← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 313

Sashe 155

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ur evidence via 07087865788 Bayan rubuce rubuce Dr Khalil yayi discharging Mayraah, daga gefe kuma ya rubuta mata drugs a wani takarda ya mika mata yace "Ki siya wannan a pharmacy, Allah ya kara lafiya" Ta amshi takardan cikin sanyin murya tace "Thank you, nawa bill dina?" Ya nuna Ahmad dake zaune yace "Yayi clearing din bill din" Ta juya ta kalli Ahmad din kafin tace komai ya mike yace "Idan hotel din za ki koma nima can zan tafi yanzu, in kuma da inda zaki sai inyi dropping dinki it's already late now" Mayraah tace "Toh Nagode" Fita suka yi daga ward din likitan na biye da su, Mayraah ta dinga bin asibitin da kallo ganin na masu hannu da shuni ne don har da jajayen fata ta gani a asibitin, a haka har suka fito haraban hospital din, ruwan ya tsaya gaba daya amma ko ina yayi mugun sanyi, ta takure cikin hijab dinta har suka isa inda yayi parking motar sa, ta bude front seat ta shiga bayan shi ma ya shiga motar, sae da suka fita hospital din ta dinga jin wani yunwa ba na wasa ba, dai dai wani eatry tace "I want to get something here pls if u won't mind" yace "Ohk" parking yayi, ta bude motar ta sauka ta kulle masa sannan ta shiga ciki, ba a dau lokaci ba ta dawo motar rike da leda ta bude ta shiga, sae a sannan ta tuna kanta kadae ta siya ma abinci fa, bayan ya fara tafiya ta ɗan kallesa tace "in siya maka ne?" yace "No, na ci abinci, thank you" Bata sake cewa komai ba, tana ganin pharmacy har zata ce ya tsaya ta siya maganin da aka mata prescribing sae kuma ta fasa da zumar zata siya gobe idan ta bar hotel din, suna isa bayan yayi parking ta sauka tayi masa godiya ta shiga hotel din ta bar sa a baya kamar ba tare suke ba, tsaye take a reception tana jiran makullin dakinta shi ma ya shigo, ana bata aka basa nasa ta bari ya fara tafiya sama, sannan ita ma ta wuce sama, nan taga ashe dakinsa na kallon nata ne ma, ita dae bata kallesa ba ta bude dakin nata ta shiga ta kulle kofar da makulli. Tun da suka dawo asibitin Mayraah ke kwance bata yi bacci ba, don tana shigowa daki kamar tare ta shigo da cramps, wanda a hospital ko alamarsa bata sake ji ba tun da ta farka har suka bar asibitin, tun tana daurewa ta sauko kasa ta sake koma kan gado, ta mike tsaye ta zauna har dai ta kasa ci gaba da jurewa, nan da nan ta fara fita hayyacinta, wajen karfe daya da rabi ta bude kofar dakinta ta fito ko sanin ta fito ma bata yi ba saboda ciwon yayi mata yawa, ta durkusa bakin kofar dakin da taga ya shiga ta kwankwasa da kyar, sae da ta kwankwasa sau uku sannan taji yana tambayar waye, cikin rawan murya tace "Ni ce" bude kofar yayi ganinta Durkushe ya koma baya da sauri yana kallonta, ta fashe da kuka muryarta na rawa tace "Don Allah ka taimaka ka kai ni asibiti" Kallon mamaki yake mata, ta hade hannunta tana kuka sosai tace "Don Allah kayi sauri, wallahi baxan iya ba kuma" Komawa daki yayi ya dauko makullin motar tasa ya fito, sai a sannan ta mike ta jingina da bango har sannan tana kuka, ya kulle dakinsa ya tafi nata ya bude, tana kallonsa ya shiga sai gashi ya fito da hijab dinta ya mika mata, amsa tayi ta sa da sauri, ya kulle nata dakin ma da makulli, a daddafe ta bi sa suka sauka downstairs ya mika ma yan reception din makullansu sannan suka fita tana biye da shi a baya zuwa parking space. Har suka isa asibitin Mayraah kuka take don ita kadai tasan abinda take ji, shi dai tun da ya mata sannu sau hudu ya ja bakinsa yayi shiru.... Dr Khalil ya fito ward din da Mayraah take yana kallon Ahmad dake zaune corridor din wards din ya jingina da bango idonsa a kulle yace "Hey wai bacci kake a nan" Ahmad ya bude ido yace "Really, karfe nawa yanzu?" Dr Khalil yace "Biyu ya wuce, Flight din naka na karfe nawa ne?" Ahmad yace "Karfe biyar" Dr Khalil yace "Nan dae da 3 hours" Ahmad yace "In sha Allah" Dr Khalil yace "Tayi bacci yanzu, i think zaka iya komawa hotel din kar kaje kayi missing Flight dinka, ita kuma zuwa safe za mu yi expecting yan uwanta, daga nan sai ayi discharging dinta don it's just cramps, But still idan baza ka takura ba mu je office dina ka kwanta zuwa 3:30 sai ka tafi hotel din daga can ka wuce airport" Ahmad ya mike yace "Ohk I will prefer that" Tare suka koma office din Dr Khalil Ahmad ya kwanta. Wajen uku da minti arba'in ya tashi daga baccin da yayi, bai ga Dr Khalil a office din ba, ya fita yana rike da makullin motarsa, sai da ya fara zuwa ward din da aka kwantar da Mayraah, kwance ya sameta idonta biyu, har ya karaso ya tsaya kusa da gadon bata ce masa komai ba, yace "Jikin da sauki?" Ta gyada masa kai, yace "Allah ya kara afuwa" Tace "Ameen, Pls ina Dr din?" Ahmad yace "U need anything?" Ta girgiza masa kai tace "Kawai ka kira min shi pls" Yace "Ohk, i will.... Kun yi magana da yan uwan naki?" Mayraah ta sauke idonta kasa, can tace "Ni iyayena ba garin nan suke ba suna Bauchi, admission na samu a nan" Yace "Ok.. ke student ce?" Ta gyada masa kai tace "This is my first time in Abuja, na samu admission a University ne, to kafin in samu hostel shine nayi lodging hotel din" Ahmad yace "Kin samu hostel din ne yanzu?" Still ta gyada masa kai tace "Ana kan processing din mun ne" Yace "Zuwa yaushe?" Tace "Nima ban sani ba, amma idan aka gama zan bar hotel din" Yace "Na gane, shikenan ni zan tafi Allah ya kara lafiya...." Tana kallonsa tace "Ameen, thank you" Yace "I will be checking out of the hotel idan na koma, so take care of ur self, Allah ya bada sa'an karatu" Tace "Ameen, Nagode" Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, har parking space Dr Khalil ya raka abokin nasa yace "To yanzu sai yaushe kuma in ka tafi?" Ahmad yace "May be nan da 5 weeks bikin Humaira" Dr Khalil yace "Ohh haka ne fa, To Allah ya tsare" Ahmad yace "Ameen" Daga haka ya bude motarsa ya shiga, Dr Khalil ya koma cikin asibitin ya tafi ward din da Mayraah take, ya karasa kusa da gadon yace "Ya jikin yanzu?" Tace "Na ji sauki" sai kuma tayi kasa da murya tace "Pls is there anywhere i can get sanitary..... " Sai kuma tayi shiru" Yace "Ohk, give me a minute" Daga haka ya juya ya fita. Da safe breakfast lafiyayye aka kawo ma Mayraah kamar yanda ake ma sauran patients din asibitin, har ta mance rabon ta zauna tayi breakfast din kirki, sosai kuma ta ci abincin, tana gamawa ta koma ta kwanta, bayan sallan asuba Dr Khalil ya shigo ward din yana kallonta yace "Ko dai ba garin nan iyayenki suke ba? Naga har yanzu baki ce za ki kira su ba" Ta gyada masa kai tace "Ni student ce, na samu admission ne a University" Dr Khalil yace "Oh ok, amma ai ya kamata su san baki da lafiya ko" Ta girgiza kai da sauri tace "Aa bana son in daga masu hankali, jiya fa na zo garin" Yace "Really?" Ta gyada masa kai, yace "Daga ina?" Ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Bauchi" Ya ɗan buda ido yace "That's far" Kamar warce ta tuna abu kuma tayi saurin cewa "But my aunty is in Suleja with her husband" Dr Khalil yace "Ohk sun san kin taho Abuja kenan" A hankali tace "Sai nayi settling a hostel zan je wajensu" yace "Ohk that's good, ni zan tafi gida kin ga night duty nayi, zaki kira aunt din taki ne ta taho yanzu?" Mayraah tace "Ni fa na samu sauki, dama idan aka min allurai shikenan sai in ci gaba da shan magani kawai, i am feeling much better now" Yace "Kina nufin a sallameki kenan?" Ta gyada masa kai, yace "Are you sure?" Nan ma ta gyada masa kai yace "Ok then, are u still going back to the hotel?" Tace "Yes" Yace "Toh let me get u discharged sai in ajiye ki hotel din before heading home" Tace "To Nagode" Tare Mayraah suka fito reception da Dr Khalil, duk nurses din sai sallama suke masa da fara'a kana ganin haka kasan he is a free man, a haka har suka fito haraban asibitin, Mayraah dai sai kallon girman asibitin take because it is so beautiful and big, ambulances kusan biyar ne cikin compound din asibitin, sai da ta ga ya shiga motarsa sannan ita ma ta shiga, bayan sun bar asibitin yace "Ya sunan hotel din?" Shiru tayi tana son tuna sunan hotel din, yace "Ko kin manta?" A hankali tace "I can't remember" driving dinsa ya ci gaba da yi har suka iso hotel din yayi parking yana kallonta, duk da tayi mamakin yanda yasan hotel din haka dai tace masa "Nagode" yace "You are welcome Maryam" ta juya ta kallesa tace "Mayraah" yace "Sorry about that" bude motar tayi zata sauka yace "Anytime u are sick, you can come to the hospital ki ce kina neman Dr Khalil" Ta gyada masa kai tace "Thank you so much" yace "You are welcome" Daga haka ta sauka daga motar ta shiga cikin hotel din, tana shiga receptionist din da ta bata makullin dakinta tace "Wannan mutumin da ya kai ki hospital jiya ya biya maki kudin daki na sati daya" Mayraah ta dinga kallonta babu ko kiftawa, can a hankali tace "Toh Nagode" Daga haka ta wuce sama zuwa dakinta. Yanda Ammi taga rana haka ta ga dare, gaba daya ta rasa me ke mata dadi a
Chapter 155 · 0% Book details