Sashe 233
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
sauri jin mutum a kusa da ita ta kusa cin karo da shi, not minding that ya daura mata jacket dinsa a shoulders dinta sannan ya koma inda yake tsaye, ta kasa dago kanta, after few seconds ta daga kai a hankali ta kallesa, wrapping din jacket din tayi jikinta ba tare da ta saka ba, bayan kusan minti biyar Ceo ta kirasa tace kawai ya taho da ita gidanta, he was so surprise, don banda shi a duk staffs dinta infact har colleagues dinta na nan UK babu wanda yasan gidanta sai shi kadai, sai da ya sake tambayarta to be sure of what she said, ta kuma maimaita masa abinda tace, a hankali yace "Ok Ma'am" Daga haka ya katse wayar ya samu Cab din da zai kai su gidan nata, it's almost 11pm na dare, Mayraah na ganin Cab din ta ja akwatinta duk da jacket din da ya sa mata bata daina jin sanyin ba don ya riga ya fara shigarta sanyin, ya dau akwatin ya sa a booth sannan ya bude back seat ya shiga, ita ma ta shiga, har suka isa gidan Ceo Mayraah was shivering a gefensa, wannan dalilin yasa shi daukan akwatinta daga booth din motar tana biye da shi, Ceo na bude kofar mansion dinta ta kallesa da mamaki tace "Why are you not on Jacket Aliyu?" Sai kuma taga Mayraah, bude kofar tayi da sauri tace "Come in my dear" Mayraah ta shiga parlon that was soo warm and smelling nice, shi ma ya shiga parlon with her box da hand luggage dinsa, Ganin yanda take rawan sanyi Ceo kawai ta wuce wani daki dake parlon da ita giving her a huge duvet to cover her self, sannan ta dawo parlor tana kallon MD tace "Go make ur self a cup of coffee Aliyu" Yace "Ma'am Idan naje gida zan sha...." Tace "Ohk then, akwatinta ne wannan?" Yace "Yes Ma'am nata ne" daukan akwatin tayi ta kai dakin da ta kai Mayraah, ya jira har ta fito sannan yayi mata sallama, tace "Let me get u my car key, gobe da safe sai ka dawo da shi" Ya sunkuyar da kansa yace "Ok Ma'am" Makullin motarta ta dauko masa hade da sabon jacket, ya amsa jacket din da makullin sannan ya saka jacket din yayi mata godiya ya bar gidan ya nufi garage dinta, kitchen ta tafi zata hado ma Mayraah hot chocolate, Mayraah dai ta takure cikin farin duvet din da ta bata ga kamshin turaren jacket dinsa da ya cikata. Mayraah ta daga kai a hankali jin an bude kofar dakin, Ceo ta karaso da cup din hot chocolate ta zauna gefenta tace "Here dear" Mikewa zaune tayi ta amshi cup din hade da sauce dinsa tace "Thank you Ma" Murmushi ta mata tana kallonta calmly tace "You are welcome" Mayraah ta fara shan chocolate din a hankali, Ceo ta mike ta fita, ba a dau lokaci ba ta dawo dakin da few pizza slices a plate ta ajiye mata tace "Will you be okay with this?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Thank you Ma" daga haka ta dau slice daya ta fara ci, after some minutes ceo ta mike ta nufi kofa Mayraah ta bi ta da kallo har ta fita ta jawo mata kofar ta rufe, Mayraah ta sauke idonta tana ci gaba da cin pizza din, bayan ta gama ta dau handbag dinta ta ciro wayarta dake ciki, cikin minti kadan tayi activating international roaming sannan ta fara dialing number Maheer, yana fara ring ya daga, a hankali tace "Yaya" Yace "Mimi" Tace "Ka fara bacci ne?" Yace "No Mimi, was waiting for ur call, i couldn't reach you... ya hanya?" Kamar zata yi kuka tace yaya it's soo cold here, i am so cold" Murmushi yayi yace "Yeah i know, akwai sanyi sosai, hope you are on ur jacket?" Kallon jacket din MD dake jikinta tayi, ta kara lullube jikinta da shi murya can kasa tace "Yeah" Yace "kina ina yanzu?" Ta kalli babban dakin tace "Gidan Ceo din mu" Da mamaki Maheer yace "Ceo dinku kuma? Why? Where are ur colleagues?" Mayraah tace "Ni kadai ce dai a nan, su ba a nan suka sauka ba, may be they lodge in hotel, kasan duk maza ne" Maheer ya ɗan yi shiru, can kuma yace "But that's weird, why will she keep u in her home? Any way it's fine..." Mayraah tayi shiru, yace "Hope you are comfortable?" Mayraah ta gyada masa kai a hankali tace "Yeah" Yace "To abinci fa?" Tace "Ta bani har na ci" Da damuwa Maheer yace "Gashi har muryarki ya fara nuna alamar sanyi ya kamaki" Tayi murmushi tace "Yaya kasan fa bana son sanyi" Yace "I know Mimi, shi yasa nake tausayinki" Tace "But ta ban heavy duvet" Yace "To better" Tace "Yanzu Yaya tambayar ta inda zan kalla inyi sallah zan je in yi?" Maheer yace "But she is a Christian how will she know? Ke baza ki gane qibla ba?" a hankali tace "Bazan gane ba, i am confuse" Yace "Ohk try asking her... Meye ta baki kika ci?" Mayraah tace "Ta bani hot chocolate da pizza" Yace "Ohk to ki samu kiyi sallan, idan kin idar sai ki kirani" Tace "Toh" Daga haka ta katse wayar, tana sauka daga saman gadon duk da dumin dakin she was still feeling cold, a hankali ta saka hannunta a sleeve din jacket din MD sannan ta nufi kofa walking slowly ta bude kofar, tana shiga babban parlon gidan ta dinga bin ko ina da kallo sai kuma ta kalli sama, Muryar ceo ta ji ta juya da sauri ta ganta a study room dinta with heap of textbooks a gabanta, tasowa tayi ta shigo parlon calmly tace "You need anything Mary Ann?" Ta gyada kai da sauri tace "I want to pray Ma...." Ceo tace "Ohh kina tambayar gabas kenan ko?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Yes Ma" Kalle kallen Parlon ceo din ta shiga yi, can tace "I can't really tell where Aliyu faces and pray whenever he is around, let me call him on the phone sai ya gaya maki inda zaki kalla" Mayraah tace "Okay Ma" Ta koma ta dauko cellphone dinta ta fara kiran MD, yana dagawa tace "Aliyu zaka gaya mata inda zata kalla tayi sallah" Daga haka ta mika ma Mayraah wayar, Mayraah ta amsa da ladabi ta kai kunne tayi shiru, jin shi ma yayi shiru tace "Ina ji" Sai a sannan yace "Baki da Google a wayarki ne?" Taki ce masa komai saboda ceo dake tsaye, yace "In rashin kunya ne ai ba sai kin jira wani ya gaya maki yanda za ki yi ba, ba ni kika ce ma Quack Doctor ba, za ki sani" Mayraah dai taki cewa komai, Yace "Install Qibla finder on ur phone and stop being a nuisance" Mayraah bata sake tsayawa ta sauraresa ba ta katse wayar ta mika ma Ceo, Ceo tace "Ya gaya maki ko?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Eh ya gaya min" Ceo tace "Ae kina da darduma?" Mayraah tace "Ina da shi" Ceo tace "Toh sai kiyi using warm water kiyi performing ablution din so u won't catch cold" Yanda Ceo tace mata haka tayi da ta koma dakin tayi alwala da ruwan dumi bayan ta fito daga bandakin ta bude akwatinta ta ciro darduman da Ammi ta sa mata sannan ta tada sallan, tana idarwa ta kwanta ta kashe fitilar dakin sannan ta lullube da duvet nan da nan bacci ya dauketa ko Maheer din bata kira ba, cikin dare taji zazzabi ya rufeta ga tari da ta dinga yi, wajen karfe uku ceo ta bude kofar dakin ta shigo ta kunna wutan sannan ta karasa ta zauna gefen gadon ta cire duvet din jikinta tana feeling temperature dinta tace "Are you okay?" Mayraah ta mike zaune tana rawan sanyi, Ceo tace "You are running temperature dear" mikewa tayi ta fita, ba a dau lokaci ba ta dawo da magunguna da ruwan gora, bude maganin tayi ta ba Mayraah ta amsa ta hadiye da ruwan sannan ta koma ta kwanta ta takure waje daya, ceo ta lullubeta da duvet tace "Sannu kin ji...." Kafin gari ya waye ceo ta shigo dakin ya fi a kirga, da asuba haka Mayraah ta daure ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta koma ta kwanta…. duvet din da taji an cire jikinta ya sa ta bude ido a hankali, MD ta gani tsaye kanta, ta mike da sauri ta ja duvet din ta wani daure fuska tana kallonsa, sae kuma ta ga CEO tsaye a bayansa, sunkuyar da kai tayi.