← Book details Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 272 OF 313

Sashe 272

Mayraah Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

kafi wancan ɗan uwan naka hankali da sanin ya kamata shi yasa na amshi number gun Dr Khalil na kira ka mu hadu" Maheer ya dago kansa yace "Ni fa na rikice, yanzu me Ceo din ke cewa?" MD yace "You know what will happen now?" Maheer ya girgiza kai, MD yace "May be u should talk to ur dad about this Asap, sai aje gidan Ceo don ita ce zata yi bayanin wacece wannan matar wanda DNA test ya nuna ita ce mahaifiyar Mayraah, you are a Dr, and i am also a Dr, mun san babu karya a DNA test, although i know this isn't enough evidence a wajenka da ma family dinka tunda ba a gabanku aka dau jinin ba, kuma ni nasan dole za a sake wani test din don clearing doubt din kowa wanda kai da kanka zaka debi both samples ka kai duk inda ka yarda ayi test din" Maheer yayi nisa tunanin da ya fada lokacin, sai a sannan maganganun Ammi suka dinga dawo masa yanda ta dage bata yarda da ceo akan kulan da take ba Mayraah ba, kullum zancenta kenan tun kan wannan incident din ya faru na poisoning Mayraah, Maheer ya girgiza kansa don har sannan shi fa ya kasa assimilating lamarin yace "To amma me ita ceo din ke cewa akan result din?" MD yace "Kuka kawai take ta kasa min bayanin komai, ban kuma zo nan gidan ba sai da saninta, kaga she is willing to reveal who the woman in her house is" Maheer yace "Gobe da safe Abbanmu zai dawo, zan masa duk wannan bayanin, nasan kuma a goben za mu je har gidan Ceo din, amma pls ita matar da ka debi jinin ta muslma ce?" Zuciyarsa na bugawa yayi tambayar, a hankali MD yace "I can't really tell, don nace maka she is not mentally stable" Maheer ya kasa cewa komai ya jinginar da kansa da kujeran motar. Har Maheer ya shiga gida kansa a kulle yake, ya zama so confuse nan da nan kansa ya fara ciwo, Ammi dake ta jiransa ta mike da sauri gabanta na faduwa tace "Ya aka yi Maheer?" Yayi yake yace "Ba komai fa Ammi, kawai wasu magunguna wai za a daurata a kai na yan watanni" Ammi ta fashe da kuka tace "Dama ba na fada ba, kilan sun hango wani mugun abun ne" Maheer yayi dariyar karfin hali yace "Kai Ammi, amfanin maganin fa kawai wanke duk wani system dinta zai yi ne tunda poison din me karfin gaske ne, amma wallahi basu ga komai ba, kuma a likitance haka ya kamata su dorata kan magani, ina jin sun mance basu rubuta maganin bane da suka sallameta" A haka dai ya samu ya kwantar ma Ammi hankali, sannan ya wuce dakin Usman, shi ma ya sanar masa duk yanda suka yi da MD, Usman was also speechless ya dinga kallon Maheer, Maheer yace "Yanzu zan koma daki in kira Abba in sanar masa tun kafin ya dawo, don wannan issue ne da ya kamata a daukesa da muhimmancin gaske" Usman yace "But how are we to believe this bayan ba a gabanmu aka debi jinin da aka yi test din ba" Maheer yace "Duk za a zo wajen, kai ma kasan dole ne za a sake wani test din to clear everyone's doubt" A hankali Usman yace "Amma ita matar da ya debi jinin nata musulma ce?" Maheer ya sauke idonsa kasa yace "He said she is not even mentally stable" Usman ya dinga kallonsa babu ko kiftawa. Washegari Abba Flight din safe ya biyo daga kano zuwa garin Abuja, Ammi tayi mamaki sosai don da yamma ya kamata ai ya dawo ba da sassafe haka ba, ta dai yi welcoming dinsa, ko zama bai yi ba yace "Ki shirya za mu fita ne Hajiya" Da mamaki tace "Zuwa ina Yallabai?" Yace "Za mu je gidan Ceo din nan ne mu yi mata godiya kafin ta bar kasar" Nan da nan Ammi ta hade rai tace "Godiyan me kuma Yallabai? Ina ce biya muka yi..." Abba yace "Wa yace maki an biya? Au wai dama baki san bata amshi ko sisi a hannunmu ba? To a kaddara ma mun biya din laifi ne don munje mun ma warce ta ceto ran er mu godiya? Daga kasan waje fa ta taho da manyan likitoci, me yasa kike yin haka Madam?" Ammi dai ta kauda kai bata ce komai ba, Abba yace "Ina parlor ina jiranki" Daga haka ya fita ya koma downstairs, Ammi babu yanda ta iya haka ta shirya ta sauko downstairs din ko su Aunty Mariya bata sanar ma ba, da mamaki take kallon Mayraah tace "Ke kuma ina za ki?" Abba yace "Ni nace ta shirya mu je tare" Ammi tace "Haba yallabai, duka duka yaushe ta farfado ai yayi wuri ta fara fita yanzu nake ga" Maheer dai sai kallon Ammi yake, haka ma Usman dake parlon, Usman yace "Abinda mota ne Ammi, zama kawai fa zata yi a mota" Abba yace "Shi dai na gani, ku tashi mu tafi" da mamaki Ammi tace "Su kuma ina za su?" Abba ya kwantar da murya yace "Kina bata mana lokaci ranki shi dade" Daga haka ya fita, Usman ya bi bayansa, Mayraah dai ta mike tsaye tana kallon Ammi dake ta kallon Maheer, rai bace Ammi tace "Wato har da ku kenan za aje? To wai meye ma'anar haka? Haka duk sauran patients din asibitin suke idan sun warke su je gidan Ceo yi mata godiya?" Maheer yayi kasa da murya yace "Ke dai don Allah tunda yace mu je kawai mu je Ammi, ai ina ga ba wani abu bane don anje an mata godiya duba da yanda aka bamu full attention a asibitin kuma saboda Mayraah staff dinta ce ta taso tun daga kasar waje da wasu likitoci, relax plss Ammi" A haka dai ya lallabata suka fita zuwa motar Abba dake jiransu, tun asuba Maheer ya kira MD yayi sending masa address din gidan Ceo kamar yanda Abba ya bukata, suna shiga motar Abba da kansa ya ja motar suka bar gidan zuwa gidan Ceo.
Chapter 272 · 0% Book details