Sashe 269
Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Allah ya saka masu da alkhairi barrister, kuma don Allah kar ma ka gaya ma Ammi don nasan sai ta kara juye batun nan, amma nafi tunanin kawai don ta fara aiki ne tare da su yasa suka yi duk wannan abun a kyauta, yanzu dai an sallami Maheer din ne?" Da sauri Mayraah ta juya tana kallon Aunty Mariya babu ko kiftawa, lkci daya ta sauka daga saman gadon da take tace "Aunty ba shi da lafiya ne?" Usman dai kallonta kawai yake, Aunty Mariya ta ɗan zare ido don ta mance a gabanta tayi tambayar, nan da nan ta kirkiro murmushi tace "Jiya ya dawo bashi da lafiya shine ya je ganin likita, amma da sauki ai" Mayraah dai ta dinga kallonta babu ko kiftawa, Can ta juya ta kalli Usman da damuwa tace "Ya Usman dama Yaya bashi da lafiya shi ne aka ki gaya min?" Usman yace "Ya samu lafiya yanzu, idan mun je gida za ki gani" Aunty Mariya ta kama hannunta suka fita daga ward din Usman ya bi bayansu, kamar yanda MD ke avoiding eye contacts da Mayraah for the past one week now, ita ma hakan take a wajenta, don tun da ta gane shine yayan Musharraf wanda back then Musharraf ya sha bata labarinsa amma kuma yace mata yana canada ta ma rasa gane ko kunyan abubuwan da ta dinga masa a baya take, ko kuma dana sanin abinda tayi masa take, wani zuciyar sai yace mata ai ita bata taɓa masa komai ba shine ma yayi ta mata walakanci, but all the same ko don saboda Musharraf ta dau alwashin dole zata ce masa yayi hakuri abubuwan da suka faru a baya amma dai ba yanzu ba tukun, suna fitowa Reception tare da Aunty Mariya kawai ta hada ido da shi, sosai gabanta ya fadi ta sunkuyar da kanta da sauri, Aunty Mariya na kallonsa da murmushi fuskarta tace "Toh Dr mu zamu tafi gida, Allah Ubangiji ya saka da alkhairi, don Allah ayi ma sauran likitocin ma godiya" Ya sauke idonsa yace "Ameen, Allah ya tsare" Kallo daya yayi ma Usman ya juya ya tafi sama, su kuma suka fita daga asibitin, Mayraah na shiga gida bayan ta rungume Ammi dake kitchen tana masu girki don Aunty Mariya ta kirata ta sanar mata an sallamesu, tambayar farko da ta fara yi ma Ammi bayan ta saketa shine "Ammi ina Yaya?" Ammi ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Anjima zai dawo, mu je kiyi wanka" Da damuwa Mayraah tace "Aa Ammi dama ashe bashi da lafiya ne kika ce min ya tafi kasar waje, don Allah ki gaya min inda yake" Ammi ta kama hannunta tace "Kin ga, in dai yaya ne ai dole zaki gansa tunda gida daya za ku kwana, yanzu mu je ki yi wanka ki ci abinci kafin la'asar yayi" Daga haka Ammi ta ja ta suka fita daga kitchen din zuwa sama. Tun da MD ya ga result din DNA test da Ceo ta sa ayi for the past one week ya shiga wani irin rudani da confusion, gaba daya tunaninsa ya kwance, don result din na fitowa kasa hakuri yayi har sai da duba duk da yasan bai kamata ya duba ba, kasa zaune yayi ya kasa tsaye a office dinsa, gashi ko awa daya ba ayi da su Mayraah suka tafi gida ba, does it mean matar nan da ya gani kwance saman gado ita ce mahaifiyar Mayraah? But how? Meye relationship din matar nan da Ceo? Da kansa fa ya debi jinin matar, sannan ya debi na Mayraah, how comes Genetic test din came out Positive, bai san sanda ya dau wayarsa ya kira Ceo da sauri ba, yana fara ring ta daga, ya koma ya zauna cike da confusion yace "Ma result din ya fito yanzu" Shiru Ceo tayi kamar bazata ce komai ba, sai kuma a hankali tace "Nasan ka duba Aliyu, me ka gani?" Cike da confusion yace "Ma'am it came out Positive" Cikin rawan murya Ceo tace "To ita ce mahaifiyarta" MD ya mike tsaye yace "But how Ma? Are you in anyway related to the Woman?" Ceo tayi karfin halin cewa "It's a very long story Aliyu" sai kuma ta fashe da kukan da take ta kokarin dannewa, MD da zuciyarsa ke bugawa yace "To mahaifinta fa?" Nan ma Ceo tayi shiru kamar bazata ce komai ba, sai kuma tayi murmushin takaici cikin rawan murya tace "Yana nan Aliyu, da kuma zan ambaci sunansa kai kanka zaka san sa, don he is well known amma yafi shekara bakwai rabonsa da Nigeria, time to time mu kan hadu da shi a UK" MD ya koma ya zauna ya ma rasa abinda zai ce mata, da kyar daga karshe ya iya cewa "Yanzu taya za a gabatar ma foster parent dinta wannan issue din?" Shiru tayi kamar bazata ce komai ba tana murmushin takaici, sai kuma a hankali tace "I will give them the time, day, date, month and year din da suka ganta, da kuma dai dai inda suka ganta din, da kuma yanayin da suka ganta" zuwa yanzu she was trying so hard to control her self kar ta fashe da kuka sosai, MD ya kara shiga wani confusion din, ya mike tsaye yace "Amma ta yaya kika san duk wannan Ma? Dama kinsan sanda aka yi deserting dinta ne da kuma inda aka yi deserting dinta?" Hawaye ne kawai ke sauka idonta ta kasa ce masa komai, bayan wasu seconds tayi gathering courage tace "I said it's a long story Aliyu, i will get back to you" Daga haka ta katse wayar yanda zata yi kukan dake cin ta sosai.