← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 291 OF 313

Sashe 291

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

Mami ta ɗan buda ido tana kallonsa at the same time speechless don Jiddahn nan er yayarta ce uwa daya uba daya, kuma wajen yayar nan tata MD ya tashi tun daga yaye ta rikesa har zuwa yanzu don ya ma fi sabawa da ita akan Mamin nasa, shi yasa ma ba wani shakuwa tsakaninsa da Musharraf, Mami ta sauke idonta a hankali tace "Sai dai in ma yaya bayani, idan ya so in ma janyewan ne sai ayi kawai a bar zancen Jiddar, don farin cikin Musharraf shi ne nawa, nasan ba shi da wani option ne dama shi yasa ya amince da auren Jiddah, duk da Jiddah lacks nothing too" MD na gyada kai yace "Sai miskilanci" Mami ta hararesa, sai kuma ta kalli Musharraf tace "Ka kwantar da hankalinka zan kira Umman ko zuwa anjima" Mikewa zaune Musharraf dake ta sauraronsu yayi calmly yana kallon Mamin tasa yace "You know what Mami?" Mami dai kallonsa kawai take kamar yanda MD ma ke kallonsa, Musharraf ya ɗan yi murmushi yace "Baza su bani Mayraah ba" A hankali Mami tace "Me yasa kace haka?" Musharraf ya sauke idonsa yace "Za su canza mata ra'ayi, shi yasa Amminta tayi saurin supporting cewar she needs time to think, baza su bani ita ba" MD dai kallonsa kawai yake, Mami da jikinta yayi sanyi ta kasa cewa komai don sarai ita ma ta gano hakan bata dai son ta daga masa hamkali ne, amma daga furucin Ceo da Ammi ta sha jinin jikinta, A hankali Musharraf yace "Don haka ni na cire rai da Mayraah, i know everything happens for a reason in life...." Yana fadin haka ya koma ya kwanta facing the other direction, Mami tayi tagumi duk jikinta yayi sanyi, MD ya ajiye cup din shayin hannunsa ya mike ya fita daga dakin bai taɓa jin tausayin kanin nasa irin yau ba, Mami ta koma daya side din tana kallon Musharraf seeing tears in his eyes immediately broke her down too. MD na barin dakin ya tafi har zuwa daya part din with different thought in mind, Mayraah ya hango rike da tray din drinks da ruwa tana tahowa, tun da ta hangosa ta rage tafiyarta, hakan yasa ya nufeta ta sha kunu ta tsaya seeing he is coming directly toward her, da ido ya bi wajen da kallo bayan ya isa har gabanta sannan ya amshe tray din hannunta ya ajiye a nan wajen, a takaice yace "I want to speak with you" Ta ɗan buda ido kafin tace komai ya fixgo hannunta, buda baki tayi tana kallon sa da mamaki tana biye da shi lkci daya ta hau waige waige a wajen taga babu kowa, bude kofar wani part yayi ya shiga ciki da ita sannan ya kulle kofar, ita dai kallonsa kawai take fuska daure, Ya zagayo gabanta yana kallonta yace "Did you know what heartbreak means?" Mayraah ta gyara tsayuwa tana kallonsa at the same time looking so confuse, as if counting his words MD yace "Do not break my brothers heart! shi ne first love din ki, idan kika ƙi aurensa kin ci amanarsa after all what he went through, duk abubuwan da suka faru lokacin da aka fara saka bikin ku bai guje ki ba, bai ƙi ki ba, bai canza maki ba, he was there for you all through, idan kika ki sa yanzu kin ci amanar sa, kin ci amanar kauna" Mayraah dake ta kallonsa nan da nan hawaye ya cika idonta, cikin sanyin murya tace "Kaga alamar ni zan ce bana son sa ne? I will never do that, i still love him just like he loves me, and he is still my first love nothing can change that" MD dake ta kallonta yace "Better!!" Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, a hankali ta zauna saman kujeran Parlon tana goge hawayen dake zuba idonta. Karfe biyu da rabi Abba ya ce ma Alhaji Saminu za su koma kano bayan sun dade suna hira da shi a parlon sa, Alhaji Saminu yace "Amma dai zaka bar iyalinka da er ku zuwa ko gobe ne a yankar masu ticket" Abba yace "Eh to, dama mai dakin nawa tace min zata je wani ziyara nasan za su kai har gobe a garin nan" Alhaji Saminu yace "To madallah, sai kuma magana ta biyu ina ga kai yafi dacewa ka tambayi yayar Maryam kwana nawa za su diba na tarewar kanwarta, in kadunan ne ko Abuja or even kano nasan it will be okay for Abdallah don duk yana harkokinsa a garurrukan nan" Abba yace "Toh zan sameta yanzu mu yi magana in sha Allah" Ceo na zaune a parlon dake downstairs da Abba da ya sa aka kira masa ita, bayan Abba ya sanar mata dalilin kiran nata Ceo ta dan yi murmushi tace "Wannan sai mun koma Abuja za mu yi deciding da ita Alhaji ai ba abun gaggawa bane, bayan nan i am sorry to say akwai tests da ya kamata duk su biyun za su yi a asibitina na Abuja" Abba yace "Eh hakan abu ne me kyau gaskiya, amma kinsan me nake so da ke?" Ceo ta daga kai tana kallonsa tace "Aa" Yace "Alfarma nake nema don Allah, kiyi hakuri duk ma abinda za ayi kar ya wuce sati biyu" Shiru Ceo tayi, bayan few seconds a hankali tace "To shikenan Alhaji" Abba yace "Nagode kwarai, ni yanzu zan koma Abuja da su Maheer don har sun samar mana ticket din jirgin kasa that is heading to Abuja" Ceo tace "Fine, if it's still available zan sa Aliyu yayi purchasing mana ni da Aaria, nasan shi kilan ba yau zai koma ba, to amma Madam dinka da daughter dinku fa?" Abba yace "Akwai ziyaran da za su yi ne cikin gari, sai gobe za su koma Abujan in sha Allah" Ceo tace "To Allah ya kai mu" Karfe uku da rabi Ceo da kanwarta da Abba da su Maheer suka fita compound drivers din Alhaji Saminu za su kai su Train station dake Hayin rigasa don hawa jirgin kasa da zai je Abuja, duk da yanda Abdallah ya so ko sallama ne su yi da Aaria amma Ceo taki bada wannan space din ta saka kanwarta a mota ita ma ta shiga, Mayraah dai na tsaye kusa da Amminta tana daga ma su Ceo hannu duk da su ma ga nasu drivern da zai kai su Asibitin da Badiyyah take, Mayraah ta kalli motar da su Abba da Maheer suka shiga su ma ta daga masu hannu tana murmushi, babu wanda bai fito daga gidan yi masu sallama ba har Alhaji Saminu sai da ya daure ya fito, Aaria dai sai kallon Mayraah dake makale da Ammi take, Bayan fitar motocin su Abba da Ceo, Hajiya Halima ta bude ma su Ammi motar da za su shiga tace "Amma dai nan za ku dawo ku kwana ko Hajiya?" Ammi tayi murmushi tace "Gidan kanwata zan je daga asibitin, amma in sha Allah da safe za mu dawo mu yi sallama" Hajiya Halima tace "To shikenan, don Allah a gaida mana su, kuma ayi ma me jiki sannu" Ammi tace "In sha Allah" Hajiya Ramatu ta kalli Mayraah tace "Baki dauko maku takeaway din ba Mayraah" Ammi tace "Dama nace sai ta manta sa in dai Mayraah ce" Murmushi Mayraah tayi ta juya ta tafi taje ta dauko, Musharraf na zaune balcony don motar su Abba na barin gidan bayan an yi sallama can ya koma ya zauna, tun bata karasa balcony din ba ta gansa zaune, shi kam bai ganta ba sai da ta zo dab da wajen, suna hada ido taga ya mike ya juya ya shiga cikin parlor, bin bayansa tayi walking a little faster amma tana shiga parlon taga babu shi, waige waige ta dinga yi ko zata hangosa a babban parlon amma bata san direction din da ya bi ba cause the house is so big, lokaci daya jikinta yayi mugun sanyi, tana tafiya a hankali ta haura sama ta tafi ta dauko takeaway din da Hajiya Ramatu tayi masu sannan ta dawo kasa tana kalle kallen ko zata ga Musharraf amma still bata gansa ba, bata san dalilin da yasa hawaye ya kawo idonta ba amma tayi saurin gogewa ta nufi kofa ta fita, a haka ta koma parking space tana tafiya a hankali, ita da Ammi suka shiga motar da zai fita da su suka bar gidan ana daga masu hannu, sai da suka yi nisa Ammi ta kalli Mayraah da tayi shiru, ta jawota kusa da ita tace "Lafiya daughter? Why are u quiet?" Mayraah ta kirkiri murmushin yake tace "Kawai na gaji ne Ammi" Ammi tace "Yanzu gidan Hajiya Murya za mu tafi don sai zuwa karfe shidda za mu je asibitin, Mariya ta kirani dazu wai sunyi waya da Hajja ita da Baaba Yahanasu suna can, to kin ga kar mu je mu cika dakin asibitin, ta so mu sauka gidanta amma nace gwara dai mu je gidan Hajiya Murja" Hajiya Murja cousin sis din su Ammi ce. Kamar yanda Ammi ta fada sai wajen karfe shidda suka fita daga gidan Hajiya Murja zuwa asibitin da Badiyyah take, sai dai ko da suka je still din dai Hajja da Baaba Yahansu suna asibitin, Hajja na kallon Mayraah bayan ta amsa gaisuwar Ammi, a hankali tace "Ya jikin Mayraah?" Mayraah na murmushi tace "Na ji sauki Hajja, ya jikin Sis Badiyyah" Hajja ta sauke kanta tace "Toh da sauki Alhamdulillah" Kana ganin yanayin Hajja za ka ga kamar dai kunyan Mayraah take duk taki sakin jiki, Ammi dai na tsaye bakin gadon da Badiyyah take tana mata sannu, can ta kalli Baaba Yahanasu tace "Yanzu ya ake ciki Baaba?" A takaice Baaba Yahanasu tace "Ɗa fa ya mutu a ciki tun jiya, yanzu dai likitocin sun ce mu jira zuwa nan da sati biyu zata fara nakuda da kanta, in kuma baza mu iya jira ba to za su tattago mata nakudan a irin dubarunsu na asibiti, ni dai nace za mu jira sati biyun in muna da rai da lafiya, sun ma ce ba lallai ya kai sati biyun ba" Ammi dai ta kasa cewa komai amma a ranta hamdala tayi da ɓarin cikin nan, Baaba Yahanasu tace "Toh kin dai ji abinda ake ciki, ciki dai kam ya lalace, kar fa kice wani zamewan kirki tayi don bana ma tunanin ta kai kasan bandakin tunda ina zaune tsakar gida a lkcn, ikon Allah kawai, ciki dama ba daga sati daya zuwa sati takwas ake ɓarin sa ba in ma barin ne? Na taɓa jin inda aka yi barin cikin da ya riƙa, to astagfirullah ban dai sani ba tunda ni ba likita bace, cikin dai Badiyyah kam bai da rai maganar da nake maki yanzu" Ammi ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Allah Ubangiji ya bata lafiya, Allah kuma yasa hakan shine mafi Alkhairi gareta da ma mu baki daya" Baaba Yahanasu tace "Ameen, ai kam shine ma alkhairin, ba mu da rabon wahala kawai" Mayraah tayi farin cikin wannan batu na lalacewar cikin Badiyyah sosai kuwa, ta karasa bakin gadon tana kallonta tace "Sannu sis Badiyyah" Kai kawai Badiyyah ta gyada mata, Baaba Yahanasu tace "Yanxu komawa za mu yi can gidan nawa sai Hajja ta zauna da ita kawai...." Ammi tace "Ai yanzu ma daga gidan Hajiya Murja muke Baaba" Baaba Yahanasu ta rike haɓa tace "Kika sauka gidanta? Matar da har yau ko ci kanku bata ce mana a asibiti ba, ku dai wallahi ba ku da zuciya kare ya lashe, babu yanda ban yi da Mariya kan ta fita sabgar murjan nan a garin nan ba amma taki, ke kuma don neman suna ga gidana kika tafi gidan wata Murja tunda ita tana da babban tsakar gida kuma da gas take girki" Ammi ta kwantar da murya tace "Wallahi ba haka bane Baaba naga kuna asibiti ne, mu kuma gobe da safe za mu koma Abuja, Hajiya Murja kuma tana can tana fama da yarinyar nan nata Sickler wallahi bata da lafiya sosai yarinyar shi yasa ba ku ganta a asibitin ba har yanzu" Baaba Yahanasu dai ta kyabe baki ta ki cewa komai, sai kusan karfe tara su Ammi suka bar asibitin da Mayraah. Washegari da safe kamar yanda Ammi ta fada sai da suka koma gidan Alhaji Saminu yi masu sallama, su din ma dai train ticket aka siya masu don babu jirgi, Ammi kuma tace baza su kai har yamma ba, Mayraah dai sai kalle kallen inda zata ga Musharraf a gidan take amma bata gansa ba sai MD, Ko Mami bata gani ba a gidan, a haka dai MD da Babanta suka kai su train station bayan Hajiya Ramatu tayi masu sha tara ta arziki bayan ta jaddada masu next week duk za su shigo Abujan, Alhaji Saminu ma 200k ya ba Ammi, suna isa station din Ammi tayi sallama da MD da Abdallah, ita dai Mayraah mance waye Abdallah take a gareta don ko dazu sai da Ammi tace mata bata gaidasa ba sannan tayi saurin gaida shi, shi kam sai dai yayi ta bin ta da ido, Da ladabi Abdallah da ke kallon Ammi yace "In sha Allah sati me zuwa za mu shigo Abujan da su Abba" Ammi na murmushi tace "Allah Ubangiji ya kai ku mu" A haka suka rabu a tashar, suna isa Abuja Maheer na tasha yana jiransu, Mayraah was so happy to see him.
Chapter 291 · 0% Book details