← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 290 OF 313

Sashe 290

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Saminu ya juya ya kalli direction din Mayraah, Calmly yace "Mayraah" Mayraah ta dago kanta daga jikin Hajiya Ramatu ta kallesa, ya nuna mata gefensa calmly yace "Come over my dear" Mikewa tayi suka hada ido da MD dake kallonta ta sunkuyar da kai ta nufi kakan nata ta zauna inda ya nuna mata, duk kowa na parlon kallonta yake barin Babanta da ya kasa dauke idonsa a kanta, Alhaji Saminu na kallonta kafin yace komai Ceo ta dakatar da shi tace "I think tana bukatar a bata lokaci ta kara samun nutsuwar yin nazari kafin aji komai daga gareta Alhaji, beside she just recovered daga rashin lafiya" Ammi ta gyada kai da sauri tace "Wannan gaskiya ne, ba lafiya isasshe gareta ba, we were just discharged from the hospital not long ago" Tana magana ne amma har hawaye ya cika idonta, Alhaji Saminu yayi ma Mayraah side hug a hankali ya kwantar da murya yace "She should take her time, duk yanda ake ciki next week za mu shigo Abujan gaba daya" Shi dai Musharraf har sannan bai dago kansa ba, Mami dai sai kallon Ceo take haka ma MD.... Hajiya Ramatu ta mike ta tafi gun mai gidan nata ta dago Mayraah dake kusa da shi sannan ta juya tana kallon Ammi da su Ceo tace "Ku mu je can bangare na, ko ruwa baku sha ba...." Mami da Aunty Halima duk suka mike gaba daya suka bar parlon tare da Ammi, Ceo dake bayansu na rike da hannun kanwarta, duk da Hajiya Ramatu na rike da Mayraah amma gaba daya hankalinta na gun Amminta to be sure tana biye da su..... Kamar yanda Alhaji Saminu ya fada bayan barin su Ammi parlon ya maida auren Aaria da Mahaifin Mayraah akan Sadaki dubu dari biyu wanda shi ya bada, Abba kuma ya zama waliyin Maryam. Abinci iri iri aka yi serving din su Ammi a part din Hajiya Ramatu bayan ta kai su can, gidan Alhaji Saminu gida ne me girman gaske don Hajiya Ramatu ma parlor biyu gareta manya, Mayraah dai na gefen Ammi tana cin abincin gabanta, Aaria sai kallonta take babu ko kiftawa haka ma Hajiya Ramatu that couldn't take her eyes off her, Mayraah ko sanin suna yi ma bata yi ba, can ta daga kai ta kalli Ammi for the 4th time, tayi kasa da murya tace "Wai Ammi an kai ma su Yaya abinci?" Kamar an ce ta daga kai taga duk kallonta ake a parlon har Mamin Musharraf, rufe fuska tayi jikin Ammi da sauri tana murmushi kamar yanda Ammi ma ke murmushi, Hajiya Ramatu na girgiza kai tace "Sannu er Ammi, kin kira Ammi yayi sau goma yanzu a nan, kin ki barin ta ma ta ci abincin" Aaria ta sauke idonta a hankali tana juya abincin gabanta, Ceo dai Calmly take cin snacks din gabanta don ta ki cin abinci. Bude kofar wani Bedroom Mami tayi bayan ta fito daga ɓangaren Hajiya Ramatu, MD ta gani zaune yana juya coffee din hannunsa da tea spoon, kallo daya yayi mata ya ci gaba da abinda yake, ta karasa cikin dakin bayan ta kulle kofar tana kallonsa tace "Aliyu ina Musharraf?" MD yace "A masallaci na bar sa" Mami zata yi magana aka bude kofar dakin duk suka juya, Musharraf ne ya shigo Mami ta dinga kallonsa har ya karaso cikin dakin, tace "Ka ci abinci?" Kwanciya yayi saman gadon dakin a hankali yace "I am okay" Mami ta zauna gefen gadon tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Ya kake ga za ayi yanxu Musharraf?" MD ya kalleta yace "Na me fa?" Mami tayi kasa da murya tana kallon MD tace "Mamar ka ta Adamawa tace zata hadasa da Jiddah, ko baka da labari ne?" MD that was surprise yace "Jiddah? No bata gaya min ba, may be ta sha'afa ne but mun yi waya yau da safe ai" Mami tace "Na zata ta gaya maka shi sa ban maka maganar ba, har mun gama shirya komai da ita da Hajiya Safiyya, dama ina da niyyar zuwa nan kaduna in sanar ma Baffan ku sai ga rashin lafiya ta samesa, to dazu ma na fara masa maganar tunda jikin da sauki yace satin da za a shiga sai a kai kudi ko ba da shi ba, idan ya so sai a tsayar da sati daya bikin...." MD ya kalli Musharraf dake danna wayarsa, kallon Mami ya sake yi yace "But Mami tunda an dawo da zancen aurensa da ita Mayraan why not ki gaya ma Umman Adamawa abinda ake ciki yanzu, nasan idan taji abinda ke kasa zata janye batun Jiddah" Mami dai sai kallon MD take ta ma rasa me zata ce, MD yace "But in kuma yaga zai iya duk biyun sai ya aure su, it's not bad ai...."
Chapter 290 · 0% Book details