayi mata magana yace "Me ya faru" Da kyar tace "It's paining me" Nan da nan hawaye ya fara sauka idonta tana girgiza kai, sai da ya kai zuciyarsa nesa ya daga ta yana jin wani mugun tsanar ta har cikin zuciyarsa, suka fito daga kitchen din da kyar tana numfarfashi taki zama parlor tace "Daki zan je" Haka nan suka tafi dakin nata, hawaye na sauka idonta ta dinga juye juye tace "Wallahi mutuwa zan yi ciwo yake min sosai" Shi dai yana tsaye yana kallonta as if trying to diagnose what she said is wrong with her, muryarta na rawa tace "Kilan Ulcer ne ranan na bar maganin a kitchen din Ammi da ya tasar min" After few minutes ya juya ya fita daga dakin tana jin ya bude kofar parlor sannan ya rufe ta taso da gudu ta leka parlon ganin ya fita ta koma dakinta da sauri ta jawo karamin ledan dake karkashin gadonta ta fito parlor a guje ta nufi inda Mayraah ta ajiye masa abinci hannunta na rawa ta bude warmer din miyan ta juye abinda ke cikin kwalban gaba daya a miyan, ko ina na jikinta rawa yake, da yatsanta ta jujjuya miyan sannan ta kulle da gudu ta koma daki ta tura ledan da kwalban karkashin gado ta shiga bandaki ta wanke hannunta da handwash ta fito ta kulle kofar bayan ta goggoge hannunta ta koma inda ya bar ta ta kwanta ta kulle ido, bayan few seconds ta ji ya bude kofar parlon ta dinga sauke numfashi a wahale idonta a kulle har ya shigo dakin.....
Chapter 246 · 0% Book details