← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 170 OF 313

Sashe 170

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.
Mayraah na zaune wani ward da babu kowa ciki ta daura kanta kan gadon idonta a lumshe, ga cup din Caffeine drink da bata shanye ba kan table dake kusa da ita, Dr Khalil ne ya shigo ward din tare da wani Dr Hamid, duk suka nufota Dr Hamid na kallonta yace "Why didn't u lie down?" Mayraah ta daga kai da sauri tana kallonsu don bata ji shigowarsu ba alamar bacci ya fara daukarta, Dr Khalil ya kalli cup din coffeen yaga rabi kawai ta sha yace "Me yasa baki shanye ba?" Ta girgiza masa kai a hankali tace "Ya isheni" Wata nurse ce ta shigo ward din rike da blood pressure gauge, Dr Hamid yace "Check the Bp again" Nurse din ta kama hannun Mayraah ta hau duba Blood pressure dinta, bayan ɗan lokaci da dago tana nuna masu tace "It's almost normal sir" Dr Khalil na kallon Mayraah yace "Ki kwanta ki yi relaxing zuwa anjima kadan" Mikewa tayi ta cire takalman kafanta a hankali sannan ta hau kan gadon ta kwanta, Dr Hamid ya juya suka fita tare da Dr Khalil, Dr Hamid na kallon Dr Khalil yace "When was she employed here? I have never noticed her, naga kuma babu vacancy, in ma akwai 'ya yan masu ƙasar suke ba ma ae" Dr Khalil ya ɗan shafa kai yace "Ai ina jin transfer aka mata..." Dr Hamid na gyada kai yace "But she is really good gaskiya, irin nurses da nake son aiki da kenan, tana da nutsuwa da composure wajen aiki she did all the sutures perfectly without waiting for directive, ba ko wace nurse ce zata iya ba, Intradermal suture fa, even Dr Balogun commended her" Dr Khalil na gyada kai yace "Nima na gani, i was also surprised, stress din aikin ne yayi weighing dinta down, dama kuma bata da lafiya tace min" Dr Hamid yace "She needs to work on her diet, and decrease her carbs intake, hypotension ai ba abu bane me kyau" Dr Khalil yace "Gaskiya kam" Mayraah na bacci wajen karfe shidda saura Dr Khalil ya shigo ward din da take, ya taɓa gadon da take kai ta bude ido a hankali, yace "How are you feeling now?" Ta mike zaune tace "I feel better" yace "Pls avoid eating lot of carb food Ilham, bai kamata jininki na kasa haka ba, more veggies to ur diet" Ita dai tayi shiru, yace "Yanxu yamma bai yi ba kice za ki koma Suleja? And I don't think it will be possible kullum kina komawa can kina zuwa nan, the distance..." Mayraah tayi saurin katse sa tace "Ai mun yi magana da Aunt dina da mijinta tun da kace zaka samar min aiki sai suka ce ko hostel na student ne sai in samu a nan Abuja in zauna saboda da nisa daga can garin ace in dinga zuwa nan kullum, duk sanda bana da aiki sai in je sulejan" Shiru tayi don ita kanta sai taji kamar maganar bai mata ba a kunnenta, shi dai Khalil kallonta kawai yake as if observing something, har ta tsargu ko ya gano karya take ne, gabanta dai sai faduwa yake ta sunkuyar da kanta, after few seconds of silence yace "Shikenan, amma at the first place da nace zan samar maki aiki ai kamata yayi ita aunt din ko Uncle dinki wani ya biyoki nan don tabbatar da hakan tunda yanzu kowa yasan yanda duniyar ta dawo, amma naga duk basu yi hakan ba" Nan gaban Mayraah ya tsananta bugawa cikin few seconds tayi cracking brain dinta ta samo abinda zata fada tana kallonsa tace "Ranan da muka zo da matar nan da yarinyarta ta rasu ai tare muke da aunt din nawa, ita komawa gida tayi ta bar mu, to nace mata nan asibitin ne...." Dr Khalil na kallonta yace "Even at that Ilham, amma ya ku ke da ita aunt din taki na Suleja? I mean dangantakar ku?" Mayraah taji hankalinta ya fara tashi, amma ta dake tana kallonsa tace "Kawai ta taɓa auren dad dina ne kafin ya rasu" Dr Khalil yace "Ur stepmom kenan?" Ta gyada masa kai tana kokarin sauka daga kan gadon alamar tambayoyin sun isheta, Dr Khalil yace "How about ur mum?" Ta wani kallesa a takaice tace "But i told u my parents are late" Ita kanta tasan she sounds pissed off, Dr Khalil yace "Dangin mamanki da babanki fa?" Tace "Dr... suna bauchi, admission din nan ya kawo ni Abuja ban san anyi cancelling dinsa ba, if not ni bani da kowa a Abuja ai sai stepmom dita a suleja" Dr Khalil na nodding kansa yace "Ohk i get, to bari zan kai ki inda zaki yi passing night din yau don yanzu yamma yayi kice zaki koma Suleja, amma ki fara kiran stepmom din taki ki sanar masu tukun, sai ku samu wani alternative din inda zaki zauna a Abuja" a hankali Mayraah tace "To" a ranta kuwa tunanin ina zai samar mata ta kwana take, kawai ita dai taji har ranta ta yarda da Dr Khalil don yawancin abubuwa idan yana yi ma kallon Maheer kawai take masa, kusan personality dinsu da halinsu daya, tun daga caring, tausayi, sannan he is also very free like Maheer, uwa uba kuma ta lura he is also observant just like Maheer, dole sai ta tsaya at alert incase ya mata tambaya ta jefa masa amsa babu bata lokaci yanda bazai sa zargin komai a ransa ba, Da sauri ta kallesa don har a sannan kallonta yake as if dai yana nazari, tace "To in kwana a asibitin kawai mana" Yace "Aa ai asibiti ba wajen kwana bane idan ba dole ba, kuma u need much rest, yanzu ki tashi ki dauko stuffs dinki, let me get my car key don i will still have to come back akwai surgery da za mu yi bayan magrib...." Mayraah tace "Toh" Sai da ya fita ward din sannan ta bi bayansa har a sannan kuma bata daina jin dizziness ba, awa biyu kawai tayi a theatre da wasu daga manyan likitocin asibitin har da wani ba indiye a cikinsu all trying to save the the lives of 4 people da suka yi mummunan hatsarin mota irin 'ya yan masu kudin nan, kawai daga taje mika wasu allurai da Matron ta bata ta kai wani likita ya tsayar da ita alamar bai ma san ranan ta fara aiki a asibitin ba, haka nan gabanta ya dinga faduwa duk da ko da suka yi clinical rotations dinsu back then in school she was one of the best student, but yanzu kam she is so nervous and afraid amma haka nan tayi composing kanta a wajen aka fara aiki da ita, Daga nan kuma bayan aikin awa biyu bata san sanda ta sulale kasa ba tsabar gajiya da dizziness shine likitocin dake wajen suka yo kanta da sauri. Mayraah na fitowa reception bayan Hafsat ta dauko mata jakarta da ledan uniform dinta tace "Allah ya sauwake Nurse Ilham, hope you are much better now?" Mayraah tace "Alhamdulillah naji sauki" Sauran nurses din dai sai kallonta suke kuma babu wanda dai yace mata sannu, Nurse Hafsat tace "Sae gobe kenan?" Mayraah tace "In sha Allah" Dai dai nan Dr Khalil ya sauko da makullin motarsa ya fita, Mayraah ta kara yi ma Hafsat sallama ta bi bayansa, nan ma duk aka bi ta da ido, suna barin hospital din bayan sun hau hanya Khalil yace "Amma a wani asibiti kika koyi aiki Ilham?" Sosai gabanta ya fadi tana kokarin tuna ko wani asibiti ta fada masa, ai ko nan ta kirkiro suna babu bata lokaci ta basa, yace "Wani gari kenan?" Ta ɗan kallesa tace "But i told u, a Bauchi nake" Yace "Yea na tuna, Shekara nawa kika yi kina koyan aikin?" Tace "Na ɗan dade fa" Yace "No wonder! but...." Mayraah taji gabanta ya fadi tana jiran jin but what, sai kuma ya karyar da kai ya fasa fadin abinda zai fada yace "Anyways it's fine.... u did a very good job dazu a theatre i was so impress kin ma fi wa enda suka yi karatun nurse din nutsuwa wajen aiki, you are so composed" Ta ɗan yi murmushi tace "Nagode sir" Yace "You are welcome" Bai sake ce mata komai ba har sai da suka yi tafiyar kusan minti ashirin ita dai sai bin cikin garin Abuja take da kallo, sai da suka shigo wani anguwa yayi horn bakin gate din wani gida aka bude gate din, ita dai har a sannan bata ji gabanta ya fadi ba ko kuma taji tsoro she don't even get the kind of trust she have for him daga haduwan sati daya da kwanaki, yana parking ya bude motar ya sauka ita ma ta sauka rike da ledan uniform dinta, wasu yara maza biyu yan shekara sha uku ne wanda da alama yan biyu ne ke ta ball a tsakar gidan suna ganinsa dayan ya dau ball din nasu ya rike a hannu a tare suka ce "yaya sannu da zuwa" Dr Khalil yace "Ba islamiyya?" A tare suka ce "Ai mun dawo" Gaida Mayraah suka yi ta amsa tana kallon kyawawan yaran, Dr Khalil ya kalleta yace "Mu je" Ba musu ta bi bayansa har suka shiga cikin parlon gidan, Wata elderly woman ce da bazata haura shekara 56 ba zaune parlon da mai aikin gidan suna hira, Khalil ya zauna kan kujera yana kallonta yace "Ummi ina wuni" Mayraah ta zauna kasa tana kallon matar da yace ma Ummi ita ma ta gaishta, Ummin tace "Aa tashi ki hau kujera mana" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Aa nan ya isa" Ummi ta kalli Khalil din tace "Ashe kuna hanya ma ka kirani kenan" Yace "Aa ko fitowa ban yi daga office ba, Ummi za mu shiga theatre after magrib zan koma" Ummi tace "To Allah ya bada nasara" Yace "Ameen" Ya kalli Mayraah yace "Ilham feel at home" Daga haka ya mike sai kuma yace "Ummi ya jikin Inna?" Ummi tace "Ai bacci ma take ina jin" Yace "Ohk, kilan sai gobe zan shigo" Daga haka ya fice daga parlon, Ummi na kallon Mayraah tace "Sannu da zuwa Ilham, ya aikin?" Mayraah na murmushi tace "Alhamdulillah" Ummi tace "Yace min suleja kike ko" Mayraah tace "Eh" Ummi tace "Suleja kam ai yayi nisa, sai dai ki nemi alternative, Karima ki kai ta daki ga magariba ma ya gabato" Mai aikin ta mike tace "To Hajiya" Wani daki da ba kowa Karime ta kai Mayraah, Mayraah ta shiga ta zauna gefen gadon dakin. Bayan isha Mayraah na dakin da aka sauketa, wata yarinya kyakkyawa da bazata wuce 11 years ba na cikin dakin ita ma sai labari yarinyar ke ba Mayraah da turanci, tun da yarinyar ta kyallara ido taga Mayraah shikenan bini bini zata shigo dakin, Mayraah na kallon yarinyar tace "Har yanzu ai baki gaya min sunanki ba" Yarinyar ta kyalkyale da dariya tace "My name is Fatima amma ana ce min Mimi" Mayraah ta gyada kai tace "Nice name..." Yarinyar ta dawo kusa da Mayraah tace "Aunty ke ya sunanki?" A hankali Mayraah tace "Ilham" Dai dai nan wayarta ya fara ring, Mimi ta mike da sauri ta dauko mata ta kawo tace "Aunty in kin gama wayar ki kirani" Mayraah tace "Toh zan kira ki" Daga haka yarinyar ta fita daga dakin, Mayraah tayi picking call din don Dr Khalil ne ke kiranta, bayan sun gaisa yace "Hope you are comfortable Ilham?" Mayraah ta gyada kai tace "Sure, Nagode sosai" Yace "That is my in-laws house" Mayraah ta buda ido tace "Ban gane ba" Yace "Gidansu matana mana, that's her mother" Mayraah was shocked ta ma rasa abinda zata ce masa.....
Chapter 170 · 0% Book details